← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 30

Sashe 14

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

‘Daga kai sukayi, tare da bin bayanshi da ido, suka sauke idonsu kan na juna tare da sakin murmushi me sauti

“Zaki iya tashi?” Munu ta tambaye ta

‘Daga kai Sam tayi a shagwa’be, hannu ta miqa mata ta kama, tana me fad’in “zo muje wurin tsohuwa da fillo”

***
Bismillah yay ya danna number cikin ikon Allah wayar se faman ringing take ba’a d’aga ba , qiris ya rage ta tsinke aka d’aga daga can bello yayi saurin qagawa a kunne

“Bro...A ya Allah bro ina kake? Ina ka ‘boye mana?”

“Shiii...first ina wani gari me nisa da bazan iya fad’a maka yanzu ba, all I want you to know is that I’m perfectly fine, inaso ka sani na barka a hannun ubangiji, I trust no one..”

Jijjiga kai bello ya yake hannunsa saman baki ya danne sautin kukan dake neman fitowa , yacigaba da saurarensa “..Bro B a situation d’in da muke yanzu inaso kad’a ka saki jiki da kowa ciki har da uncle saboda wasu dalilai dana barwa kaina sani, a qarshe ka turo min da isashshen kud’i yanzu ba anjima ba zan tafi can wani garin na shirya mu bar qasar nan”

“Okay bro I’ll do that right away, ya..su Sam?”

“They ar ok maza kayi abinda na saka, idan nayi settling zan kira ka”

Hasheem dake ta kallon bello ya fisge wayar “Man where d f*ck are you???” Ya fad’a da qarfi

Murmusawa yayi “somewhere..somewhere in the world, ka kula da Rayya,..”

“Tsaya tukunna I’ve received another latter from ‘hidden ‘“

“What!?”

“They said na fad’a maka no matter how far you are taking the treasure from them zasu nemo kuma they will hunt you down “

Lumshe ido yayi, “..Allah ya fi su doctor, se wata rana”

Bello ya amshi wayar cikin zubda hawaye yace “Ammi? Me kake so nace mata?”

“Kanemi abin fad’a mata, Ina sonka “ qitt ya katse wayar,

Bello ya kalli time kan ya dubi hasheem yace “bari naje mayi magana”

Kan hasheem ya iya furta wani abu tun ya ja mota, da qarfi yace “da me kake son naje gida?” Ya doki bango tun qarfi washhh ya hau yarfe hannu, tare da jan tsaki, ringing d’in wayar sa ne yaja hankalinsa ya duba Rayya ce,

“Babe come and pick me at sardauna crescent SS office” be jira ansar ta ba ya katse, aikuwa ko minti biyar batayi ba se gata sallama yayi wa bashari ya tafi

Hannu ta kawo zata ta’ba goshinsa cikin qosawa yace “babe sau nawa zan fad’a miki banason yawan had’a jikina da naki, Anya is kuwa kinje islamiyya?”

Burki taja wanda kad’an ya rage motar bayansu ta goge su yayi saurin kai hannu ya jasu shoulder d’in titi daddage wa tayi ta fashe da wani ubansun kuka har taso firgita shi, hannu yasa ya cakud’a sumar kanshi a zuci ya furta Allah na gode maka,

Facing d’inta yayi cikin karyayyiyar murya yace “babe I’m so sorry I don’t mean to hurt your feelings, soyayyar da nake miki ne yayi yawan da bazan iya jurar ganin kina yin wani abu ba batare da na tunatar miki ba, yayi shiru jin taqi kulasa sema turo baki da tayi

Yaci gaba is da cewa, “I know my words are harsh, am sorry my love Insha’Allah bazan kuma ba”

A shagwa’be tace “ya wuce amma meyasa kai kuma kake ta’ba wasu matan a hospital har da matan aure kuma”

Lips d’inshi na qasa ya shiga taunawa duk gudun kar dariyar da yake qunshewa ta fito a zuci cewa yake “yarinyar nan akwai daru”

Numfashi ya sauke a hankali yace “look at me Rayya”

Maqe kafad’a tayi “har yanzu kina fushi da ni ko babe “

Ta girgiza kai yace, “am a Doctor my love, a gynecologist wanda dole nayi huld’a da mace”

Cikin cool voice ya kuma cewa”but mind you duk huld’ar da zanyi dasu is different from yours, i love you from every drip of my blood”

Jikinta yayi la’asar dan ko d’ago kai ta kasa se fuskarta data mamaye da murmushi wanda ke fallasa fararan hakwaranta, side mirror ta kalla game da nausa motar kwalta, shima sanin cewar bazata kulashi ba yasa shi komawa da baya ya jingina da seat idanunsa stick on her face cike da tausayawa condition d’inta tare da matsananciyar soyayyar ta a gare shi badan komai ba yana mata kallon tsintar dami a akala a ganinsa tafi qarfin ajinsa me zata yi da likita kamarsa tafi kalar manya,

Lokacin data saukeshi a qofar gida ya leqo ta setin widow d’inta zan shigo anjima ki fad’awa mami zan ganta, drive safely ya ‘karashe da kallon ke kad’ai nake so, yau kam likita ya kashe bakin noisy Rayya dan har taje gida Gaza gane kanta tayi shin wani irin so take wa hasheem ne? Kai ta cusa cikin pillow tana imagining how her life will be without the hottest doctor, alarm na ya buga na lokacin shan maganinta ta tashi a hankali ta d’auki gorar ruwa dake saman bedside drawer tasha maganin kan ta miqe da niyyar zuwa wurin Mami dan sharia mata saqon likitan ta.

