← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 32

Sashe 9

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama da suka fito tare da Baba daga ɗaki a burkice, suka yi burki a tsakar gida, su Suwaiba tuni sun yo waje daga ɗakin, cikin rige-rige. Nana kuwa na cikin ɗakin, tana ta uban kuka da gurnani, tana ihu iya ƙarfinta.

"Gaskiya na fara gajiya da wannan bala'in, kullum sai bawa ya sanya haƙarƙarinsa a ƙasa ya kwanta, ya fara bacci, sannan ta fara ihu, gaskiya na fara gajiya." Mama ta yi maganar a ƙufule.

Ɗakin Gaddafi ya nufa a fusace, Baba cewa yake "Gaddafi ka bi ta a hankali dan Allah, ka tofa mata abin da ya sauwwaƙa".

Yana shiga ya tarar da ita, tamkar ana girgizata, yatsun ƙafafuwanta duk sun ƙandare, kamar kuturwa.

Ƙafa ya saka yayi ball da ita, tamkar abar banza, yana zabga mata ashariya.

Sai dai ba ta san yana yi ba, iya ƙarfinta take ƙoƙarin karanta addu'a a cikin baccin, amma ta kasa.

Gaddafi ya danƙo ta, ya fito da ita tsakar gida, ya watsar da ita a wurin, ya ce "Ku wuce ku kwanta, idan ta gama iskancin ta tashi, ba wani aljanu iya shege ne kawai, kowa ya koma ɗaki ya yi kwanciyar sa".

Jikin Baba ya yi sanyi ganin halin da Nana ke ciki, ya ce "Ba iya shege bane, na kira ma an yi mata karatu fa, kalli yadda jikinta yake yi" yayi maganar yana tsugunawa a kanta, duk da wannan abun na Nana shi kansa ya ishe shi.
Wasu lokutan, sai yayi tunanin ko ƙarya take yi, amma idan ya yi la'akari da wasu abubuwan, sai ya ga normally mutum ba zai iya haka ba.

Sanyin Asuba, da zafin cizon cinnaku ne, ya sanya Nana farkawa, daga nannauyan baccin da take yi, da babu komai a cikinsa ban da azaba da wahala.
Ba ta damu da yadda ta ganta a tsakar gida ba, a tunaninta ita ta fito da kanta ta kwanta a gurin, dan yanzu ba ta mamakin yadda wasu abubuwan suke faruwa da ita.

Alwala tayi ta shiga É—akinsu, ta yi salla, sannan ta tashi su Suwaiba.

Cike da farin ciki ta tashi, dan yau É—in ta kama litinin ce, za a koma hutun makarantar boko.
Domin tana koyarwa a wata private school, da Nanny ta nema a makarantar, sai malamar da take koyar da 'yan kindergarten ta koma garinsu, aka bata riƙon ajin, kasancewar tana da kwalin sakandare, sai dai ƙoƙarinta da sabon da tayi da yaran, ya sanya suka ƙyale ta, suke ba ta dubu bakwai a wata. Tana matuƙar jin daɗin, yadda take shiga cikin ƙananan yaran, su yi ta tsalle-tsalle da wasa tana koyar da su. Sai dai ta tsananta addu'a, Allah ya rufa mata asiri, kar ciwonta ya tashi a makarantar, ta cutar da 'yan yaran.

Tana ta hanzari, ta gama abin da zata yi, ta shirya ta fita, Gaddafi ya shigo da buta a hannunsa, da alama sai a lokacin zai yi sallar asuba.

