← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 30

Sashe 3

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Zan le’ka gidan sa’idu ne, bazan jima ba mubi na nan ku zauna yanzun zan dawo kinji”

Fad’ad’a fara’arta tayi, “ok umma Allah ya dawo dake lafiya”

Mubi ta d’aga mata hannu, ta fice.

Bayan gushewar kusan minti arba’in suka ji bugun ‘kofa, “ina zuwa”Sam tace da mubi ta nufi downstairs,

For kusan 20mins jin shiru Sam bata dawo ba despite kiran da take ‘kwala mata yasa mubina bin bayanta idan har kunnenta ba ‘karya suke mata ba tana iya jiyo muryar Sam na pleading daga can bayan gidan a guje ta nufi hanyar me zata gani?

“Ya habibii? What are you doing?” Ta fad’a cikin kakkausar murya

Ba zato yaji muryar ya waiwayo yana sakin wani yaudararren murmushi “oh mubina yaushe kika zo?”

Kallon da take watsa wa hannun dake cakume da hannun Sam ne yasa shi saurin saki yana shafa kai “am umm...a..”

A fusace ta janyo Sam suka nufi d’aki bayan ta zaunar da ita bakin gado tayi folding hannu “is he beating u”

Cikin rawar murya tace “no, it’s just his natural way of treating me “

“What!? Amma meyasa baki fad’a ma umma ko baffa sunyi masa fad’a ba, can’t you ever stand for yourself kinga fa ya habibii is so mean”

“Don’t worry mubi May be bayason zamana gidansu ne, afterall nan da kwanaki kad’an ze tafi, and I will be back to my normal self “

“Uhm, zo muje muyi game”

“Wanne?”

“X and O”

Da fara’a ta girgiza kai suka nufi d’aki

****
*Birmingham, London UK*

Tsananin azaba da hucin sanyi yasa kowa ka gani sanye yake da cardigan babba da hular kai har dasu safar hannu dana ‘kafa, hakan take ga magidancin dake driving motor d’insa yana kuma ansa kira at thesame time

Daga can ‘bangaren aka ce “uncle please kataimaka min na dawo ko da na wata d’aya ne AB machinaries need me, kaga nan tunda bro B yana nan....”

Tun kan ya kai aya ya katse shi “hey mr Man oh let me call you with your name, Anwar bana san kame kame ka zama babban kwabo kenan tunda har ‘kaninka ze iya abu amma kai baza kayi ba, wannan ne taimakon da kake ta ikirarin zaka yi? Ko kuwa ka manta al’kawarin da kayi na DABAIBAYAR al’amuran nan, ka manta da Ammin ka...”

“Uncle na kasa samun nutsuwata I don’t know what to do, amma Insha’Allah ko dan al’kawarin da na d’auka sai na cimma burina ko da zai zama aikina na ‘karshe a doron ‘kasa, but before that uncle inason hutawa inason ganin ammi na i missed her...”

“...and AB machinaries ko?, kai wannan yaron da ace ba a nigeria aka haife ka ba da bansan yanda zakayi ba, zaka zo hutu amma na 2weeks kawai ka tattara komai ka barshi a hannun qaninka”

“Yesss that’s my super uncle, I love you muah” ya manna wa wayar kiss ya shige gida.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(5)
Bayan wasu kwanaki...

Firgigit ta tashi jin yadda ake buga ‘kofar d’akinta kamar za’a ‘balle, a iya ‘kiyasinta yanzu sha biyun dare ta wuce tabbacin kowa na gidan ya jima da kwanciya to wane haka? Ko de horror ne yazo cinye ni tunanin daya kuma rud’ata kenan har takai ga zubda hawaye jiki na makyarkyata, can ‘kuryar gado ta ma’kure kanta kira take
“Daddy...wayyo umma na...um...” kan ta’karasa aka banko ‘kofar tun ‘karfi wanda yayi daidai da d’aukewar numfashin ta.

Washegari
Kwala mata kira ta ke tun ‘karfi amma shiru kakeji wai malam yaci shirwa, “kai yarinyar nan kuwa Anya lafiya?

