← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 30

Sashe 12

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jinjina kai uncle yayi idonshi kan Anwar “hakane ka shirya gobe ku tafe da safe tun kan garin Allah ya gama washewa”

“Ni kuma..amma...”

Barrister yace “uhm uhm ka koma bakin aikin ka se ka rinqa kular mana dasu, nayi magana da mss chloe kan makarantar da ka sauka ka je ka same ta” ya kalli bello “Kai kuma ka shirya dan muma da safe zamu tafi garin damagaran dake jamhuriyar nijar “

“Barrister ni kuma fa?”

“Kar ki damu , bazan bar gidan nan ba face na bar miki yan sanda wanda zasu kula da lafiyarki ”

Ta girgiza kai, “shikenan kai ni gurin yarana na kintsa su tunda fitar wuri zasu yi,”

Bello ya taka mata, Anwar da uncle kua , kusan raba dare sukayi suna tattaunawa.

3:00am
‘Kishin ruwa ya farkar da Anwar, kasancewar dare ya tsala ba abinda kake ji se qarar haushin karnuka, qafafunsa ya fara s’aukarwa qasa daga bisani ya miqe tsaye seda ya duba fridge d’in d’akinsa babu ya nufi frdge d’in kitchen,

“Gwaggo yinwa muke ji” muryar su Sam ta bigi kunnen sa,

“To ya kuke so nayi muku, dan Allah ku daure zuwa gobe da safe se na bada a samo muku qosai da asuba”

“Ni...ni dai Allah kinsan fa ba za’a samu da asuba ba, wayyo zan mutu”

“Ke samira, kul kul na kuma jin kin ambaci mutuwa maza ku tashi ku d’auro alwala kuyi ta sallah yinwar zata ragu “

“What” ya furta a hankali bud’e warmers d’in dake saman dining yayi, ganin akwai abincin da cook ta dafa, tun na dare yasa shi yin hamdala saman trey ya jera har da plates da spoons ya nufi d’akin

knocking yayi, daga ciki kallon kallo sukayi, gwaggo addu’a d’auke da bakin ta ta nufi qofar

“Au Anwar kana tsaye dama, abin hannunsa ta kalla, “har da hidima haka da dare ai da ka barshi ma” a zuciyarta cewa take kar de yaji maganar da muke

Murmushi yayi yana jinjina Kawaci irin na matar yace “aa bakomai”

Hannu tasa zata kar‘ba yace “aa gwaggo barshi, kai maza kuzo ku kar‘ba kun tsare mutane da ido, munu ce ta fara zuwa ta kar‘ba, ita kuwa Sam dad’a sunkuyar dakai tayi tana dad’ matse cinyoyinta a qirji duk kunya ta kamata saboda rashin mayafi

Kamar daga sama taji yace “Ke mara jin magana bazaki taso ba” rau rau tayi da ido idonta akan hijabinta dake jikin munu ta taso, a hankali ta isa gabanshi ido a runtse ta miqa hannu ta amsa plates d’in ta juya nan ma tamkar wacce kwai ya fashewa a ciki, qofar yaja ya rufe ya jingina jikin bango ido lumshe

Daqyar ya ‘bam’bare daga jikin bangon ya koma d’aki, fad’awa yayi saman gado had’e da ruqunqume pillow, ido ya rufe ba komai yake gani ba illa tafiyar Sam wacce duk takun da tayi yammatan qirjin ta ke motsawa kasancewar rigar baccin jikinta ce kawai tayi musu sutura, tsaki ya ja had’e da sakin guntuwar dariya yace “lemun tsami kenan” tashi yayi ya fad’a band’aki ya d’auro alwala ya shiga yin nafila

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(18)
Abinci cike da baki ta watsa wa munu hararar qasan ido, tana fad’in “wlh tunda kika sa namiji ya ganni a haka se na rama,”

a hankali munu tace, “To ba kece da gwaggo tace mu tashi muyi nafila ba, baki tashi ba, me kike dashi da zaki ‘boye masa..” ta qarashe da dariya

Takaici ya cika Sam tayi qwafa, “To wayace ki d’aukar min hijabi ko bani da komai ai mu’allim bello yace duk namijin da ba baban ka ko qaninka ba ba muharraminka bane ka kasance me killace kanka...” qwarewar da tayi ne ya hanata qarasa maganar gwaggo data kishingid’a ta tashi a firgice tana shafa mata baya, munu kuma ta bud’e fridge ta d’auko mata ruwa, daqyar ta dawo daidai, abincin da bata qarasa ci ba kenan bacci yayi awon gaba da ita.

Misalin 5:30, zaune suke suna hira Anwar yayi sallama, cikin qasaitaccen takun sa ya qarasa cikin falon daidai kujerar da gwaggo take ya tsugunna yana gaida ta, gaishe shi suma su kayi, ya amsa ba tare da ya kalla inda suke ba yace “Gwaggo akwai saqo na ajiye miki a d’aki,”

jinjina kai tayi cike da tunanin ko menene? tace “To madallah angode Anwar”

“Ku tashi muje ko” ya furta a hankali, gwaggo suka nufa ko wacce cikinsu ido ya kawo ruwa, amma ba damar kuka ganin yacce Anwar ke tsare gida,

“Allah yayi muku albarka, kuji tsoron Allah, ku kuma riqe addinin ku, kar kuga bama tare bazan kwa’be ku ba, Allah na kallon ku kuma ku ze hukunta ku gwargwadon lefin da kukayi masa” ta kalli Anwar “a yanzu ragamar kula da ku su na hannunka, gasu nan amana” ta qarashe cikin rawar murya kallonsu tayi ganin yacce suke qiqqifta ido yasa ta shige d’aki da sauri, “Allah ya sauke ku lafiya” ta fad’a daga ciki.

