← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 32

Sashe 15

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke Nana lafiya, ke ce ko aljanun naki ne? Wani mugun kallo ta yi wa Yaya Atine, ta ɗauki takalmanta a hannu ta riƙe.

Yaya Atine ta koma É—akin mai maganin, ta tarar da shi hanci na zubar da jini. Cikin tashin hankali ta ce "Malam lafiya kuwa?"

"Artabu muka yi da aljanun nata, ba aljanu ne a kanta ba, baƙaƙen iblisai ne, shaiɗan ne da zuriyar sa" ya yi maganar yana shafo jinin da yake fita daga hancinsa.

Sai hankalinta ya rabu biyu, tana ƙoƙarin ta tambaye shi, abin yi, kuma ga hankalinta a kan Nana. Ta koma in da ta bar Nana a tsaye, wanda suke zaune suka ce mata ai ta fita.

Ta fita da sauri, amma ko alamar Nana ba ta gani ba, ta bi hanya tana salati da fatan ba wani wurin ta yi ba.
Sai da ta ƙarasa titi, ta hangota zaune a gefen hanya, takalmanta a hanunta tana ta layi.

Su na yin ido huÉ—u, kafin Atine ta tsallaka, Nana ta tashi ta shige wani adaidaita sahu, ya ja sun tafi.

Salallami da salati, Atine ta hau yi, ta tari wani adaidaita sahun, ta tafi gidansu Nana.

Baba na ganinta a rikice ya ce "Atine yaya dai? Lafiya kuwa?"

"Ina fa lafiya Isa, mu na wurin mai magani, sun yi karambatta da aljanun nata, kawai ta fita ta haye adaidaita sahu, ai na za ta nan ta yo"

Gaddafi da yake wanki, ya ja tsaki ya ce "Wallahi lamarin yarinyar nan har da iskanci, kuma da gangan take ƙin yin auren nan, a kaita gidan mutumin nan da na gaya maka Baba, idan ba gaske ne, idan ma ƙarya take yi duk zai faɗa babu wani aljani da ya gagare shi"

"To yanzu a ina za a ganota?"

Baba ya ce "To wa ya sani, kwanaki fa kwananta biyu ba ta nan, sai daga baya suka zo da Ummi, wai kawai ganinta ta yi a gidanta, idan ma da gaske take, idan ma ƙarya suke yi oho musu. Ni wallahi na gaji da sabgar yarinyar nan shi yasa nake Alla-Alla a samu mai so ya aura na huta. Kuma ga wannan ƙanin mijin Ummi ta tsaya tana iyayi"

Babu tsammani, sai ga Nana ta shigo, Jamila ta riƙota tana ta tangaɗi, da takalmanta a hannu.

Gaba É—aya suka yi kan Jamila da tambaya "A ina ki ka ganta?"

"Gidan maman khairat zan je, kawai na hangota tana ta tangaÉ—i kamar ma ta kasa gane hanyar gida ne"

Mama da take ɗaki, tana jin su, sai yanzu ta yi but ta fito ta ce "Jamila, ban hana ki naniƙar yarinyar nan ba, sai kin kwashi masifa da bala'i"

Atine ta ce "To 'yar nema, da ki na jin duk abin da ake yi, ki ka ƙule a ɗaki?"

Mama ta ce "Ya shafe ni ne da zan fito, ba zaki cikata ba?"

"Mama faÉ—uwa za ta yi fa idan na cikata"

"Dan ubanki ki rabu da ita aka ce, duk ranar da ta ji miki rauni, ta sabauta ki ai kya shiga hankalinki" Gaddafi ya yi maganar cikin É—aga murya.

