← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 30

Sashe 21

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata iyamurar mata irin masu kula da masu laifi d'innan ta kalle ta tana girgiza kai dan taji duk abinda take fad'a, ciki da tausayawa

Tace "dukkan ku da kike gani anan shed'an ke rinjayar ku, gara ma ke kinsan zaki fita, da yawa anan sede a fidda gawar su? Kinga meye ribar kenan? Ina me baki shawara duk da bansan kalar lefin ki ba, da ki amfani da lokacin ki anan ki nemi gafarar ubangiji dan rayuwa yanzu ba ta da tabbas, mutuwa kuma bata neman shawara"

Kukan tane ya dad'u, cikin sanyin murya tace "nagode da shawara insha'Allah zanyi yadda kikace d'in", tun kan ta rufe baki aka shiga qwala kiran batch C grp dinsu kenan, kallon matar tayi had'e da miqewa ta nufi gurin aikin da Allah kad'ai yasan ranar gamawa.

***
Hannunta biyu tasa tana jijjiga qofar cell d'in ciki karaji take fad'in
"Ku bud'e min qofa nace! Tun kafin ku gamu da fishina, shin ko kunsan ni d'in wacece..."

"Her excellency hajiya maryam jamilu mainasara..or let me just call you kidnapper..tsk tsk tsk uwardaba suits you best.."

Ido, hanci, baki duk ta saki cikin rawar murya tace..." your excellency dan girman..."

"...dakata maryam!! Wullahi tallahi bazan ta'ba yafe miki ba har gaban abada! Kuma ki sani bawai zan sawaqe miki bane i will keep you hostage sede ki sani le da dabba a wurina babu maraba! Ki shirya abinda zeje yazo" da fad'in haka ya juya ya fice cikin qunar rai, Allah kad'ai yasan meke zuciyar shi.

Bayan kwana biyu...

"Ammi duba yanda duk kika fita a hayyacinki dan Allah ki kwantar da hankalin ki..."

"Ann...mariya...tana raye cikin qunci da wahalar da Allah kad'ai yasan adadinta for almost 13 to 14 years ya kake ganin halin da zamu same ta ciki..."

"Ammi bro B yace she's fine and fine means fine insha'Allah, so please muje ki zauna a motor na janyo trolley mu tafi kada muyi missing flight"

Cikin zubar hawaye ta girgiza kai, shi kuma ya koma ya janyo kayan, bayan yasa cikin booth ya nausa motar bisa kwaltar dake shimfid'e cikin company d'in.

Hannu tasa ta d'auka wayarta dake vibrating mss patricia tagani nan da nan ta murmusa kan ta qaga a kunne had'e da sallama

"Ammina.." ta furta in a shaky voice,

"Sam my daughter, how are you?"

"Good, ammi kina lafiya?"

"Same here, i'm on my way to the airport"

"Airport? Ammi ina zaki tafi ki barmu?"

Ido ta lumshe cikin kukan zuci a fili kuwa cewa tayi "nigeria sweetheart zanje ganin bello i will be back in 2days insha'Allah"

"Ammi kizo muyi sallama pls inaso na ganki"

Hannu tasa ta matse idonta had'e da jan hanci ta kalli Ann, "can we make it? Ina so mubi ta saint teresa"

Kai ya d'aga tare da juya akalar motar zuwa titin da ze kai ka makarantar,

"Gamu nan zuwa"

Kai ta d'aga kamar tana gabanta, ajiye wayar keda wuya munu ta fad'o d'akin, kallon mamaki ta bita dashi ganin tana ta faman cleansing face d'inta fara'a kwance saman fuskarta , tamkar ba ita ce ta bari kwance magashiyan ko lectures ta kasa zuwa.

Kula da irin kallon da munu ke mata yasa ta juya qwayar ido tace "fine naji sauqin jiki na ne, and yes ina goge face d'ina coz banson Ammi ta ganni wani iri"

Ido wide open munu tace "is she coming.."

