← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 30

Sashe 2

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Amen, ina haladu azo a samo nama a zuba a freezer da duk abubuwan da aka san babu dan bana son ko alawa taji tana so ya zamana babu”

“Gaskiya fa ai maraya hidimar sa daban take, gara mu fita hakkinta, oh Allah sarki yaya Ibrahim da mariya wai yau an wayi gari babu su, duniya labari “
Sallamar baba megadi ce ta katse su, yace ana sallama da Alhaji kabiru.

****
Kwanan Sam bakwai aka sallameta lokacin mahaifinta na da kwana bakwai cif da rasuwa, gwaggo da kanta ta kai ta gidan Alhaji kabiru inda ta dam’ka amanarta a hannun umma salamatu,

Dafarko ta d’anyi raku’be raku’be kasancewar bata saba da shiga cikin jama’a ba, kullum tana tare da mahaifinta indai ba makaranta ta tafi ba, se daga baya ta sake dake tasu tazo d’aya da Amir.

Faran faran take da rana amma fa da ta shiga d’aki ta kwanta se tasha kukanta ta ‘koshi kan barci ya d’auketa wanda kuma kullum da kukan take tashi saboda mafarkin da ya riga ya zame mata jiki dan jazaman ne se tayi gashi har yau Allah be bata sa’ar ganin Daddy ba da kuma mutumin da kullum daddy ke kiransa da hasken ta.

Duk wani jin dad’in rayuwa daidai gwargwado tana samu gidan baffa kabiru kullum iro driver dinta ke kai ta school se de tun bayan rasuwa ba a bata security ko d’aya a cewar Kawu kabiru iro kad’ai ma ya wadatar

Kwanan Sam arba’in da bakwai umma salamatu ta sauka inda ta haifi ‘yar ta mace sak kawu se duhun fatar umma data d’auko, a lokacin nan abubuwa suka fara sauyawa Sam dan tunda akayi haihuwar nan ita ke taya uwani me girki hada hadar gidan kai har ta kai ita ke sharar gidan, ranar suna kuwa har zazza’bi tayi dan gajiya dama gashi ba sabo , yarinyar da aka haifa taci suna safiyya.

Bayan shekara biyu

Tashi tayi da salati a bakinta, ta fad’a toilet tayo alwala tayi salla da sauri sauri ta nufi falo dan gyarawa seda ta tattare komai sannan ta fad’a kitchen tana aiki tana kallon agogon bango gudun kar tayi latti bayan ta had’a komai ta jere bisa table sannan ta fad’a toilet dan yin wanka

Kintsawa tayi cikin sabon unifoam d’inta na junior classes ta rataya sabuwar jakarta da aka bata a makaranta dan ever since daddy ya rasu komai kyauta hukumar makaranta ke mata.

Kasancewar ta fara tasawa yasa wani ni’imtaccen kyau ya fara bayyanar mata idan ka ganta lange Lange kamar ka hureta amma kyau kam ko ‘yar uwarta mace ta kalle ta se takuma kallon ta.

Muryar Amir taji yana kwala mata kira daga can sama kuma tana iya jiyo kukan safiyya, saurin fita tayi su kayi kici’bis da Amir yayi mata👌🏻Alamun tayi kyau ta turo baki tana masa hararar wasa yana faman tsokanarta iyeh kaga ‘yammatan j.s 1, dan alokacin shi j.s 3yake daidai ‘kofar fita tayi tuntu’be ‘kiris ya rage takai qasa ya taro ta, idanunta dake runtse ta bud’e a hankali suka sauka cikin na shi

Cikin rawar murya ta furta “ya...

©️Kdeey😊
DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(3)
“Ya ha..habibii”

Kanne mata ido yayi ” have I been missed?” yayi saki wata muguwar dariya “oya matsa daga gabana before na mangare ki” ya sake ta da sauri,
Sum sum sum taja jiki gefe har tana neman fad’uwa, Amir da shigowarsa kenan yaga duk abinda ya faru ya ja hannunta a fusace suka nufi mota.