Duk da abin da mai maganin nan, ya shaƙa wa Nana, bai gama sakinta ba, amma tana jin duk abin da suke faɗa.
Ta zame hannunta daga jikin Jamila, ta dafa bango ta nufi É—akinsu.
Tana jin Baba yana tambayar ta, dan me ta baro wurin mai magani, tayi masa shiru dan ko buÉ—e baki, wahala yake yi mata balle doguwar magana.
Tana jin yadda Yaya Atine ta cafe, take yi masa bayanin, bataliyar aljanun da ke kan Nana, har da ƙara abin da ba a yi ba, kamar yadda mai maganin yayi mata bayani.

Tun tana jin su sama, har wani abu mai kama da bacci ya É—auketa.
Kamar a zahiri ta daina jin komai a duniyar da take ciki, ya zauna a gabanta yana kallonta, kafin ya ƙyaƙyace da dariya wani irin baƙin hayaƙi yana fita daga bakinsa.
Sam dariyar babu daÉ—in ji, ta saka hannu ta toshe kunnuwanta, amma ba ta fasa jin dariyar ba.

"Igiyar ƙaddara, ta ɗaure ki ta ko ina, kuma kina da damar kwanceta, amma azabar baƙin taurin kanki, ya hana ki saduda ki karɓi ƙaddararki"

Nana ta numfasa ta ce "Shirka ba ta cikin ƙaddarata, komai za ka yi mini, ba zan karɓi abin da ka ke buƙata na yi ba"
Ya É—ago dogwayen yatsunsa, ya kai fuskarta ya lakuto gumin da take ta yi, ya kalli gumin a hannunsa ya ce "Ki daina cika baki, lokaci zai fayyace komai"
Daga haka ya ɓacewa ganin Nana.

Bayan farkawar Nana, ta tashi da wata azababbiyar yunwa, ga sallolin da ake bin ta.
Ta tarar da Ummi ta zo, ta gaisheta amma ta amsa mata sama-sama. Ba a damu ba, ta yi sallolinta ta koma tsakar gida ta ce "Mama akwai abinci kuwa?"

"Babu" ta bata amsa kai tsaye.

Ummi ta ce "Mhmm Nana kenan, ai in dai irin wannan abubuwan ne, yanzu ki ka fara gani, tun da zaman gidan bai ishe ki ba, shi wancan na farkon Allah bai ƙaddara an yi da shi ba. Shi malamin naku an ce ya fito yaƙi, amma duk da larurarki, Saleh ya ce yana sonki amma sai wulaƙanci ki ke yi masa. Ya je ai ya gaya mini duk abin da ki ka yi masa"

Nana ta yi kunnen uwar shegu da Ummi, kamar ba da ita take ba.

"Mun yi magana da Baba, aure babu fashi, ya ce a gaya masa iyayensa su turo"

Nana ta kalli Ummi ta ce "Yanzu za ki so hafsa ta auri mutum irin Saleh? Kin san fa É—an shaye-shaye ne, kuma a Lagos É—in kin san ina ne wurin sana'arsa da suwa yake tare? Duk ba kwa duba mini wannan?"

"Nana ke ma fa kina da aibun nan, amma ya runtse ido ya ce ya ji ya gani, ita fa rayuwa yanzu idan ki ka samu mai sonki, duk wani tone-tone ba naki ba ne ba" ba ta sake kula Ummi ba, har ta gama abin da za ta yi ta bar gidan.

Tunanin yadda Allah ya ƙwaceta daga hannun mai maganin ɗazu take yi, da tuni ya cuceta ya cuci rayuwarta, ita kanta ta san Allah ne kawai ya ƙwaceta, amma ya riga ya bugar da ita.
'wataƙila ga in da addu'oinki suke yi miki amfani, amma ki ke garaje da ɓacin rai' wata zuciyar ta tunatar da ita, a take ta yi ta istigfari.

Sosai Baba ya ɗauki maganar Saleh da muhimmanci, Nana kuma ta na ta kai kukanta ga Allah, duk da neman lafiya da take roƙa ya rinjayi duk sauran adduo'in da take yi.

