← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 32

Sashe 14

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da ta waiwaya, mutumin nan ne da suka haÉ—u a ofishin director, ta sauke muhsin, ya nufi wurin babansa da gudu, ita kuma ta É—aukko masa jakarsa da lunch box É—in sa.
Har ƙasa ta risuna ta gaida shi, ya amsa cikin sakin fuska ya ce "Ya yaran naki, ya ƙoƙari?"

Ta amsa da "Alhamdilillah"

"Madalla mu na ta goɗiya, mun yaba da ƙoƙarin da ki ke yi wa yara, Allah ya saka da alkhairi"

"Amin na gode sosai"

Har zai juya su tafi ya ce "Amma yaran naki, sun tashi gaba É—aya ko?"

Ta ce "Eh, sun tafi dama Muhsin ne ya rage, zan tafi nima"

"To mu je, sai mu sauke ki a hanya mana"

Nana ta É—an yi turus ta ce "Bakomai na gode, ai babu nisa sosai"

"A'a bakomai, ai ni na ce muje sai mu ajiye ki a hanya" sai ta ji mutumin yayi mata kwarjini, ta ci gaba da jayayya da shi, amma har cikin zuciyarta ba ta so hakan ba sam.

Su na tafe a hanya, yana yi mata tambayoyi, kan matakin karatunta, da makamantansu. Ta din ga bashi amsa sama-sama a tsorace, dan haka kurum ta ji ya takura mata da yawa.

Sai dai ya din ga yaba mata, da ƙoƙarin da take yi da yara. A bakin titi ta ce za ta sauka, ya ɗauki kuɗi dubu biyar ya ba ta, ta ce masa ba zata karɓa ya ce ba zata sauka daga motar ba, sai da ta karɓa, sannan ya buɗe, ta yi masa godiya ta nufi hanyar gida.

A ƙofar gida ta hangi Baba, yana zaune a ƙasan bishiya, sai hamma yake yi, idanunsa jawur.
Ta nufi inda yake, ta je ta durƙusa tana gaishe shi. Da ƙyar ya amsa mata yana kawar da kai gefe. Ta ɗaukko dubu uku a kuɗin nan ta miƙa masa ta ce "Baba ga wannan, yaran da nake kula da su ne, baban wani ya bani" sai ya waiwayo da sauri ya saka hannu ya karɓa.

"Masha Allah, ai yakamata dai dama iyayen yaran nan, su din ga yi miki ihsani, tun da dai yaran nan na su da ki ke yi musu wahala, ba wani biyanki ake yi da kyau ba. Ko suturar jikinki suka kalla ai sun san mabuƙaciya ce ke, ba sai an ce su baki ba"

Nana ta basar da zancen, dan ba ta son ire-iren waÉ—annan zantukan na Baba, masu cike da son zuciya ta ce "Bari na shiga na shirya, na tafi Islamiyya"

"Zauna nan mu yi magana kafin ki shiga gidan" Nana ta zauna sosai tana sauraren Baba.

"Nana duk abin da ki ka ga ina yi, ƙoƙari nake yi a kanki. Ki daure ranar talata ki je gidan yaya Atinen, a jarraba mai maganin wurinta ko za a dace. Idan bai yi ba sai fa mun dangana da mai maganin da Gaddafi ya bani labari, idan ba haka ba babu lallai ki iya zaman aure ki yi haƙuri  shi wancan malamin naku dama ba sonki yake ba, tun da ya gudu bai turo iyayensa ba. Tun daga wannan ba sai ki haƙura ayi da shi ba, nima a rage mini ɗawainiya ba. Yanzu ba a auren soyayya, ko wani zurfafa bincike duk bayi ake ba. Ki tashi ki shiga kar ki makara"
Ba ta ce uffan ba, ta tashi jikinta a sanyaye ta shiga gida, gaba ɗaya kalaman Baba babu na ƙwarara gwiwa sai na kashe jiki da cire wa mutum tsammani.