***
Banki ya wuce direct inda ya ci sa’a qiris lokacin tashin su yayi amma ganin babban customer ne yasa suka shiga bashi kyakkyawar kula ganin irin maqudan kud’ad’en da yake nema, ba a wani d’auki lokaci ba transfer tayi ya tura wa anwar text da

Done! Ina jiran call d’inka, Allah ya tsareka, ka kula da amana.

Murmushi yayi lokacin da saqon ya iske shi, saukowa yayi tare da dafo kafad’ar fillo

Yace “wani gari ne mafi kusa da nan?”

Ha’ba ya kama alamun tunani kan yace “yawwa garin bununu, daga nan kuma idan ka haura ruwa zaka ‘bulla minna”

“Kana nufin naija state”

“Aa garin nufawa de”

Numfashi ya fursar “zamu iya tafiya gobe da safe? Mu isa naija kan la’asar?”

“Aa fa, saboda se an kwan biyu cikin ruwa”

Ido ya fiddo waje “kwana biyu, babu wani alternative d’in, Ina nufin ba wata hanyar bayan wannan?”

“Eh to akwai mamman me ice matuqin babbar mota ne idan zaku iya binsa se ya kaiku amma zuwa dare yace ze kama hanyar minna”

Lips dinshi yayi nibbling kan yace “hakan za’ayi dan tafiyar tamu nada tsayi zo muje”

Zaune suke tsohuwa na gyaran zogale tana basu labarin ta da rayuwar su ta da, suka shigo “tsohuwa mu zamu wuce” yace yana me tsugunno a gabanta”

“Ku wuce? Ku wuce kuje Ina d’an samari?”

Caraf fillo ya amshe “tsohuwa munje gurin me ice ne yace ze sauke su a minna, tunda a hanya suke”

“Kai d’an samari babu inda zakuje da wannan yaron haka jikinshi ba qwari”

Kallon sashen da suke yayi yace “tsohuwa Insha’Allah ba abinda ze sameta inaso mu tafi ne gudun kada mu shafa muku kashin awaki dan na tabbata mutanen nan dake farautar mu baza su gaji da bibiyar mu ba har se sun cimma burin su, a nawa tunanin barin mu qasar nan ne kawai mafita hakan ze faru ne idan mun yi katin shiga wata qasa”

Had’e rai tayi, idonta kan ‘yammatan biyu da kwana biyu rak taji sun zame mata wani ‘bangare na jikinta

tace “Tunda haka ne shikenan, ta nuna masa yatsa kayi min alqawari duk randa kuka dawo zaku kawo min ziyara?”

Qasaitaccen murmushi ya saki “Insha’Allah tsohuwa ke da zaki min zaman d’aki ma”

“Ja’iri” ta furta cikin sadda kai ta shige d’aki, can ta fitoya riqe da qwarya cike da damammiyar fura ta ajiye gabansu sam “maza ku shanye kar ku tafi da yinwa”

Ta kalli anwar “zuwa qarfe nawa yace ku same shi?”

“Bayan sallar magriba”

“Madallah kafin nan kun huta ai”

HANYAR MINNA

Irin motar nan ce me rufaffen baya wacce ake safarar itatuwa daga wani gari zuwa wani gari kasancewar hayar motar su kayi ba komai a bayan se bencina biyu jingine da ko wani ‘bangaren motar Samira da Munu saman d’aya yayin da Anwar ke zaune saman wanda yake facing d’insu yana faman danna waya

Munu da ta jima da yin bacci jingine take da ledar kayansu, yayin da Sam ta nad’e qafafunta a qirji fuskarta na kallon waje iskar Allah na kad’ata tana me bin duwatsu da bishiyu da ido tana jinjina baiwa da iko na ubangiji, iska ta fursar a hankali ta juyo tana me facing Anwar, a nutse ta d’ago kwayar idonta ta sauke a kanshi cikin zuciyarta tana mamakin yadda baya gajiya da latsa waya, mayan waya! ta harari side din da yake

Murmushi ta saki a hankali ta lumshe ido se de tana bud’ewa de cikin hasken flash d’in waya

“Maimaita abinda kika fad’a...” ya furta in a harsh tune.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI 👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey)😊
WATTPAD @Deejaht ahmad

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers )

(21)

Jiki na rawa ta runtse ido har tana neman jirkitawa qasa,
"Kayi...kayi hakuri bazan kuma ba dan...Allah" ta qarashe cikin rawar murya

Shi dariya taso bashi ma se shegiyar tsokana ga tsoro daya yi mata katutu, yasa hannu yaja kunnenta "duk ranar da na kuma jin kin fad'i magana mara dad'i a kaina sena d'inke wannan qaramin bakin naki, silly girl" ya qarashe tare da d'allar lips d'in da hannu, har ya zauna be dena hararar ta ba, kula da hakan yasa ta qi bud'e idonta se ma jan jiki da tayi ta kwanta jikin munu har babban 'barawo yayi awon gaba da ita.

2:15am
Chapter 14 · 0% Book details