← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 30

Sashe 18

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yes" suka furta a tare, wata dattijuwar baturiya ce ta leqo d'akin with a smile plastered on her face,
"Wellcome to saint teresa college"

Nodding sukayi game da fad'in "thank you"

"I'm miss patricia, dafatan zakuji dad'in kasancewar ku a nan, ni ce shugabar d'akunan hostel d'inku hope you will cooperate with me"

"Sure" suka ce tayi musu thumbs up ta tafi had'e da rufe musu qofa"

"Saint teresa" munu ta furta cikin rolling eyes kan ta fad'a saman gado, dariya tayi ta juya ta nufi bathroom ta dauraye hannu ta fito gefen gadon ta zauna ta shiga bud'e flask dan kauda yinwar dake qwaqularta.

~
"Care to explain yourself?"

Hannu sa daya d'ora saman handle ya janye game da waiwayo zaune take medicated glass maqale saman idonta tana duba jarida, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kan ya taka ya isa gabanta

Daidai qafarta ya gurfana kansa a qasa tunda yake be ta'ba jin kunyar Ammi kamar ta yau ba,
"Ina saurarenka"
Muryarta ta katse sa, lumshe ido yayi game da bud'esu saman qafarta ya d'ora hannayensa a kai ya shiga mata matsa, ga mamakinsa se ta janye qafar cikin had'ewar fuska

Tace "Ann kar ka maida ni babbar kurum mana , taya kake neman fito da sabbin d'abiu wanda ko a yahudu mara kunya ke yin hakan, kar ka bari na kuma tambayar ka"

Rufe ido yayi, yace "...mata tace..."

Cikin rawar murya tace "Ma..mata kace??"

'Daga kai yayi idonshi a qasa "Ammi banso kika yi pushing d'ina na fad'a miki ba, this is not the right time..."

"..right time? Is this what you are suppose to say to me? Wait Anwar taya akayi Samira ta zama matar ka da yawun wa? Wane ya baka ita?"

"...kawun tane, kawu kabiru," yace idonsa a lumshe,

"Anwar yaushe ka fara qarya? Na zata kawunta an nemeshi an rasa, wait..don't tell me you are behind all this"

"Not all Ammi.."

"Ya isa.." ta d'aga masa hannu, tare da juy masa baya, rarrafawa yayi ya riqo qafarta jin tana sheshsheqar kuka,

"Na rantse miki da Allah Ammi nayi hakan ne saboda farautar ransa da aka fara"

Ta juyo hawaye na bin fuskarta "kanaso kace shima ana neman rayuwar sa ne?"

"Hakane, ciki harda matar sa da yaronta"

Cike da mamaki tace " ban fahimce ka ba"

Gyara zama yayi, ya fara da cewa
" wata rana na fita zagayen gari dai dai wani lungu a amadu bello way na hango wani saurayi na leqe hakan yasa naja gefe nayi parking dan ganin abinda zeyi bisa mamakina da yaga babu kowa se ya fito game d yafito wata babbar mace tazo suka fad'a wani d'an qaramin gida se da na tabbatar sun shige na fito , ta bayan wani window na tsaya dan naji meke faruwa a gefe guda kuma inason ne naji inhar barayi ne ko wasu masu tada zaune tsaye na kira 'yan sanda cikin ikon Allah se naji maganar mace na fad'in

"Nace muku ki ida kashe shi kunqi wai shin ba kunyi min alqawarin kashe kabiru bane ko dai bakwa son kud'in ne! Kun kuwa san alqawari, dakanku kuka dafa qur'ani kuka kuma rantse zaku kashe mana shi, kai kuma Amir ina zancen fyad'en da zaka yi mata!

Wai ku wasu irin daqiqai ne to billahillazi na baku kwanaki uku rak ku aiwatar da abinda nace muku in ba haka ba mu zamuyi da kanmu idan yaso kuyi biyu babu, haka itama uwar yarinyar mu kasheta dan mun gaji da ajiyar kayan da ba mamora.."

Baya naja da jin haka, a take na bar wurin jiki na rawa na nufi makarantar da Bro B yake kula da Sam, na shaida masa duk abinda naji mummy wlh kuka nake daqyar na iya sanar dashi labarin tun daga wannan ranar muka saka ido kan shige da ficen su kwatsam a kwana na biyu sega shi an kawo Samira asibitin hasheem ganin haka nasa Dss bashari ya tura aka kama kafatanin gidan with d exception of shi uncle dinta da babban yaron ta na tura su nijar qarqashin kulawar aboki na shugaban qasar garin,

Aurena da Sam kuwa ya faru ne dalilin ajiyeta a wurina da nace zanyi, kawu ya nemi tayina a kanta da farko naqi aminta sedai tsoron abinda ya faru da ita da Amir kada ya kuma faruwa da ita tunda ga habiibii yasa na yarda a ranar mutawakkilu ya amsa walicci na aka d'aura aurenmu bisa sadaki millon d'aya, wanda na bud'e acct da sunanta na ajiye a ciki da alqawarin duk sanda tasan gaskiyar lamarin zan mallaka mata haqqinta, sa'annan a tambayi ra'ayinta a kaina,

Ba iya nan na tsaya ba dan nayi tattaki har turkey na damqa kamfanin dake can a hannun gomnati da taci gaba da kula dashi tare da basu 2 % na riba, a yanzu haka habibii wato d'an kawu kabiru na tura shi karatu singapore shi kuma kawu yana gidan mutawakkilu wato shugaban qasar nijar"

Ammi durqushewa tayi hawaye nabin fuskarta, tace " Ann cikin labarinan wace uwar yarinya da aka gaji da ajiya",

Murmushin da yafi kuka ciwo yayi yace "Ammi na mummyn Sam na raye..."