Da hannu ya nuna musu hanya, jiki a sanyaye suka nufi waje ko wacce na qunshe kukanta kar Anwar yayi musu fad’a, cikin wata golden d’in jibgegiyar motar Lexus Jeep suka shiga inda ya umarci d’aya cikinsu ta shiga gaba, munu tayi saurin shigewa baya ta bar Sam tsaye wacce kukan ta ya koma da biyu ga na rabuwa da gwaggo ga kuma na zama kusa da dodon ta, dan ita har firgita take idan taji koda motsin sa ne , inaga yau gashi gata?,

“Ke ba zaki shigo bane,”

Girgiza kai tayi ta bud’e ‘kofar a hankali zata rufe kenan se ga bello kamar wanda aka cillo yana haki alamun yasha gudu yace “hold on, taya zaku tafi ba sallama, ya miqa musu wasu manyan ledoji ga kaya nan idan kuka je abuja Bro A ze kai ku a d’inka muku kafin ku tafi, munu dake baya ta amsa su kayi Godiya, da baya ya koma yana Sarawa Anwar

“Drive safely bro”

Murmushi ya masa kan ya harba motar.

***
Kusan minti biyar yana duba takaddar ba dan be fahimci abinda ke rubuce ba, se dan son tabbatar da abinda ke jiki shin ya take me?, wayar Anwar ya kuma trying for the fifth time in taqi shiga, bello ya fad’o masa a rai dialling wayarshi yayi ringing biyu ya d’aga

“Babban likita na Rayya bada kanka a sare..”

One sided murmushi yayi “Abokina Ina Yayanka?”

Bello yace “yana daf da shiga Abuja”

Duka ya kaiwa bango, yana to and Fro yace “ ya Allahu I really need to see him why did he left ba tare da sallama ba, when is he coming back?”

“Well May be in a year or two”

Da qarfi hasheem yace “what! Ze wuce UK ne, uncle ya sani?”

“Yeah shi yace ya tafi da su Sam”

“Sam kuma?! Ahhm ahh...is all right ina zuwa” yatsunsa biyu yasa saman goshi yana murzawa, kan ya zube hannuwansa saman table yana girgiza kai ya kalla agogo 11:45am key ya d’auka da wayoyinsa ya fita bayan ya barwa sakatarensa sallahun kowa yazo ace ya fita a dawo da yamma.

***
Driving yake amma hankalinsa baki d’aya na kan wayar sa dake haske ba damar dauka.

Juyawa tayi cikin lafiyayyen baccin da ya d’auketa tun barinsu kano, Mafarki take gata kwance saman gadon ta gefen ta daddy ne kwance yana kallonta a hankali tashiga bud’e ido

“Morning daddy” ta furta murmushi d’auke a fuskarta,

Gyara zaman medicated glasses din idonshi yayi

Yace “morning mami” yayi pecking goshinta, hannu tasa ta maida cincinrindon gashin kanta baya, ta matsa kusa da shi tare da d’ora kanta saman kafad’arsa ta rungume hannunsa a jikinta,

“Have you saw him?”

‘Daga ido tayi tana kallon fuskar daddyn tace “who?..”

Murmushi yayi tare da Jan dongon hancinta yace “the one Mami”

Jimm tayi tana kallon daddy tace “ he didn’t appear yet, ta turo baki gaba, daddy waye ne haka da ze shigo rayuwana? Bayan kowa guduna yake har dasu Abba, umma,Amir and that monster habibii “ Ta fashe da kuka

Hannu yasa yana share mata hawaye still yana sakar mata murmushi yace “he will come, he will soon come”

Cikin sheshsheqar kuka tace “daddy do you trust him?”

Ya d’aga kai “Yes, he’ll bring no harm to you, he will be your guardian” ya tashi tsaye yana kallonta yana tafiya da baya da baya se da yaje daf qofa

yace “se wata rana mami, Ina sonki “

Qwala masa kira tayi gashi ta Gaza tashi tamkar wacce aka danne.

~
Kuma rirriqe ta yayi da hannu yana qoqarin daidaita motar da d’ayan hannun, bugar bishiyar mangoron da yayi ne ya bashi sa’ar fusge hannunsa daga kan steering wheel ya fincikota had’e da zare mata idanu

Cikin muryar bacci tace “i...a..m sorry.”

Be kulata ba haka be sake ta daga ruqon ba, se bin jikinta da yake da ido har ta fara ruqunqume kanta taga yasa hannu ya had’a ta da jikinsa da qarfi har tana iya jiyo bugun zuciyar sa

“U r safe”ya furta cikin sanyin murya,

Ihun da munu ta saki ne yasa su d’agowa da sauri, ta zaro idanu had’e da rufe bakinta da hannu, maida idonsu sukayi ganin su saman wani tsibiri qwaqqwaran motsi idan su kayi zai iya ja motar ta hantsula

Numfashi Sam taja tun qarfi lokaci d’aya ta fad’a saman qirjinshi a sume.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(19)

(For the 2nd time dirty human being kwance jikin Anwar😆)

Ware ido yay waje yana kallonsu duka duk ya rud’e wannan shine ba’a motsi ranar mutuwa shin meye mafita?

Hannu ya zira ta baya ya bud’e qofa, yace “ Ke d’auki kayan nan ki sauka a nutse”
Munu kamar tsutsa ta shiga cilla ledar kayan su waje taja jiki ta sauka, bud’e qofar side din da suke ke da wuya motar ta shiga gilu gilu wanda yasa munu fashewa da kuka.

Rintse ido yay yaja salati, a hankali ya matsa gefe ya fad’a waje wanda yayi daidai hantsulawar mota cikin tafkeken Ramin da ko qasansa ba’a gano wa.
Chapter 12 · 0% Book details