Gashi duk da shirun da take yi wa Saleh idan ya zo, ba ya zuciya sai ya kuma dawowa, dan babban abin da yake saka shi zuwa ba yau ba gobe, bai wuce tozali da ƙirar jikin Nana ba, da yake jin kamar zai ɗimauce, idan bai kai hannunsa jikinta ba.
Ta kan ƙare masa kallo, tana mamakin yadda Baba ya rintse ido, daga ganin aibun Saleh, kama daga kan askin banzar da yake kansa, zuwa suturar da yake sakawa da sunan gayu. Kodayake dama gayu idan ya haɗu da jahilci hauka ne tuburan, duk soki burutsun da zai yi mata babu maganar Allah a ciki sai shirmensa.

Gefe guda ga kewar malam Auwal da ta dameta, tabbas ba dan mutunci da kamewarta, na ɗiya mace ba da babu abin da zai hanata zuwa gidansu ta tuntuɓi ko lafiyarsa ƙalau. Sai dai duk da haka sai da ta tambayi abokinsa malam Nura, ya tabbatar mata da lafiyarsa ƙalau ayyuka ne su ka yi masa yawa kawai.

Kimanin makwanni biyu kenan, ba ta ga malam Auwal ba, zuciyarta na raya mata, karɓar lambarsa a wurin malam Nura, ta ari waya ta kira shi, amma ta kasa.
Kwatsam su na cikin karatu a aji, ta jiyo muryarsa a waje. Ta kasa riƙe kanta, ta tashi ta fita.

Kafin ta isa, har ya shiga cikin ofishinsa, yana cikin tattara litattafansa, kawai ya waiwayo ya ga Nana.

"Yaya Auwal meyasa ka ke guduna? Ina ta son mu haÉ—u na yi maka bayani, amma ka daina zuwa ma gaba É—aya"

"Babu malami a ajinku ne?"

"Eh, tilawa muke yi"

"Ki koma aji" ya bata amsa ba tare da ya kalle ta ba.

Ta marairaice ta ce "Amma Yaya Auwal, magana nake son mu yi, dan Allah ka fahimce ni ba abin da ka gani, ba abin da ka ke tunani ba ne...

"Ki tafi aji na ce Nana, ba sai kin yi mini bayanin komai ba" yayi maganar cikin tsawa.

Tsayawa ta yi tana kallonsa, bayan tayi nasara sun haÉ—a ido.

A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta tafi ba kuma ba ta ce komai ba, sai dai idonta ya cika da hawaye.

Sai ya tausasa murya ya ce "Ki je aji Nana, ba na son gardama"

Ta girgiza kai ta ce "Koma me ka ke ɓoye mini ka gaya mini. Kai malamina ne, kuma abin koyi na, ka karantar da ni nagartattun halayen fiyayyen halitta Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam. Wanda ya haɗa da gaskiya, da kuma haƙuri. Ka gaya mini ko ma mene ne a ranka dan Allah"

Jiki a sanyaye ya ɗan sunkuyar da kansa, sannan ya kalle ta ya ce "Nana kin san komai nufi ne na Allah, maganar aure tsakanina da ke, ba zai yiwu ba yanzu haka Qatar zan tafi da wani ɗan ƙanƙanin lokaci"

Murmushi ta yi, duk da hawayen da ya cika mata ido, ta ce "Ko kai fa, ka ga yanzu da ka gaya mini gaskiya zan fi samun nutsuwa sosai da sosai. Ina yi maka fatan alkhairi amma dan Allah ka ci gaba da yi mini addu'a, na san larurata ce ta saka ka fasa aurena, ka yi mini addu'a Allah ya bani wanda zai iya aurena da larurata a haka"

"A'a Nana, idan baki manta ba, tausayinki da halin da ki ke ciki, ya sanya na ce zan aure ki, ban ƙi auren ki saboda larurar ki ba"
Chapter 15 · 0% Book details