Baffa ya sauke jaridar dake hannunsa yace “kinsan fa yau saturday qila bata farka ba”

“Haba Abban yara sha d’aya fa ta gota ri’ke min yarinyar nan kaga bara na dubo ta”

Fad’owa yayi d’akin kamar wanda aka wurgo kallon sama da ‘kasa ta masa
“Kai lafiya naganka a firgice?”

Sana’ar tasa yayi ta susar kai yace “ko d’aya uwarmu kawai de...”

“Kawai de me?, kai gafara da Allah naje gun d’iyata” fuu ta wuce sa, fuska a cakud’e ya isa gaban Abba ya zauna yana faman kukkumbura “ya dai yayana?”

“Abba wai meyasa umma kullum take son min fad’a ni idan batason ganina ne ba se nayi komawa ta ba”

Murmushinsu irin na manya yayi kan ya Kada baki yace “yayana kenan ka ta’bajin inda uwa ta guji d’anta?...”

“To amma Abba baka ganin kullum kullum...”

“Kayi haquri kasan umman taku gidan gargajiya ta taso har da kunya irin ta d’an fari yasa take maka haka bawai intentionaly bane,um?”

“Abba shekarar ta nawa a birni nazata duk qauyencin mutum idan ya shekara arba’in ze dena amma...”

A tsawace Abba yace “kai da Allah can banson sakarci mahaifiyar taka kake fad’ar haka a kanta, To lallai yau na kuma tabbatar da kanka yana da matsala dole mahaifiyarka take complain a kanka tashi ka bani wuri” ya ja tsaki rai a ‘bace, cikin tafiyar bouncing ya nufi hanyar waje

“Ka kintsa dan jirgin ‘karfi biyar zaku bi”

Wani qululu ya tokare mishi wuya a zuciye ya nufi waje dede lokacin da ihun umma Salamatu ya iske kunnansu

A kusan tare suka fad’a d’akin, Amir ya tsugunna gabanta yana jijjiga ta “Sam Sam ki tashi! Sam wake up please”

Umma salamatu dake a firgice ta nufi kawu “Abban yara Sam..Sam bata motsi” rasa abinyi yay kawai ya ciro hular kansa yana firfitu dan duk da AC dake d’akin d’igar gumi yake.

Amir ne ya shiga girgiza sa “Abba muje hospital, Abba banson wani abu ya samu Sam”

Aljihu ya shiga laluba fad’i yake “ina kake ina na ajiye “ ya d’ago kai yana kallon habibii “kai maza d’auko key “ ya cicci’be ta suka nufi parking lots inns salamatu na sa’be da safiyya kafad’a .

*one hour later*
Likita ya kalli Alhaji kabiru a fusace “malam anya kuwa yarinyar nan ‘yar kace kamar yanda ka fad’a yarinya qarama ace tana d’auke da hawan jini?”

Murya na rawa umma salamatu tace “Ha..w..an jini likita?” Tare da dafe qirji

“Kwarai kuwa hajiya, am sorry to say amma a gaskiya ku kiyaye dan bugun zuciyarta am ba daidai yake ba, ko zaku iya tuna wani abu daya faru da ita jiyan?”

Umma tace “umm to gskya bama ce ba dan lafiya qalau muka rabu da ita ta shige d’aki ta kwanta”

“Basu samu matsala ba, kuma ba wanda sukayi fad’a dashi cikin yara” ya nuna su Ameer da ya hannu, habibii kuma se dad’a had’e rai yake, umma ya kaikace tana duban sashen habibii

“Umma” ameer ya furta yana kallonta yana girgiza kai ta juya gun doctor “babu”

“Well To gskya de zan baku shawara ku rinqa bincikar a wani hali ‘yarku take ciki dan tabbas firgici ne yasata a wannan halin and again zan riqeta ta kwana biyu zuwa ta warware,

“To bari muje mu dawo Ameer Kai se ka....”