Kan ta bata amsa wayarta tashiga ringing nuna mata screen d'in tayi game da cewa "yes ta qaraso" light yellow veil kalar atamfar jikinta ta yane kanta dashi, tasa hannu ta amshe littattafen hannun munu ta ajiye game da jan hannunta sukayi waje.

Tun daga nesa yake hango fararan hakwaranta garai garai tamkar qanqara, murmushi yayi me kamar ajiyar zuciya yayi crossing leg d'insa daga tsayen da yake kusa da kujerar Ammi ya rungume hannun hagunsa a qirji yayin da hannun damansa ke tallafe da fuskar sa yana tapping hancinsa da yatsa (manuniya),

Na mujiya ya zuba mata from head to toe ya shiga qare mata kallo, takalmi ne flat sanye a qafarta shi ba lemon green ba haka kuma ba yellow ba, skirt ne pencil wanda ya fallasa dukkan wani curve na jikinta, yayin da idonsa ya sauka saman rigar jikinta kuwa taune lips d'insa ya shiga yi game da had'e rai, lips d'inta dake kyallin farin lipbalm kuwa seda ya sashi d'auke wuta na wani d'an lokaci, idanunta da sukayi d'an jaja-jaja ya qurawa ido ta rame shine abinda yayi crossing mind d'inshi bata da lafiya ne? Ba amsa , gaza d'auke idonsa yayi daga kanta sema gyaran murya da yayi yashiga amsa gaisuwar da suke masa,

Rungume take jikin Ammi suna sallama, bayan ta d'agata karaf sukayi ido hud'u, tsintar kanta tayi da son kallanshi wanda hakan yayi mutuqar faranta ransa ko banza he will be able to look into those white and black balls she's the definition of beauty zuciyarsa ra fad'a masa hakan a tare suka d'auke kai,

Ammi ta d'anyi dariyarsu irin ta manya, idonta a kan munu da itama ta kula da kallon kallo da suke,

"Munu zo ki raka ni gurin mss chloe mu gaisa kada tace nazo ban leqata ba"

Kai ta d'aga tana satar kallonsu, "Ammi bari na b..."

"No kuje muna jiranku" yace his eyes still fix on her's,

Tura baki gaba tayi idonta akan hanyar da suka bi,

Yatsa ya d'alla mata saman lips ta saki wata kasalalliyar qara , cikin kunnenta yace "kinci sa'a Ammi is around da se nayi punishing bakin rashin kunyar" ido ya lumshe lokacin da hancinsa ya shaqi qamshin gashin kanta har be san lokacin daya furta

"Wani irin turare ne wan..nan?"

Dad'a runtse tayi kanta setin qirjinsa cikin sarqewar murya tace...

©️Kdeey 😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(27)

"..ou..dul arab.." ta qarashe maganar cikin in-ina, girgiza kai yayi har sajen shi na gogar gefen fuskarta, jin da tayi kamar taku na tunkaro su yasa tayi saurin tura qirjinsa da hannu, taja baya tana sauke numfashi kanta a duqe tamkar mara gaskiya

"Ann muje ko?"
Numfasawa yayi game da bud'e lumsassun idanunsa, "yea, muje Ammi na"

Murmushi tayi masa kan ta maida kallonta gurin Sam, miqa mata hannu tayi "muje ki rakani kinji samira na"

Cikin sissinna kai ta zira hannunta cikin na Ammi suka nufi wurin mota, tsayawa tayi game da waiwayo wa cikin sakin qaramar dariya tace "munu wai meye sirrin ne naga se qiba kuke yi kamar ana hura baloon?"

"Laa Ammi wlh babu komai, sede ko weather d'in garin ne ya amshe mu"

"Shiyasa kuke qiba kenan?"