Yana ganin Nana ya tsaya ya ce "Yauwwa ke Nana, dan abu ta kaza kazanki, idan ki ka kuma tashi cikin dare, ki ka hana mutane bacci kina yi mana ihu, sai na yi miki shegen duka, dan wallahi sai na karya ki na gaya miki. Mahaukaciyar banza maƙaryaciya" Duk da ba wannan ne karon farko, da ake kallon ƙaryar ciwon take yi ba, amma tana mamakin yadda za ace, tana wulaƙanta kanta a gaban mutane, ta hanyar yin wasu abubuwa tamkar mahaukaciya.
Ba ta fatan ko maƙiyinta, Allah ya jarrabe shi da irin larurarta, ba dan haka ba da ta roƙi Allah ya jarrabi Gaddafi da jarrabawar da ya daɗe yana ƙaryata ta, a kai.

Ba ta ce masa komai ba, ta ci gaba da gudanar da aikinta, ba ta damu da rashin samun abin da za ta karya ba, duk ta ga an yi abin karin kumallon, ta kammala shirinta ta fice.

Nana akwai ƙoƙarin sammako, dan haka kusan hatta malaman, duk a makarantar suka tarar da ita, ta ji daɗin ganin yaran sosai, kamar yadda su ma suka ji daɗin ganinta, suke ta murna tamkar sun ga mahaifiyarsu.

*****

Ƙurii ta yi masa da idanu, yadda yake ta jujjuya kofin kokon hannunsa, ya kalli yarinyar da take kwance a kan katifa ya ce "Ita wannan ba ta tashi rashin lafiya ba, sai da aka koma makaranta?"

Babbar macen da take gefe tana karyawa ta ce "Dama rashin lafiya ana saka masa lokaci ne? Larura ce Allah ya kawo mata" ya jinjina kai ya ci gaba da cakalar abincin.

"Wai Auwwalu me yake damunka ne?"

Auwal ya numfasa ya ce "A ina?"

"Ka ƙi cin abinci, sai jujjuya kofin kawai ka ke yi" ya jinjina kai ya ce "Mama magana na ke son yi, amma ban san yaya za ki kalli abin ba"

Ta ajiye kofin hannunta, ta ce "Ko ma a yaya zan kalle shi, gaya mini ina sauraron ka"

Ya tattara hankalinsa, cikin nutsuwarsa da kamala ya ce "Mama dama akwai wata yarinya ne, da nake zuwa wurinta, to shi ne mahaifinta ya ce in tura magabatana ayi magana"

Tayi masa ƙuri da ido, sai da ya kammala, sannan ta ce "Me ka taka haka ne Auwwal, da zaka ɗaukko maganar aure? Fili ne fa kawai da kai a ƙasa, babu muhalli ba wata uwar da ka ke yi tun da ka kammala makaranta, bayan koyarwar nan sai 'yan kame-kame, abin da ka ke samu mu kanmu bai ishe mu ba, balle ka yayimo mana wata a bar maganar nan, kar ka sake tayar da ita yanzu maganar aure, ba nan ba ce"

Auwwal yayi shiru, ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i, ba ya son mutuncinsa ya zube a idon Nana, da mahaifinta. Har cikin ransa yake son ya taimaketa, mussaman da ya fuskanci ita sam ba ta da buri, kamar na sauran 'yan matan zamani.

****

A wannan karon ma, Alhaji zailani ne a zaune a gaban Malam, fuskarsa É—auke da damuwa ya ce "Wanda aka samu ka ce duk ba su yi ba, abin ba zai yiwu da su ba, na rasa abin yi gaba É—aya"

"Alhajin Allah, ai ci gaba da duddubawa za ayi, za a samu dai ba za a sare ba, sai kuma É—aya aikin da na baka, yaya ake ciki yau kwana ashirin da huÉ—u da fara shi ko?"