*****

Gaba É—aya Auwal ya daina shiga makaranta, wanda hakan ya É—agawa Nana hankali, ta na ta son su haÉ—u da shi, ta yi masa bayanin abin da ya gani ranar da ya je gidansu, amma ba ta samu ganinsa ba.
Ita ba waya ba balle ta kira shi, abin duniya duk ya dameta. Ranar asabar da sassafe, Baba da kansa ya tashi Nana, ya sanyata shiryawa, ta tafi gidan yaya Atine.

Babu yadda ta iya Baba, zuciyarta ta din ga raya mata, kar ta je, amma ta tabattar idan ba ta je ba, fushi zai yi da ita.

Tun da Allah ya sa ta je gidan, bayan sun gaisa yaya Atine take masifa, wai ta ƙi tsayawa a nema mata magani ta wahalar mata da ɗan uwa. Nana dai ba ta ce uffan ba, Yaya atine ta yi ta faɗanta.

Ta shirya ta saka Nana a gaba, suka tafi wurin mai magani.

Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU

Ayshercool

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)

P8

Kallon farko da Nana ta yi wa mai maganin, takaici ya kama ta duƙun-duƙun da shi kamar wakilin sarkin dauɗa. Yana zaune a cikin wasu tarin shirgi da ta rasa ko na uban mene ne.
Ɗakin sai azabar ƙauri yake yi, da tsamin wasu abubuwa da ta kasa tantance ko na mene ne.
Jikin bangon ɗakin, an zana wasu irin hatimai, kuma an saƙale ƙahunhuna da layoyi. A take zuciyar Nana ta bata wannan mutumin boka ne, ba malami ba, ko kuma malun malun.

Ya ƙare wa Nana kallo, ta kawar da kai ta ƙi kallonsa, Yaya Atine ta gyara zama za ta fara yi masa bayani, ya dakatar da ita, ya ce "Ɗan saurara tukuna Hajiya. Ba ki ga ta kasa haɗa idanu da ni ba? Ai sun zo shegun sun ƙaraso, tare ku ka shigo da su ai, ku na tafe su na biye da ita runduna guda, manya da yara tsofaffi da matasa, yanzu haka kusa da ke ma duk su ne a zazzaune makaran nata, sun cika gurin nan"
Yaya Atine ta zabura ta tattare ƙafafuwanta ta ce "Innalillahi. A nan ɗin malam?"

"Eh fa, yi a hankali kar ki hau kan wani"

Nana kuwa waiwaya ta yi, domin ƙara tabattar da a kan wa yake maganar ne?.

Ya gyara zama, ya juya ya ɗaukko wani ruwa, a wata tasa ruwan duk yayi gansa kuka, baƙi ƙirin da shi, ya ɗebo a hannunsa ya watsowa Nana. Take Nana ta ɗan ja da baya, saboda idan wannan ruwan dauɗar ya zuba a hijjabinta jirwaye zai yi.

Ya ce "Kin gani ko, ga su nan za su yi magana, sun ji ruwan azaba, wane su dan uban su. Waye ya zo kanta za ka yi magana ko kuwa?"

Nana ta É—ago kai baki buÉ—e tana kallon ikon Allah, tana tsoron ta yi wani abin, ya ce Aljanun ne suka zo, kar ta je ya zane ta. Sai dai ta ga idan ba ta yi da gaske ba, sai ya yi mata wanka da ruwan dattin nan, aikuwa ta tashi tsaye ta ja da baya.
Yaya Atine ta miƙe da sauri, ta yi baya cike da tsoro da fargaba.

"Ba za ku yi magana ba?" Yayi maganar yana zare mata ido, tare da miƙewa.