Qirji ta dafe da hannh cikin kufcewar kuka take fad'in "um um um um Ann kada kayi min qarya! Ka fad'a min gaskiya dan yin hakan baze kwantar min da hankali ba sede ya tada min"

Hannuwanta ya kamo cikin nasa "Ammi ki nutsu ki saurare ni yi miki qarya da wannan maganar babu riba a gareni mahaifiyata ki sani duk wannan fad'i tashin da nake saboda farincikin ki nake"

Hannu tasa ta share hawayen fuskarta "Ann zan had'a ka da chief of army staff na nigeria madu Aliyu lallai inaso a kamo min matar kabiru dan tabbas tana da masaniyar inda mariya take" waya ta d'auka da niyyar kira yayi saurin cewa
"Ammi zan fiso mubi komai a sannu, idan muka ce zamu bi abin sama ta ka abin baze zo mana da sauki ba, yanzu haka Bro B yana can kan binciken wanda suka kawo mana hari a hanya wanda nake kyautata zaton hakan will lead us to mutanen dake riqe dasu aunty mariya"

Jimm tayi,can tace "Ann all this years ace mariya na raye? Shin wani irin hali take tsayin shekaru sha wani abu ba tare da taga wani nata ba?" Ta qarashe cikin tsananin kuka.

Kwantar da kanshi yayi a qafarta shima yana zubda hawaye yace "Ammi na inaso kiyi min wani alqawari" yayi rigingine idonsa a kanta yace "you will never let Sam knows about this ciki harda zancen aure na dake kanta"

Girgiza kai tayi cikin dashewar murya tace "meyasa.."

"Hankalin ta baze d'auka ba, and nafison ta kammala makaranta tukunna"

"Se idan ka iya d'auke idonka a kanta, dan idan har abinda ka aikata d'azun ya kuma faruwa to kuwa lallai ita da kanta zata kawo wani abu koda be danganci igiyar ka dake kanta ba"

Nannauyan ajiyar zuciya ya sauke had'e da jinjina kai cike da tunani bacci yayi awon gaba dashi , murmushi tayi cikin zubar hawaye ta d'aga hannuwa sama tana dad'a godewa Allah da kuma roqon Allah ya bayyana 'yaruwarta ya kuma kawo musu komai cikin sauqi, pillow ta janyo ta d'ora kanshi a kai ta d'auko blanket ta lullu'be shi, ta shige d'aki ta kwanta hawaye na zubo mata cike da tausaya wa rayuwar su, su duka,

Bello ko a wani hali yake ciki? Tunanin hakan yasa tayi saurin kiran wayar bello,

***
Cikin wani babban gida suka shiga bayan sun tabbatar da ba wanda ke ganin su, wata mata ta fito jikinta sanye da tsadadden leshi wuyanta da hannunta cike da gwalagwalai se d'aukan ido suke shigowarta cikin haske yasa hasheem da bello dake kallonsu tamkar a TV ta cikin camera da suka manna jikin salihu ba tare da sanin sa ba suka miqe a firgice...

"Haj..iya mar...yam..mainasar" suka furta cikin rawar murya kallon juna sukayi a rud'e zuciyoyinsu na tsananta bugu, qurawa mini TV d'in ido,

_Tafa hannu tayi "you guys did a very good job, you deserve a medal you know, tayi dariya kan ta hakimce saman kujera tayi musu alama da hannu cewar su zauna,_

_"Nafi'u kunyi qoqari mutuqa se dai naso ace ku da kanku kuka qarasa su, dake Allah na sona se ya kawo min komai cikin sauqi" ta kwashe da wata arniyar dariya lokaci d'aya kuma ta gimtse tamkar ba ita ba_

_Tace "naji ance baquwar fuska ta shigo unguwar ku" jimm sukayi cana rody yace "eh madam wani corper ne yazo serving anan makarantar arean mu"_

_"You know i hate new faces so ku iya takun ku" kai suka jinjina,_

_"Madam have u heard from lawalin nijar kuwa?" Cewar aqilu,_

_"Har yanzu ba wani labari, amma akwai tabbacin be fita daga garin ba"_

_"Partaining hajiya ya ake ciki akwai wani improvement?" Cewar salihu_

_Kafad'a ta d'aga "talking about waccan matar je kazo min da d'an iskan dattijon nan" ta furta hakan idonta saman wani qaton gardi dake tsaye a gefenta_

Sulalewa su bello sukayi , ganin an _shigo da wani dattijo hannunsa da qafafunsa maqale da ankwa jan qafa yake dan tafiyar ma ta gagare shi, shi da qashi marabar su qalilance se fata, janshi akayi har gabanta aka tunkud'ashi kansa se gilu gilu yake ko d'aga kai wannan ya kasa, qur suka zuba mishi ido sai salihu daya sadda kai,_

_"namadi" ta kira sunan sa tun qarfi, na rantse da wanda raina ke hannunsa idan baka fad'i inda diamond d'in nan yake ba, da kai da hajiya a yau kwanan ku ze qare"_

_dattijon da ta kira da namadi ya d'ago kai jiki ba qarfi cikin inda inda tamkar me koyon magana yace na rantse da Allah baki na baze ta'ba furta sirrin ubangida na ba koda zaku rinqa yankar nama na kuna zubar wa"_
Chapter 18 · 0% Book details