Alhaji zailani ya ce "Eh, na kusa kammala shi wannan, kuma na fara ganin alamun nasara"

Mutumin yayi dariya ya ce "In dai zaka yi biyayya, to za ka samu duniya yadda ka ke so, shi wanda ka ke maganar a kansa, shi ma ba a zaune yake bane ba, wani shu'umin aljani nake so ya yi mana aikin nan, zai iya dan yana da juriya da baƙin naci, amma fafur yaƙi"

Alhaji zailani ya tattare babbar rigarsa ya ce "Dan Allah ka tambaye shi, ko me yake so zan yi masa, ba ni da burin da ya wuce, na ga bayan fatuhu, gaba ɗaya shi ya hana arzikina haɓaka, ba a faɗar sunan kowa sai nasa"

"Ai duk wani tayi, da mu kan yi wa aljani, domin mu saka shi aiki yayi, na yi masa ya ce ba zai yi ba, akwai aikin da yake yi. Makirin aljani ne, idan na matsa masa zai iya ɓata mini wasu ayyukan, amma ka ci gaba da waɗanda na baka, sallar asuba da la'asar sai kwanakin da na ɗibar maka sun cika, sannan za ka ci gaba. Zan so ace kafin lokacin a samo yarinyar nan, aikin zai fi tafiya dai-dai "

"In sha Allah, zan ci gaba da ƙoƙarin hakan, za a samo yarinyar duk in da take"

"To shikkenan, kai nake sauraro" yayi maganar yana ci gaba da zazzana ƙasar gabansa.

*****

Shigar Nana gida babu daÉ—ewa, Baba ya ce mata, taje gidan da Jamila take zuwa, ta kira masa ita. Nana ta ji daÉ—in hakan, domin a zatonta Baba zai tsawatar wa Jamila ne, saboda yadda take zuwa ta shantake a gidan, ta wuni kamar a gidan ubanta.

A ƙalla Nana tayi sallama ya kai sau huɗu, sannan aka amsa aka ce ta shiga.

Jamila ta tarar a zaune a falo, tare da matar gidan maman khairat, sai kuma wata hamshaƙiyar mata a gefe, su na ta hira.
Rashin dacewar hakan Nana ta gani, bai kamata ace Jamila tana tsakiyar su, su na ta uwar hira har tana sallama ba sa jin ta ba.

Nana ta kalli maman khairat ta ce "Ina wuni?"

Cikin sakin fuska ta ce "Lafiya ƙalau Nana, ke ba kya zuwa gidana, Jamila ce kawai 'yar ɗakina" Nana tayi murmushi, ta kalli matar da tun da ta shigo, ta ƙure ta da ido. Haka kurum gaban Nana ya faɗi, amma ta dake ta gaishe ta.

Cikin ƙasaita ta amsa mata "Lafiya ƙalau 'yan mata ya ki ke?" Nana ba ta iya amsawa ba, jikinta ya hau rawa har bakinta ya nuna ta ce "Ja.jam..jamila Baba yana kiranki" tana faɗar haka kawai ta juya ta fice.

Maman khairat ta ce "Jamsy, meya samu yayarki ne?"

Cikin ko in kula ta ce "Wallahi ban sani ba, kin san tana da aljanu ba wuya ta burkice, kamar sun taɓa mata ƙwaƙwalwa ma"

Maman khairat ta ce "Subhnallah, ƙwaƙwalwa kuma?"

Jamila da ta tashi tana É—aukar mayafinta ta ce "Wallahi Anty, to sai ta tashi cikin dare tana kurma ihu, ranan fa kwananta biyu ba ta gida, babu ma wanda ya san in da take ba, kullum cikin ciwo take"

Matar da take gefe ta ce "Allah sarki, har ta bani tausayi, amma ta burge ni a nutse take masha Allah. Masu irin larurarta na buƙatar tausayawa da ja a jiki, kar ku ƙyamace ta, abin zai yi mata yawa"

Jamila ta ce "Ai ko ba ka ƙyamace ta, ka yi gudun ceton ranka, duk da ba ta duka, amma idan ta fara ihu cikin dare da gurnani, layin nan ba wanda zai rintsa.
Yanzu hatta ƙawayenta sun daina zuwa wurinta, saboda tsoron kar su kwasa" Jamila ta daɗe tana ba su labarin Nana, sannan ta tafi gida.
Chapter 9 · 0% Book details