← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 30

Sashe 20

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dss bashari, col. Najib (labarin aurena), tare da bello ne ke zaune a office d'in Najib suna shirya yanda operation d'in ze kasance, knocking a kayi bisa door

"Yes" najib ya amsa, wata budurwa me matsakaicin kyau ta leqo "sir me girma governor ke neman iso"

"Let him in×2"

Suka miqe a tare dan girmamawa a daidai lokacin da jamilu mainasara ya shigo, sara wa najib yayi fuskarsa d'auke da murmushi,

"your excellency sir" auka furta hakan a tare , da hannu ya nuna musu

"pls have a seat"

Sabuwar gaisuwa suka kuma yi, yace "Anwar right?" Yace idonsa kan fuskar bello,

Hasheem ne ya amshe da cewa "qaninsa ne bello"

"Uhum? Yeah se yanzu na kula wancan be kai wannan haske ba"

"Yes sir " bello yace in a low voice.

"Hasheem ya wajen manya"

"Lafiya qalau sir" yace cikin shafar kai cike da kunya, jinjina kai yayi kan ya tattara hankalinsa kan col Najib,

Yace "colonel akwai labari ne, dan daga ni had'uwar nan taku waje d'aya akwai magana"

Dariya col najib yayi "we all went to thesame institute"

Gira ya d'aga had'e da karkace kai yace "hmm, shi kuma wannan (hasheem) shine siriki na"

Jinjina kai najib yayi "Masha'Allah Allah ya sanya alkhairi, hasheem nada kirki qwarai, se fatan Allah ya sa albarka"

Cike da farinciki ya amsa da Amen×2.

Shiru ne ya ratsa cikin nutsuwa col najib ya fara jawabi " your excellency sir ina me baka haquri a kan neman gaggawa da ka samu tare kuma da taso ka da mukayi cikin sanyin yamman nan dafatan za'ayi mana afuwa?"

Girgiza kai gov jamilu yayi da hannu yayi masa alama ya cigaba ba komai, "ahm ur excellency sir wannan abokai nane bello da hasheem sunzo min da wani batu ne wanda ya shafeka hakan yasa naga abinda yafi kamata shine ka sani,"

'Dan had'e fuska yayi had'e da jinjina kai yace "ina saurarenka"

Nan suka zayyana masa duk abinda ke faruwa, lokaci d'aya gumi ya shiga karyo masa, fararen idanunsa suka kad'a zuwa ja,

Murmushin daya fi kuka ciwo yayi "wato maryam bazata ta'ba canza hali ba" ya kalli najib da bashari

Ni gomnati na bazata ta'ba d'aga qafa ga duk wanda ke neman kawo naqasu ga alummata ba saboda haka ina me umartar ku da kuje ku kama first lady da yaronta halim, inaso ku toshe kunnuwanku ga duk surutun da zeje yazo, haka kuma inaso hasheem ka tafi da motar ambulance a bawa mariya da yaronta taimakon gaggawa, kai kuma bello inaso ka kira min d'anuwanka da duk wanda kuka san maganar nan ta dangance sa dole a fasa kwai ko zuciyata ta samu sukuni"

Ya tashi tsaye "inaso yanzu ba se dare ba a kamo duk wanda ke da sa hannu a alamarin nan" ya fice muqarrabansa suka mara masa baya,

Ya bar su zaune cikin qullewar kai, hasheem da wayarsa ke ta haske ya duba ganin sunan Wife kamar yanda yayi saving yasa shi sauke ajiyar zuciya game da picking ya fita varender,

Dss bashari ne ya fara miqewa yace "bari mu kamo 'yan daban can mu garqame se mu had'u a can gidan sirrin"

"Hakan yayi, nima bari na sanar su shirya motoci" ya fita.

Bello kad'ai ya rage zaune kansa yake murza wa dan ji yake yayi wa jikin sa nauyi, a hankali yasa hannu ya shiga dialling number Ammi

***
"Bello lafiya naji muryarka haka" tace hannunta riqe da serving spoon da ta gama zubawa Anwar soup dashi,

Kasa riqe kukan yayi har seda ya fito, cikin rawar murya yace "Ammi na mummyn Sam na raye..."

Ludayin hannunta ne ya su'buce ya fad'i jiki na rawa tace "bel..lo me kake cewa?"

Jinjina kai yayi "yes Ammi, ina da tabbacin hakan, yanzu haka a yau zamu qwato su daga hannun azzaluman da suka 'boye su"

Wani marayan kuka ne ya kufce mata, Anwar yayi saurin amsar wayar yasa a kunnen sa, "Bro mekake cewa ne?"

Fad'a masa yayi duk yanda sukayi, yace kuma yayi qoqari su taho nigeria cikin satin nan, haka kuma me girma governor yace a taho da dukkan wanda abin ya shafa.

***
Sanye take da doguwar riga irin ta sudanese d'innan kalar ruwan qwai, kanta yane da mayafin kayan tayi turban yayinda kunnenta ke maqale da earpiece qira'ar sudeis ke tashi cikin suratul baqrah

Ba bacci take ba, dan har tana iya jiyo hirar sholey da munu, gyara kwanciyarta tayi had'e da jan blanket ta rufe fuskar ta dan sam bata son sauraren zancen nasu.

Wayarta da tayi haske ne yasa ta dubawa, _"tafiya ta kama mu, kiyi mana addu'a"_

_waye?_ tayi reply

_mijin ki_

Taga an turo, had'e fuska tayi had'e da jan tsaki, ta ajiye wayar.

Bubbuga qafarta sholey tayi, ta bud'e fuska,

"Ke da wa kike jan tsaki haka?"

