Sashe 7
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana ji tana gani, malam ya saka almajiransa, suka rirriƙe ta, suna yi mata karatu, malam yana shafa mata man gelo a fuska, yana zuba mata wani ruwa a jikinta, ga kuma bulalar da yake ta zuba mata tana ihu. Babban abin da ya ɗaga mata hankali, bai wuce yadda a wayance ɗaya daga cikin yaran malam, yake goga mata jikinsa yana naniƙar ta ba, kuma yana sane.
Tun tana kuka muryar ta na fita, sai da ta yi laƙwas ta kasa motsi gaba ɗaya, kukan ma ta kasa sai ajiyar zuciya da take saukewa, ji take da da makami a kusa da ita, sai ta illata wanda yayi mata rashin ɗa'ar nan, sai ta daina jin zafin bulalar, sai na baƙin cikin tozartar da ta yi.
A banza wanda ba muharramanta ba sun daddaneta, babu ladduban ruƙiyya babu komai.
Malam ÆŠayyabu ya ce "Ina ga aljanin ya tafi, duk na ga gardamamme ne, bai yi magana ba, amma ya kau. Ku tashi muje zan bawa babanta magungunan da zata din ga yi"
Nana tana daga kwance tana ji suka fita, hannayenta da suka banƙare suka riƙe kamar ba a jikinta suke ba, ga fatarta kamar an sakata a cikin wuta saboda raɗaɗi.
Ta jima a kwance tana numfarfashi, daga baya ta ja jikinta a hankali, ta fita tsakar gida ta yi alwala, ta idar kenan Baba ya shigo da ƙullin baƙar leda a hannunsa, ya ce "Kin farfaɗo kenan?" Ta ɗaga kai ta kalli Baba, ta mayar da kanta ta sunkuyar, wani mugun haushin Baban ya kamata, ba ta ce masa uffan ba, ta shiga ɗakinsu.
Tana kallon suwaiba tana raɓe raɓe, za ta shigo ɗakin, ba ta kula ta ba ta tayar da salla. Da ƙyar ta yi sallar, ga yunwa ga zafin duka.
Ta zame rigar jikinta, tana haska jikin nata da mudubi, wani wurin har jini ne ya fita, ita kanta ta san ba ƙaramin dakuwa ta yi ba, a take wasu hawayen suka ci gaba da zubo mata. Hankalinta ya kai kan raunin da yake wuyanta, ta shafa wurin ta yi shiru tana tuna mafarkinta da tayi jiya.
Jamila ta shigo É—akin da sallama, Nana ta amsa a hankali. Cikin tausayawa ta ce "Sannu Nana, subhnallah haka duk suka ji miki ciwo?" Tayi maganar cikin tausayawa, ganin yadda fatarta tayi ruÉ—u-ruÉ—u.
Ga buredi da ƙosai ki samu ki karya. Sai da ta ɗan yi jimm, sannan ta karɓa ta ce "Na gode sosai"
Tuni masu aiki suka fara aikin gyaran gidan su Nana.
Jamila na shirin fita, mama ta tsare ta a É—aki ta ce "Ke magana nake son mu yi da ke"
"To mama, ina jinki"
"Gidan maman khairat É—in za ki tafi?"
Jamila ta jinjina kai ta ce "Eh mana, idan ban je ba me zamu samu mu ci?"
Mama ta gyara zamanta ta ce "Zuwa la'asar ki dawo, kin san ba a bori da sanyin jiki, duk da tana yi miki alheri, matar nan tana ƙaunar ki, amma dole mu bi ta wurin malamai, a ƙara yi mana aiki a kanta, yadda zata ƙara sakar mana hannu, ai ni tarewar matar nan alkhairi ne a gare mu" Jamila ta ce "To mama, duk yadda ki ka ce, amma duk da haka ai tana yi mini ƙoƙari sosai fa, kalli abubuwan da take yi mana"
"Ke dalla can ba a zama haka, idan ta kama mijinta ma, ba sai a shiga a fita, ayi wadda za ayi ba"
Jamila ta ce "Ahh haba mama, banda auren mijinta, butulci kenan ai"
"To na ji, ita ɗin dai a ƙara mallake mana ita, ta ƙara sakar mana hannu, daga ita har mijin nata"
Jamila ta gyara zaman gyalenta, ta ce "Shikenan, sai na dawo"
"To Allah ya tsare yarinyar kirki, duk abin da ki ka ci dai ki tuna da ni, Allah ya yi albarka"
"Amin" Jamila ta amsa ta nufi hanyar ficewa.
Haka Suwaiba ma ta shirya, tana ta baza ƙamshi, cikin matsatsun kaya ta fice.
Nana ta ɗan girgiza kai, su waɗanda suke shigar banza, su wuni jin kaɗe-kaɗe, ba Qur'ani ba azkar, aljanu ba su bi su sun takura musu ba, sai ita da take ƙoƙarin killace jikinta da ƙoƙarin yin addu'oi. Saurin katse tunanin ta yi, ta fara istigfari.
Ta lallaɓa jikinta ta fita tsakar gida, ta fara kaye-kaye, ta tattara kwanukan wanke-wanke, ta koma gefe dan ta wanke. Dan bayan da larurar nan ta waiwayota a 'yan kwanakin nan, su na tsoron taɓa ta, da akan wanke-wanke sai a ci mata mutunci, har ma a haɗata da Baba ya yi mata nasa cin zarafin.
