← Book details Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 30

Sashe 4

Dabaibayi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ha’a to gatanan ai se kaci gaba, doctor let’s go, meet me down there idan ka gama scanning d’in” ya furta cikin wata deep voice, suka fice

Wanda aka kira da Bro B ya maida hankalin sa kan wayarsa dake hahhaska Sam tamkar me yin video, daya gama ya mayar aljihu ya Mara musu baya.

Fitowa tayi daga inda take la’be tana tapping gefen bakinta da manuniya tana jinjina kai cike da tunani

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(6)
Tayi saurin juyawa ta koma office d’inta,

GET WELL HOSPITAL, asibiti ne da babban d’an kasuwa Alhaji Ammani ya ginawa babban d’ansa Hasheem bayan dawowar sa daga UK inda ya karanci gynecology wato likitan mata, asibitin be tsaya anan kad’ai ba akwai ‘kwararrun likitoci daga ‘bangarori da dama dake aiki cinkinsa tsaftataccen asibiti ne wanda ya gaji da had’uwa ta fannoni da dama kama ga ma’aikatan kiwon lafiyar, masu gyare gyare, wadatattun magunguna da dai sauran su

Saboda sau’kin da asibitin ke da shi da kuma kwararrun likitoci ga kyakkyawar kulawa da ake baiwa majinyata yasa mutane ke tururuwa cikinsa. Wannan kenan,

Alhaji ammani abokin Alhaji Ibrahim ne sosai hakan yasa alhaji kabiru ya bud’e family file a GET WELL gashi basu da nisa sosai.

***
Tun kafin motar takai ya tsayawa ya dira yayi cikin gida direct d’aki ya shiga yana tattara kayan sa ya na tura su cikin akwati ya d’auko passport d’insa ya zira cikin Jakar dake goye a bayansa wayarsa dake hannunsa ya sa gaban aljihu ya nufi hanyar fita

“Yayana ya haka?”

“Abba zan wuce airport ne “

Ya kalli agogon hannunsa “airport by this time?”

“Abba remain 2hrs fa”

Umma tace “To ai ka jira abokin tafiyar taka yazo ko?”

“Ya sameni a can” yayi gaba

Baki, hanci, ido ta saki tana binshi dasu,

A tsawace Abba yace “Yayana haka ya kamata kayi wa mahaifiyar ka magana?! Tamkar wata sa’arka!, ka dawo nan ko kuwa!”

Cak ya tsaya, har seda Abba ya kuma cewa “ba da kai nake bane?”

Dawowa yayi yana faman hura hanci, daf dasu ya tsaya, “idan har ka tafi ba tare da ka bawa mahaifiyar ka ha’kuri ba kai fa Allah!” Ya juya zuwa cikin gida.

***
Dr Hasheem ya kallesu murmushi bisa fuskar shi “gaskiya you are a lazy being Anwar”

Lumshe ido yayi kan ya bud’e su a kan hasheem “think whatever you want, bazan damu ba” ya cigaba da daddanna mini laptop d’in dake bisa stool,

Girgiza kai Bro B yayi sanin cewar d’an uwan nasa baze kuma furta wata kalmar ba, ya kalli Dr yace “Allah da ace bansan Bro A ba zan iya ko bin hanyar da yake ba talkless of na mishi magana, kaga fa da muka shiga d’akin can ko kusa da gadon qin zuwa yayi, kamar wanda yaga trash”

“Ai wallahi da zan samu uncle zance masa ne kai ya kamata kaje hutu shi ya zauna ya cigaba da aikin”

Wani kallon karka fasa ya watsawa hasheem, hasheem ya kwashe da dariya yana fad’in “Allah kuwa kai da qasar haihuwar ka amma kabi ka tsane ta,”

“Ka fad’awa wanda aka Haifa anan ba de Anwar ba!”