"Nothing..is just that nagaji da zama kuma banjin karatu yanzu"

"To kece ai kin wani kwanta, ki tashi muyi hira kin qi"

"Sholey ba haka bane ke da munu baku da aiki se hirar soyayya, gara ke shattima yasan kina yi, ita kuma she's always day dreaming and i have no business with it all, hasalima ba saurayin nake dashi ba"

'Dala mata duka munu tayi tana dariya tace "Allah ya isa, insha'Allah wannan mafarkin da kike raina wa soon ze zamo gaskiya, ke kuma your husband will soon knock on your door" ta qarashe tana me kanne ido,

Dariya sukayi duka, a shagwa'be tace "bazaku gane ba jikina ke min ba dad'i yau kamar wani abu na shirin faruwa"

Sholey ta dakatar da ita da cewa "Heyy why bored bayan kina da ni, yalla ku zo muje yawo"

Taja hannuwansu, "ina?" Sukace a tare, "school tour" ta amsa su

riqe da hannun juna suka mara mata baya.

***
"Meke faruwa ne your excellency?" Hajiya maryam ta furta a rikice

"Take her away" yace ba tare da ya ko kalle ta ba,

Macen soja ce ta matso kusa da ita "ur excellency please ki bamu had'in kai ta yarda komai ze zo mana ta sauqi"

Hannu ta d'aga cikin zare idanu tana yin baya baya "keh kinsan kuwa ni d'in ko wacece i'm the firstlady of this state so babu wanda ya isa ya kamani" ta fad'a cikin karaji,

"Maryam!" Gov jamilu ya furta a hasale

"Ina me umartarki da ki basu had'in kai suyi aikinsu, kada ki bari nasa baki!!"

Gaza furta komai tayi se rawar baki da take, daidai lokacin da Rayya ta fito, bin sojojin da sukayi cirko cirko da bindiga tayi a gefe guda kuma mahaifiyarta ke durqushe a qasa tana kuka, mahaifin ta kuma na tsaya can gefe daban ya juya musu baya ga halim sanye da ankwa hannu da qafa,

A guje ta qarasa shigowa falon cikin inda inda ta rasa ma ina zata nufa, "daddy" ta dafa shi ta baya, waiwayo wa yayi yana me girgiza mata kai

Yace "col kuje dasu, idan wayanda nake jira sun iso zan shaida maka, but please kamar yanda mukayi abinnan a sirrance inaso mu barshi a hakan"

Sara masa col yayi tare da bada umarnin a tafi dasu, sede tun kafin su gama fita Rayya ta yanke jiki ta fad'i.

Juyowa hajiya maryam tayi a guje tayo kanta, a tsawace gov yace " i said take her away" nan da nan akayi waje dasu, a take ya kira asibitin cikin gidan gomnatin aka shiga bata taimakon gaggawa, inda aka tabbatar da suma ce kawai nan da rabin awa zata farfad'o

A can gidan barrister kuwa bello, barr, gwaggo da mom hajar ke zaune jugum jugum tun bayan da bello ya gama zayyana musu abinda ke faruwa ya kuma ce dasu nan da zuwa lokacin da me girma gomna ze neme su babu me fita daga gidan ciki har da yaran gidan.

A can kuma hasheem ke zaune cikin motarsa gefensa ambulance d'in get well ce, daga inda yake yana iya jiyo qarar bindiga da qurar dake tashi zuwa can yaga ana firfito da mutane sanye d handcuffs, alamar da aka yi masa da hannu yasa shi bada odar a shiga da gado a fito da majinyata

Cikin wani underground building cikin wani d'an qaramin d'aki me dubun gaske da yafi kama da cage aka zaqulo hajiya mariya wacce idan ka gani zaka rantse skeleton ce aka aza ta saman gadon aka fita da ita, namadi ma haka aka d'auko shi aka tafi dashi,

Duk dauriya irin ta sojoji seda suka zubda qwalla ganin halin da suke ciki, haka ma hasheem dake basu taimakon gaggawa se faman shedding tears yake dan gaba d'aya ya kasa controlling hawayen.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(26)

_pray for me please ,..i'm sick🥺_

*kano state prison*

Gidan masu laifi, wasu mata ke ta aiki a saman duwatsu, yayin da wasu ke zaune cincirindo guda suna hira wacce kashi 30/100 batsa ce, can gefe guda kuma wasu ke yashe a qasa irin wayanda idan suka jigata suka yanke jiki su fad'i saboda tsananin gajiya.

Bulala ce riqe a hannun wata daga cikin masu basu tsaro tana shad'ad'a ma wasu daga cikin wanda ke yashe a qasa dan a ganinta qarya suke aikin ne basa so,

Gefe guda umma salamatu ke zaune duk ta fita a hayyacinta wannan jikin duk babu d'an hasken ma yanzu babu shi se baqi da kayan qasusuwa, hannayenta tallafe da fuskarta hawaye na zuba daga idanunta girgiza kai tayi game da ajiyar zuci a fili take fad'in "oh ni salamatu×2 mahaifina ya yafe ni cikin yaransa tun sa'ilin da nayi wa matarsa dukan tsiya yace na bata haquri naqiya, mahifiyata shekararta shabiyar a cikin qasa, danginta duk sunqi waiwayo ni tun bayan da naci musu mutunci a tunanina tunda mijina nada arziqi to zan iya taka wuyan kowa, mijina maji'bancin al'amurana son duniya irin tawa yasa shi datse igiyar auremu d'aya , yaro na Ameer na d'ora shi bisa muguwar hanyata gashi ya 'bige a firsun, a yanzu haka banson a duniyar da yarana suke ba, ko hajiya maryam data yi ikirarin ganin bayan su taci nasarar hakan? Ko kuwa?, kaico na ni salamatu son duniya ya kai ni tashar dana sani"
Chapter 20 · 0% Book details