"A a Ammi fa yinwar ganin kice ni dai take sani qiba" ta qarashe a shagwa'be, jan hancinta Ammi tayi "eh shiyasa naga kin tsaya gun d'anuwanki baki bini ba"

Ji tayi tamkar qasa ta tsage ta shiga ga wani tsananin fad'uwar gaba da taji, 'ko de Ammi na zargin wani abu ya kuma faruwa tsakanina da bro A' rau rau idonta ya ciko da ruwa, jan hanci tayi idonta a qasa cikin muryar kuka tace "Allah Allah Ammi.."

Gyaran murya yayi idonsa kan fuskar Ammi yace "mami mun kusa latti"

Gyad'a masa kai tayi, kallon sam tayi cike da qaunar gudan jinin 'yaruwar tata tasa hannu ta goge mata fuska tana girgiza mata kai,

Se da ta zauna tace dasu "to yanzu de na kauda yinwar ko, se ku maida hankali sosai a karatun ku dan mss chloe ta shaida min cewa soon zaku yi exam so ku dad'a riqe damtse kunji, make us proud uhm" suka jinjina kai

"Insha'Allah Ammi"

"Good, Allah yayi muku albarka"

"Ameen"

A sanyaye tace "Ammi.."

"Uhm, samira na"

"Bansan meyasa ba inajin wani iri tamkar wani abu na shirin faruwa, kuma kwana biyu bana mafarkin daddy na da haske"

Jimm Ammi tayi cikin tunani kan tace "khairan insha'Allah, ki yawaita salati koma mene Allah ze maye shi da alkhairinsa, daddyn ki ma ki yawaita masa addu'a akan wacce kike masa"

Kai ta jinjina, a tare sukayi musu addu'ar sauka lafiya, suna nan tsaye har seda motar ta 'bacewa ganinsu.

***
Kimanin awanni biyar kenan da su kayi transit a Dubai, cikin wani restaurants dake cikin airport suke zaune Ammi is busy with her coconut milk shi kuma yana zaune ko kwanciya za'ace idonsa lumshe yana sipping watermelon drink

Daga inda take zaune ta shiga leqen fuskar sa,"is everything okay Ann?"

Firgigit yay, yana qarasa had'iye lemun bakinsa "bbbakomai.."

Jimm tayi kan murmushi ya maye fuskar ta, "do you really love her this much?"

Saurin kallonta yay tamkar wanda aka tsikara, kan ya hau kame kame irin na marasa gaskiya, qwayar idonsa ya sauke saman agogon rolex dake saqale da hannun sa yace "Ammi remain 20min jirgi ya tashi lets go" ya ajiye lemun yayi gaba da sauri yana susar qeya, bin bayansa tayi da ido murmushi maqale da fuskarta tana jin wani irin farinciki cikin ranta.

*Kano Nigeria*

Hannu biyu tasa ta tallafi wayar dake kunnenta, cikin muryar kuka take fad'in "doctor mami na,.."

Hasheem dake tsaye jingine da qofar d'akinsa cikin tashin hankali yace "Rayya, calm down please kinsan condition d'inki..."

"How the fuck do you want me to calm down bayan mahaifiya ta na cell.."

"Babe tsaya ki saurareni ba nufi na kenan ba, i assure you mahaifinki baze ta'ba bari ta wuce daren yau ba.."

"...kaima ka fad'a daren yau amma ta kwana a qasqantaccen wurin nan ai ko! Can't you get it! Damn it" ta katse wayar had'e da fashewa da marayan kuka, cikin kuka take fad'in "na zata kaine wanda zaka sharen hawaye na in my tough time ashe i am wrong, meke faruwa ne?" tashiga dukan goshinta da hannu.

~

Cirko cirko suke cikin cell d'in ko wannen su na hura hanci, aqil cikin qunar rai ya kaiwa salihu duka a hanci nan da nan kuwa jini ya hau zuba,

Durqushewa yayi, kan ya d'ago shima ya kai masa dukan "me nayi maka da zaka kai min mazga"

"Kana so kace ba kai bane ka nuna masa hideout d'inmu ba!" Nan f kokowa ta kacame tsakaninsu,
Chapter 21 · 0% Book details