← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 30

Sashe 25

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A fusace hajiya maryam tace "Kasancewar sa me kud'i, k..ku..ma taya kike tunanin zan jure ganin kinyi aure kin barni ni da na girme miki da shekara kusan uku!..kinsan baqincikin hakan ne yasa ranar d'aurin aurenki na gudu bq d'in gidan kaka na 'buya ina kuka ashe a d'akin aka sauki baqin da suka zo d'aurin aure daga kano...daga cikin ma'boyata mahaifin namadi yaron Alhaji d'anqasa yana d'aya daga cikin wayanda aka sauka, daga ma'boyata na hangi shigowarsa ya shige band'aki fitowarsa tayi daidai da tashina zan fita naji ya janyoni na fad'a kansa a lokacin ya lalata min rayuwa...,tun daga wannan ranar na ci alwashin rama gi'bin da yayi min, a lokacin dana bincika naji labarin rasuwar sa yasa na maida hukuncin kan d'ansa namadi..shine dalilin da yasa na aikata haka..."

Dariya jamilu mainasara yayi "to Alhamdulillah tunda har kin iya fad'ar dalilin ki amma ki sani ba wai mun yarda bane, na sani asiri gaskiya ne tunda har ya kama Annabin mu, amma maryam komai yana tafiya da hali ni kuma a gaskiya na gaji bazan iya zama da macen da take iya kisa ba saboda hak na yanke igiyar aure na biyu daga kanki kije su tafi dake ..."

Rayya ta yanke jiki ta fad'i duk suka yo kanta harda hajiya maryam se de tun kan ta qaraso me girma gomna ya umarci CP ya shigo da mutanensa ya tafi da ita,

Ihu hajiya maryam ta rinqa yi fad'i take abarta ta ga lafiyar 'yarta amma ko kallonta gomna beyi ba, sema barin d'akin da yayi.

***
Haka rayuwa ta kasance yau dad'i gobe akasin haka, yau sati biyu kenan da fitowar su mummyn sam ba laifi ta samu lafiya se rashin qwarin jiki wanda hasheem ya tabbatar musu idan ta juri cin kayan gina jiki zata dawo daidai bada jimawa ba already yau kwanakin su biyu a gidan kawu kabiru wanda daqyar me girma gomna ya aminta suka tafi a cewarsa ai shima he is part of the family, sede tafiyar data kamashi zuwa france ne yasa ya yarda su tafi har ya damqa musu ragamar kula da Rayya dake kwance a asibitin hasheem dan sam jikin nata yaqi dad'i,

duk wannan dramar da aka sha su Sam basu san abinda ke wakana kenan ba, kamar ko yaushe tafe suke su uku zuwa hostel ko wannen su da abinda yake tunani, numfashi sholey ta sauke bayan ta juya ta kallesu duka

Tace "kunsan me?"

Girgiza kai Sam tayi, munu tace "se kin fad'a"

"'Dazu mami na ke fad'a min shatima ya kira ta wai zasu kawo lefe"

"Ya fad'a mata ba ma ke ba?" Munu tace cike da mamaki,

"Hmm, ance miki kunyarta yake wannan ta'b, ai yacce kika san ba yayar sa ba ko dan first cousins suke da ita, kuma kinsan yau sati d'aya bana picking call d'insa"

Kafad'a munu ta d'aga "oho dai yaje tunda dai munayin sa ai shikenan"

"Ke de bari qawata" cewar sholey suka tafa suna dariya, murmushi Sam tayi tace "congrats sweetheart"

Rugumeta sholey tayi, "All thanks to you, tunda kece kika fargar dani na hango the Angel within him"

"Group hug" munu tace tare da fad'awa kansu cikin dariya suka ce "wayyo zata karya mu"

***
_Can't you call kiji ya muke silly girl_

Karanta message d'in ta kuma yi _silly girl_ mutum d'aya ke ya'ba mata kalmar nan, zaune ta tashi da sauri tana kuma maimaita kalmar bro A sunan yayi ringing cikin kanta,

All this while dama shi ke tura mata saqo har yake kiran kansa da husband d'inta! unbelievable, baki bud'e ta koma tun farkon saqon daya fara tura mata tana karantawa.

Saurin dialling number munu tayi dake sun fita shopping da sholey, tana ta ringing bata d'aga ba haushi yasa ta wurga wayar kan pillow game da kwantawa ta rungume qafafunta a qirji gabanta na wani irin bugawa "me bro A yake nufi...ya Allah kasa ba gaske bane na shiga uku na samu na cire bro B a raina kuma ga wannan! Innalilllahi, hawaye masu zafi suka siraro mata

Thinking of him alone yana sa zuciyarta wani irin bugu, kenan shiyasa yake mata iskanci, ta waro ido waje game da fad'in wayyo!

Ta jima a kwance zuwa can tasa hannu ta d'auko wayarta, ta shiga kiran layin Ammi a lokacin suna tare da mummyn Sam suna hira, Ammi na bata labarin auren Sam da Anwar, mummyn Sam tana kuka wanda kallo d'aya za kayi mata kasan kukan farinciki ne saboda murmushin dake manne saman fuskarta,

Ringing d'in wayar yasa ta tsaya da cewa "Samira is calling.."

Cikin rawar murya tace "Pls put it on speaker"

Kai ta d'aga, "hello Ammi na"
Zirrrr hawaye suka zubo wa mariya,

"Samira na nayu fushi se yau kika tuna da ni"

Cikin shagwa'be murya tace "Allah Ammi ba haka bane, mss paticia ce tasa mu kashe wayar dan kar tayi distracting d'in mu daga karatun exams"

"Oh samira na wasa nake miki, how have you been, ya exams d'in?"