Habibii ya bisu da muguwar harara, ya shige cikin gidan yana kwala wa umma Salamatu kira.

****
“Sam muje wasa?”

Girgiza kai tayi a hankali “um um sholey I can’t play now just go ahead “

“Why Sam ?” Yarinyar ta turo baki gaba alal dole ranta ya ‘baci ,
Mu’allim bello malamin islamic wanda yazo wucewa ya ji maganar tasu ya tsugunnawa

Yace “meya samu samira naga tana ‘bata fuska ta manta yau kun shiga secondary” ya ‘karashe maganar idonsa kan fuskarta

“Mu’allim tun safe haka take”

Jinjina kai yayi idonsa kan ta, yace “Samira kina tuna daddy ne?”

Kallonsa tayi idanunta cike da hawaye ya d’aga kai, “I miss him so much”

Bud’e baki yayi zeyi magana wani security ya iso da sauri “mu’allim that your bossy brother yazo nemanka”

“Ohhhhh, yanzu kuma” ya karashe da kallon agogon hannunsa kan ya juya ya nufi hanyar gate har yayi gaba ya waiwayo inda yaga idanunsu ‘kuri a kansa

Yace” c’mon let’s go ”

Kallon juna sukayi kan su bishi a guje, daka d’an nesa yace su jira shi ya nufi motar dake parking lot ya shiga, ya jima cikin motar sannan ya fito.

Fuskar nan kadaran kadahan, har class ya raka su sannan ya koma office.

****
Umma salamatu ta d’ago a fusace bayan ta tabbatar da yaran sun tafi makaranta cikin d’aga murya tace

“Kagani ko ka gani ko, yau kwana tara kenan Ina bin kanka a tura Sa’idu (qaninta)can turkey yabi sakaran yaran nan to ga irinta nan, yanzu how sure are you manager din baze cuce mu ba bare yaga ba idon mu, nifa Ina tsoron mutanen nan, dukiyar maraya fa!”

Ajiyar zuciya Alhaji kabiru ya sauke kan ya kalli habiibii yace “Kai na baka kwana biyu ka shirya ku koma tare da sa’idu, kaji dai abinda mahaifiyar ka ta fad’a “

Fuska a had’e ya amsa “naji Abba amma...”

“Amma me? uban naka zaka kawo wa qabali da ba’adi? Eyeh? Fice ka bani guri”

A fusace ya wuce, ta kalli Alhaji kabiru “nifa Abban yara inaga kaima se ka bisu kaje ka gano halin da ake ciki dan habibii yace wannan “Hidden” d’in sun aika musu da takarda kamar yacce suka tura wa ragowar kamfanonin”

A rud’e yace “what!?”

Ta kya’be baki “uhm duba ka gani”

Amsa yayi yana shafa velvet bag d’in da aka rubuta ‘HIDDEN da manyan ba’ki bud’e jakar yayi ya fiddo takaddar da akayi rubutu da silver ‘make sure kun Adana every details’,

“this is different from the others”

“And that’s why nake so mu iya takun mu, and again ina buqatar kud’i dan zan aika ma c.i.d d’ina this time around inaso ya samomin gamsassun bayanai a kan ‘HIDDEN’ I want them to know they are dealing with d wrong people,

Girgiza kai yayi ya wuce, ta bi bayansa da ido har ya fice ta d’auki wayarta ringing d’aya tayi aka d’aga “proceed as planned “ ta furta cikin kausashiyar murya

****
Bayan wasu watanni

Ta du’kufa sosai Amir yana koya mata maths dan gobe zasu zana jarabawar gama aji d’aya, “umma salamatu inaso ki tayani da addu’a gobe zamuyi maths” ta ‘karashe a shagwa’be,

Shafo saman kanta tayi, “Insha’Allah habibty, Allah ya bada sa’a I trust you,and you never disappoint”