Bro B yace “naji d’in and I’m proud to be a Nigerian”

Harara daya watsa masa ne yasa shi saurin d’aga hannuwa “I’m sorry big Bro”

Wayar dr hasheem ce ta katse su inda tashiga qara alamun kira dannawa yayi muryar wata nurse ya doki kunnuwansu “Dr room no.18” katse wayar yayi suka mi’ke a tare banda Anwar dake cigaba da latse latsen system,

Hasheem ya kalli Bro B “ i think you should stay here gara naje naga halin da take ciki tukunna,”

Nodding yayi shi kuma ya fice xua d’akin.

Maida hankali yay kan d’an uwan nasa yace “Bro A do you think is a good idea ka tafi ka barni ni kad’ai anan?”

Murmusawa yayi “kar ka damu I’ll soon be back afterall kasan hankali na baze ta’ba kwanciya ba matsawar kana cikin mugayen mutanen nan, so chill dana kwana biyu zan juyo, kar ka manta you are my only family now”

Forming line yayi da baki, Bro A ya bashi assuring look tare da tapping kafad’ar shi , kiran dr hasheem ne ya shigo wayar Anwar, yace dasu suzo su same shi, tare suka jera zuwa d’akin

Bro B ne ya fara sallama ya shiga, tayi waal da ido
“Mu...Mu’allim Bello”

Murmushi ya sakar mata sam ya jikin ki?”

Gaza ansa shi tayi, tayi waal tana bin Bro A da ido ‘O’ shape tayi forming da bakinta, “Mu’allim is he your brother?”

“Yeah...big brother”

“Hello Mu’allim’s bro” ta d’aga mishi hannu.

Blank look ya bata without saying a word ya maida hankalinsa kan waya.

©️Kdeey😊

DABAIBAYI👄

©️Khadija Ahmad (Kdeey😊)

®️Haske writers association 💡
(Home of expert and perfect writers)

(7)
Sam da bata lura ba ta cigaba da cewa “doctor dama ka san mu’allim B?”

Kai ya d’aga, “he is nice right? U know what....”

“Kaii!!...hasheem r u sure wannan ce yarinyar da bata da lafiya?”

“Iya sani na idanunka garau suke so kar ka sa ni tantama” cewar hasheem a qafule dan zuwa yanzu ya fara jin haushin sabbin attitude d’in Anwar,

Bro B yace “kana tunanin set up ne ko ya?”

“Bro can’t you see tun shigowarmu take hayaniya ko mu bamu yi surutan da take yi ba, habaa make her stop or barshi am, bari na jira ku a office” fita yayi suka bishi da ido,

Qasa qasa ya kalleta ganin yacce tayi kicin kicin da fuska yasa shi matsawa kusa da gadon tallafe da kafad’ar hasheem yace “Sam doctor hasheem aboki na ne, nazo gurin sa ne naga file d’inki shine na nemi alfarmar ganinki dan na tabbatar ke d’in ce”

Murmusawa tayi had’e da lumshe idanu ta bud’esu saman nasa “nagode mu’allim, doctor hasheem is nice too just like you kasan me, he often give me some chocolates whenever muka zo nan and I share it with Ameer kamar yanda ka koya mana, kuma inace mishi thank you”

Fad’ad’a murmushinsa yayi “that’s very good Sam keep it up”

Gyaran murya hasheem yayi wanda yaja hankalin Bello ya girgiza masa kai, shi kuma ya amsa masa ta hanyar lumshe idanu,

Saman kujerar dake kallon gadonta ya zauna

“Sam how are you feeling now?”

“Fine mu’allim”

“Good, inaso ki nutsu ki zan miki wani tambaya but you have to promise me first zaki bani gamsashshiyar amsa”

Da sauri tayi nodding “Anything for you mu’allim,”

“Good, I want to know what exactly happens before you fainted?”