“Amm hajiya karki damu kanki, anan asibitin mutanen waje basa jinya munada wadatattun ma’aikatan da zasu kula da ita”,

“Amma ta yaya...”
Yana sakin murmushi yace “karki damu she’s safe with us”

Kallon kawu tayi ya girgiza mata kai tace “To shikenan ma iya ganinta kan mu tafi”

“Sure! Munirat munirat “

Wata matashiyar nurse ta shigo da sauri ya nunata “wannan ce zata zauna muku da ita zuwa lokacin da zata dawo daidai, ya kalleta take them to room no.18 VIP,
“Yes sir” ya furta ta na me russunawa
Kan tayi gaba su mara mata baya.

Daidai shiga d’akin wasu matasan maza biyu suka fito daga ciki kasancewar bayan su a juye yasa Amir saurin cewa “who are those guys??”

Nurse munirat tace “am.. ss..tudent ne suna bin rooms dan duba patient”

“Students a private hospital?” Cewar habibii

Duburburcewa tayi “am..a..”

“Haba mana habibii kar ka rud’ata mana ba kaji me tace bane d’aliban lafiya ne, muje da Allah, kuyi tafiyar ku” ta qarashe zancen idonta a bayan matasan, gaba sukayi batare dako waiwaye ba.

Kafad’a habibii ya d’aga irin ko a jikina, yayinda Amir ya riga kowa shigewa d’akin

Kwance take sam’bal saman gado doguwar rigar baccin mark&spencer kalar pink tabi jikin nan ta lafe har kana iya gano ‘yan qananun boobs d’inta, gashinta dake barbaje saman pillow nurse munirat tabi ta kame gu d’aya tare da Jan farin quilt ya sakaya mata jiki, fuskar nan tayi kuyat takoma pink zirr abinka da farin mutum idanta dake luhu luhu har yanzu da d’igo d’igon busassun hawaye

Hannunta d’aya an ma’kala drip yayin da d’ayan hannun ke manne cikin na Amir
“Allah ya baki lafiya, Sam”
“Amen, nifa Abban yara abin nan ya d’aure min kai shin me ya razana Sam har ya shiga wannan halin”

“Ko dai mugun mafarkai take umma”

“Banajin Amir, na fi ta’allaqa abin ga d’an uwanka Anya habibii ba kaine ka jef...”

“Haba umman su, fisabilillahi ya kamata ki kawo maganar nan a nan, kai ku tashi mu tafi ma”

“Abban yar...”

“Kinga tashi muje kinsan halin da take ciki yanzu bata son hayaniya”

Mi’kewa tayi tana fad’in “uhm yaushe ka zama likita kuma bansani ba?”

Bece uffan ba ya nufi ‘kofa, yayin da umma ta matsa bakin gadon ta shafo sumar Sam, “Allah ya tashi kafad’unki” saman goshi ta sumbace ta, safiyya dake hannunta ta rinqa zillo tana son sauka gurin Sam.

Nurse munirat dake gefe tsaye tace “hold on beauty yayarki bata da lafiya”

Umma tayi dariya “ai akwai shaquwa tsakaninsu, nurse ga ‘yata nan a kula min da ita sosai dan Allah I can even give you some extra cash”

“Kai haba hajiya bakomai ai aikinmu ne kuma ana biyanmu isassun albashi. Nagode”

“Shikenan ya amanarta nan” ta fita

Nurse munirat ta kalli gadon a fili ta furta “yacce kike me kyau am very sure haka zuciyar ki take”

“Stop admiring her and do your work,”

Saurin sunkuyar da kai tayi tana Sosa gefen wuya “am sorry sir” tayi saurin bi ta gefenshi ta fice, daidai lokacin akayi knocking bisa ‘kofar

“Yes come in”

“‘Daliban lafiya” ya furta cikin dariya

Kanne masa ido babban yayi, suka tafa da likitan

“Maza how far now? Kun ganta ba?”

“Yeah...”

“Ah ah fa Bro A wancan mutanen basu bari mun ganta sosai ba..”
Chapter 3 · 0% Book details