Nana ta ce "Wai suwaye za su yi maganar ni ce fa"

Ya ce "Da alama wannan makaran nata, su na da azabar taurin kai, sai an yi aiki tuƙuru a kansu. Yanzu zan yi mata wani ƙaramin aiki, somin taɓi idan kuma da kuɗi a hannunki ki bayar da dubu goma sha biyar, za a sayo turarukan da za ayi mata aikin da su.
Ranar Litinin kafin hudowar alfijir, ake yin aikin, za ki kawo mana namijin goro guda bakwai, da zuma farar saƙa, kuma da wuya idan ba sai an yi yanka ba, kin ga sun ƙi magana". Yayi maganar yana ƙarasa sheƙa wa Nana ruwan hannunsa, hakan ya sanya hijjabin Nana, kwanciya a jikinta ya fito da surar da Allah yayi mata.
Takaici ya isheta, tun da suka zo, mutumin nan bai ambaci Allah ba, ko ayar Alqur'ani sai shirme da soki burutsu. Warin ruwan da ya zuba mata duk ya cika mata hanci. Kawai ta nufi hanyar fita ta bar ɗakin. Yayi wuf ya riƙo hijjabinta.

A fusace Nana ta juyo ta ce "Meye haka, ka sakar mini hijjabina ba na son haka"

Mutumin ya dubi Yaya Atine da ke zare ido ya ce "Hajiya za su yi magana yanzu, ba ita ba ce ba" Nana ta saka ƙarfinta za ta fizge hijjabinta, ya saka ƙarfinsa ya hankaɗata take ta faɗa kan shirgin da ke cikin ɗakin, wani azababben wari, kamar na ruɓewar wani abu, ya daki hancin Nana, ga ƙume ƙeya da ta yi, wanda gudun kar ta yi ihu, ya sake fakewa da haka ya yi mata wani abun, ya tilasta ta yin shiru. Tana ƙoƙarin ɗagowa, ya shaƙa mata wani abu a hancinta, ta kawar da kanta ba ta sheƙa da yawa ba, amma ta ji wata irin gigitacciyar azaba ta ratsa hancinta zuwa kanta. Ba ta san lokacin da ta kurma ihu ba, jin azabar ta danne mata hanyar fitar numfashi.

Ya kalli Yaya Atine ya ce "Hajiya jeki waje zan yi aikina"

Yaya Atine ta ce "Ka na ganin ba wani abu na je?"

"Eh mana, idan ma kin tsaya babu abin da za ki iya yi, idan ba haka ba idan suka zo fita su shige jikinki" ai cikin azama ta bar ɗakin. Sai da ya leƙa ya tabattar ta bar wurin, sannan ya dawo kan Nana, da take ta layi a ƙasa.

Kan Nana ya yi, yana ƙoƙarin kai hannayensa ƙirjinta duk biyun, ta yinƙura ta juya tana takaicin yadda Yaya Atine ta iya tafiya ta bar ta, daga ita sai wannan zindiƙin mara tsoron Allah.

Ƙoƙarin juyo da ita yayi, yana laluben yadda zai saka hannu a cikin jikinta, tayi wani kyakyawan yinƙuri, ta fizgo wani ƙaho da ke rataye daf da ita, ta raɗa masa a daidai tsakiyar kansa.

Afujajan ya tashi tsaye, yana zazzaro ido, ya gigice saboda yadda ta yi masa dukan a bazata, dan a zatonsa hankalinta ya gushe.

Ya kasa tsayuwa, ya nemi wuri ya zauna, saboda azabar raÉ—aÉ—i.

Ta tashi da ƙyar, tana tangaɗi, ya yinƙura ya yi kanta domin hanata fita, kar ta tona masa asiri. Amma ta sake ɗaukan wata ƙwarya wadda take cike da ruwa, yayi baƙi ƙirin saboda tarkacen da yake ciki, ta sheƙa masa a fuska, sannan ta tattara ɗan kuzarin jikinta, ta yi masa ɓarin makauniya da ƙwaryar a fuska sai da ƙwaryar ta ragargaje.

Ganin Nana ta fito tana tangaÉ—i, ya sanya Yaya Atine tashi ta nufe ta, mutanen wurin na ta yi mata sannu.
Chapter 14 · 0% Book details