Smiling tayi har beauty point dinta ya lotsa Amir ya zira biro ciki ta bige hannun tana dariya idonta kan umma salamatu wacce take kalla,

Tsugunnowa tayi ta bata peck a chubby cheeks d’inta tace “concentrate habibty”

Smiling tayi ta juya kan littafinta tana faman turo baki, sanin cewar dashi take ya ri’ko hannunta “am sorry baby sis ni ne ko bazan kuma ba kinji”

Kallonsa tayi tare da nuna masa ‘karamin yatsanta tace “promise?”
Ya sar’kafe cikin nashi “I promise”, suka cigaba da karatun su.

Washegari
Tafe suke zuwa office d’in mu’allim bello suna hirar yacce exams d’in tayi musu dad’i sunzo daidai sport center ball ta gangaro gabansu ‘Kiris ya rage sholey tayi tuntu’be Sam ta ri’kota, a fusace ta d’ago ta fara fad’a zabgegen yaron da ya zo d’aukan ball d’in ya tsaya yana huci fuskar nan a cusgune Sam da duk ta firgice ta hau Jan hannun sholey su tafi ‘ki’kam ta’ki tafiya ala dole ta saketa ta nufi office d’in mu’allim bello a guje daidai lokacin ya d’aga labule kanta ya bigi ‘kirjinsa ‘kamshin daya doki hancinta ne yasa tayi saurin d’ago kai idonta ya sauka kan...

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(4)
Fuskarsa, “ya akayi cutie?”

“Mu’allim sho..shole..y” ta ‘karashe murya na rawa tana nuna masa hanyar da hannu, gaba yayi da sauri ta mara masa baya daidai lokacin yaron ya d’aga hannu kenan ze doke ta,

“Adnan!!” Mu’allim bello ya daka mishi tsawa, saurin sauke hannu yayi yana faman huci, kunnenshi ya ri’ko ya nufi office dashi su kuma sukayi zuru suna binsu da eyes, a hankali ta matsa kusa da sholey

Tace “sholey are you okay?”

Sholey da idanunta suka kawo ruwa ta girgiza kai da sauri ta fad’a jikin Sam “thank you for saving me”

Hannu tasa saman gadon bayanta tana sama da ‘kasa dashi alamun rarrashi tace “its okay, afterall what are friends for?” Ta d’aga mata gira with a questionable look a fuskarta, murmushi sholey,
“Good girl, let’s go home Mu’allim Bello will deal with him “ riqe da hannun juna suka nufi parking lots inda drivers dinsu ke jiransu.

Aysha Aliyu shine asalin sunan sholey yarinyar Dr Aliyu da Barr. Badariyya, they are the family of four Affan shine babba wanda ya girmi sholey da kusan shekara bakwai, su biyu jal Allah ya mallakawa mahaifansu ‘yan boko ne sosai hakan yasa yaran su da wuya kaji suna wani yare wanda ba turanci ba banda shi kuwa se dai kanuri ko hausa

Sholey sun had’u da Sam a lokacin zasu shiga primary one na makarantar capital school inda aka had’asu zama seat d’aya, tun daga wannan ranar suka ‘kulla aminta har kawo wa yanzu da suka shiga makarantar gaba da primary.

****
Yau garin na kano an tashi da ruwan sama me qarfin gaske gari yayi sanyi ko ina kirif kirif yake haka zalika mutane tsilli tsilli suke waje, Sam na zaune a d’aki ita da mubina da tazo musu weekend suna kallon Aladin wanda hankalinsu rankatakaf suka maida can, turo ‘kofar da akayi ne ya ja hankalin su

Murmushi ta saki ganin umma salamatu, “yammata na kallo ake?”
“Uhm umma movie d’in nan yayi kyau am so sure you will like it, come and join us”

“Oh Sam I will love to amma kinga fita zanyi”

“Umma fita? Ina?”
Chapter 2 · 0% Book details