‘Dago kai tayi a firgice, hawaye suka hau shatatowa tamkar an bud’e fanfo,

“U’ve already promised and kinsan lefin wanda ya karya alqawari”

*
Karkad’e rigan ta hau yi tare da gyara zaman talhar dake nad’e a wuyanta tana ganin fitowar sa ta mara mishi baya,

Qare mishi kallo ta shiga yi daga baya, Ba’kin takalmin hamez sau ciki daya sakaye doguwar farar qafarsa ta fara kalla shigar baqaqen kayan sunyi mugun tafiya da imaninta baqin jeans da baqar riga me qaramin hannu shi ya kuma fito da haibarsa, kansa dake cike da baqar suma data dabaibaye fuskar had’e da saisayeyyen sajensa ya kuma dilmiyata a kogin begensa har tana jin inama ace yana mata kallo d’aya ya fad’a tarkon soyayyar ta kamar yanda ta kamu farat d’aya daga kallo d’aya.

Jin taku daf dashi har ana neman ta’ba sahun sa yasa shi saurin waiwayo wa qiris ya rage goshinsu ya bigi na juna, direct idonta ya fad’a cikin nasa wanda yayi sanadiyyar tsayawar numfashinta na wasu sakanni, ga qamshin sassanyan turaren Ricci wanda ya had’u da versace da sauransu suka bugota har cikin qoqon hancin ta lumshe ido tayi ta bud’e cikin nasa tare da tallafar fuska da hannunta na hagu.

***’Baby ni dai ni dai se na bika um um”, kuka take har da su bubbuga qafa tamkar d’iyar goye, “habibty rayya ki bar ni naje bazan jima ba zan dawo kinji”, “To promise me ba zaka kalli kowace kucakar mace ba,” “na miki alqawari” “ba wani goodbye kiss,” “Kai baby baka da dama, To matso na baka”’***

Ba zato tasa hannu ta tallafo fuskarshi tana qoqarin manna bakinta saman nasa qiris ya rage su manne ya sakar mata lafiyayyun mari saman luntsuma luntsuman kumatun ta, zube wa tayi a qasa ba tare da ya kalle ta ba ya fad’a office d’in hasheem tare da bugo ‘Kofa da ‘karfi.

*
“Ya..yace idan na fad’a ze yimin irin yanda sukayi ma mummy nah...”

Kallon juna sukayi da hasheem kan ya kalle ta “Sam kin manta yanda nayi punishing adnan da ya cilla wa sholey ball?”

‘Daga kai tayi yaci gaba, “I will deal with whom so ever he is kinji, feel free and tell me,” kula da yacce take a tsorace yasa shi cewa “trust me”

Hanci ta ja ta fara da cewa “ bansan wane ba kullum dare idan su umma da kowa sun kwanta se yazo yayi ta buga min qofa to shine yau ma yazo”

Kukan da yaci qarfin tane ya hanata wata sa magana,

“Sam me yake miki?”

“Yana ta’ba min jikina ku...kuma da zafi..”

“Innalillahi....”

Tashi yayi ya matso gabanta ya tsugunna idanunsa sun kad’a jazur muryarsa har bata fita sosai yace” Sam who is he?”

“I don’t know, he cover his face with a lion mask” ta kuma fashewa da kuka, saurin kiran munirat hasheem yayi yace ta zauna gurinta su kuma suka yo waje “mu’allim umma na..ka kaini gurin umma na”

Yana jinta ya share tare da fita daga d’akin da sauri. Jikin qofar ya jin gina qirjinsa na masa wani irin zafi...

Hasheem ya ri’ko hannunsa yana bashi baki suka nufi office tun daga nesa ya hango mutum a yashe can bakin ‘kofa da sauri suka qarasa ya sa hannu jikin wuyanta da hannunta jin pulse d’inta na bugawa ya danna emergency button dai dai lokacin nurses biyu suka iso suka cicci’beta aka d’orata bisa gadon suka nufi wani d’aki dan bata taimkon gaggawa.
Chapter 4 · 0% Book details