"Alhamdulillah, nan da 4days zamu yi hutu gashi bakwanan"

"Yea, Ann yace ba zaku zo gida ba har se kun gama session d'in baki d'aya,"

"Ammi.. yanzu..yaushe zaku dawo to?" Ta qarashe a shagwa'be

kukan mummyn Sam ya d'an kufce dan har Sam se da ta jiyo,

A rud'e tace "Ammi is everything okay?"

Saurin riqo hannunta mariya tayi game da girgiza mata kai alamun kada ta fad'a mata,...jinjina kai tayi cikie da tausayin 'yaruwar tata tace

"Lafiya, kin ga canjin weather yasa mura ke neman kama ni"

"Ayyah sorry, yanzu when are you coming back"

"Insha'Allah in two weeks time, akwai matar uncle d'in su Ann da muke zaune anan, ta haihu yau da safe so inaso ta samu qarfin jikinta sosai sa'annan mu dawo"

"Okay Ammi, bara na barki"

"Okay dear, ina 'yanuwanki"

"They went for shopping"

"Meyasa baki je ba?"

"Period pain yasa ni gaba Ammi"

"Have you take a medic?"

"Miss patricia tace wai ba'ason ake shan magani"

"Or sannu kinji make sure you relaxed kada kiyi motsi da yawa and drink some fruits uhm?"

"Ok Ammi take care, i love you"

"Bazaki ce na gaishe da brothers d'inki ba?"

"..send my greatings to mu'allim bello" da fad'in haka tayi saurin ajiye wayar dan haka kurum taji fad'uwar gaba tun kan ta ambaci sunan Bro A.

***
"Meyasa kika hanani fad'a mata, do you know how joyous she will be?" Cewar Ammi tana qoqarin ajiye wayar bisa bedside drawer,

"..bana son ta shiga wani state ne, baki ji ba Sam d'ina ta girma har tana yin period" ta qarashe cikin dariya me had'e da kuka

Kai Ammi tayi nodding,

Muryar umma salamatu wacce shigowarta kenan ta doki kunnuwan su,
"..she will be more than happy idan ta ganki a raye, she always says she misses you kullum dare se tayi kukan rashinku a gareta..nayi hasara rashin bata soyayyar uwa dan Allah ki yafeni mariya wullahi banyi hakan a sanina ba..Ameer yau satinsa guda baya ci baya sha duk ya fita hayyacinsa, yace lallai na nemo masa Samira ya nemi afuwar ta idan har ina son ya koma yanda yake, dan Allah ku agaza min" ta durqushe a gabansu cikin zubar hawaye,

Kallon kallo sukayi tsakanin su, kan Mariya tace "muje na ganshi"

Umma salamatu tayi leading d'insu har d'akin sa, inda yake kwance rigingine idonsa bisa sealing hawaye na zubo masa, babu me cewa shine Ameer d'in Sam d'innan me wasa da dariya, ya rame duk ya fita a hayyacinsa,

Zama mariya tayi kusa da kanshi game da d'ora hannunta saman sumar shi,
"Ameer d'an lukuti me qaton tumbi me kama da bulun boti..." d'ago kai yayi game da fashewa da kuka bayan ya kwanta saman cinyar mariya,

"Itace waqar da take yi maka a duk lokacin da kazo gida back then can you remember? You are morethan a brother to her Ameer, duk abinda kayi wa Sam zata yafe maka, duk abinda ya faru kayi ba'a cikin hayyacinka ba, dole zata yafe maka uhm? Ka cire damuwa a ranka, inaji a jikina zata yafe maka"

Cikin kuka yace "mummy kin tabbatar?"

Kai ta d'aga "insha'Allah, maza zauna muci abinci kaji, yinwa nake ji and dont say no" ta nuna shi da yatsa in a playful way,

Kallon ummasalamatu yayi kan yace "zanci nima"

Nan suka zauna suka ci abincin ana ta'ba hira wacce take tun tada ce da haka har ya qoshi suka tafi suka barshi zeyi wanka ya fito falo,

***

Bello da Anwar ke zaune suna hirar bayan saduwa cikin office d'in hasheem wanda ya tafi dubo lafiyar Rayya,

"Kana son ce min first cousins muke da Sam all this while bamu sani ba?, Allah is great♡" cewar bello cike da farinciki mara misaltuwa

Numfashi ya fursar tare da gyara zama ya had'e hannuwansa wuri d'aya bayan ya kuma kallonshi ya d'anyi one sided murmushi

"Yeah, and Rayya too"

"Alhamdulillah..you know what? Yanzu komai zaizo min cikin sauqi insha'Allah.."

'Daga gira Anwar yayi, "mene?"

Ya tsugunna gabanshi "Bro A amanata, she's going to be mine, i'm willing to make her mine officially.."

Duniyar yaji ta tsaya mishi cakk babu abinda yake iya jiyowa se sautin dariyar Bello game da hamdalar da yake...amanar sa??? Ya ayyana a ransa, kan ya jiyo shi yana fad'in

"Yes Samira..i love her so very much..."

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(31)

..hawaye masu d'umi suka ciko idanunsa, yayi saurin sharesu da hannu kada bello ya gani, yayi saurin miqewa ya fice da sauri har suna neman yin karo da hasheem

"Bro A"

Yana iya jiyo muryar bello na kiransa but bashi da courage d'in fuskantar sa a halin da yake yanzu!

There is only one way out! Bello be ta'ba neman abu ya rasa a wurina ba face nayi masa, se idan bani da halin yi, wu'ka da nama duk a hannuna suke, dole nasan abin yi, ya ayyana hakan a ranshi,
Chapter 25 · 0% Book details