Kafin yamma tuni an gama da gyaran katangar gidan su Nana, har ma an ci ƙarfin aikin, gyaran masan gidan da na rijiya, mama sai alfahari take tana hura hancin albarkacin 'yarta aka ci, aka yi wannan gyaran, dan da ta malalacin mai gidan ne, sai dai a zauna a haka.
*****
"Wata guda kenan, haryanzu shiru babu wani labari, an yi addu'ar, an yi duk abin da yakamata, amma haryanzu babu wani ƙwaƙwƙwaran labari a kan ina ya tafi. Kuma babu wata shaida ko alama, ko saƙo da zai bayar da damar gano in da yake. Amma kai a naka binciken me ka gano?"
Mutumin ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ni abin da na gani, ya yi nesa da gida sosai ma, yana kudu da nahiyar nan ma"
Matar ta dubi mutumin cikin rashin fahimta ta ce "Me ka ke nufi?"
"Ina nufin, koma a ina yake ya riga yayi nesa da gida sosai da sosai"
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, yanzu mene ne abin yi? Ina mamakin dalilin da zai sanya, ya yi wannan shirmen, kawai ya tafi ya bar gida ba sanarwa ba komai?"
Mutumin ya É—an É—age kafaÉ—a ya ce "Allah masani"
"To kai yanzu mene ne abin yi, dole dole ana buƙatar sa a gida, a wannan ƙadamin da ake ciki, banda tsabar wulaƙanci da baƙin ciki, kawai sai ya kama ya bar gida? Kawai ayi masa kiranye ko gidan uban wa ya je ya dawo"
Da sauri ya ce "A'a, na so na bayar da wannan shawarar, amma na duba na ga akwai matsala idan aka yi masa kiranye za a samu matsala, idan bai dawo ba zai yi hauka tuburan, abin da yafi dai ayi tunanin wata mafitar"
Tayi shiru tana tunani, daga bisani ta numfasa ta ce "Shikenan babu laifi, zaka iya tafiya " ya jinjina kai ya tashi ya fice.
*****
Tun da Baba ya yarfa Nana, a wurin malam Auwal, take matuƙar jin nauyinsa, shi kuwa har cikin zuciyarsa ya ji ya aminta da abin da baba ya faɗa.
Yana zaune a ofishin malamai, yana marking wani assignment da ya bayar, ya hango Nana ta shigo makaranta a makare, ya zuba ido ya ga wani mataki malam Nura zai É—auka.
Ya tattara hankalinsa a kansu, baya son a daki Nana, duk da ya san duk makarantar babu wanda bai san matsalarta ba. Tayi wiƙi wiƙi da ido, tana tsoron kar malam Nura ya daketa.
Cikin ikon Allah, sai bai daketa ba, ya sanya ta É—ebo ruwa a rijiya ta zuzzuba a butocin alwala.
Yayi ajiyar zuciya, ya ci gaba da makin É—in sa, kawai zuciyarsa ta raya masa, idan kuma wani abu ya sameta a gaban rijiyar fa? Ba shiri ya tashi da hanzari ya tafi.
Tana gaban rijiyar tana jan ruwa, yayi gyaran murya.
Tana waiwayawa, ta ganshi, risunawa tayi tana gaishe shi, bai amsa ba, ya ƙarasa ya ce "Bani gugan ki tafi aji" ta zaro ido ta ce "Ya sayyadi Nura ne ya....
"Ni kuma na ce ki kawo ki taf...
A É—an raunane ta ce "Ya sa...
Auwal ya ce "Za ki bani, ko sai na jefa ki a rijiyar" murmushi ta yi, tana kallon rijiyar ta ce "To bari na janyo gugan" tayo maganar tana janyo gugan daga rijiya.
Ta juye ruwan, ta ajiye zata tafi ya ce "Nana" ta tsaya cak ta ce "Na'am" ya ce "Ya jikinki kuwa?"
Take annurin fuskarta ya ɗauke, ta ce "Na ji sauƙi"
Auwal ya ce "To Alhamdilillah, Allah ya É—orar da lafiya, ki ci gaba da addu'a da azkar É—inki" ta jinjina masa kai ta ce "In sha Allah"
"Amm goge wannan abin na bakinki, sai ki tafi aji" kallonsa tayi, man leɓe ne kawai a bakinta, ba jambaki ba, shi aka hana sakawa.
Ba tayi musu ba, ta goge. "Maza jeki, anjima zan zo gida in sha Allah" ji ta yi gabanta ya faɗi, amma ta kasa magana, ta ja ƙafafuwanta a hankali ta tafi aji.
Auwal su na gaban su Nana sosai, lokacin da take yarinya sosai suka yi sauka, bayan sun yi sauka ya ci gaba da koyarwa, ko da ya tafi karatu ya dawo, ya É—ora da koyarwar a islamiyyar.
Tunani take yi, kar dai malam Auwal, da gaske ya yadda da abin da Baba ya gaya masa.
Ganin yau tana cikin hayyacinta, ya sanya 'yan ajinsu, suka sake da ita, tare suka zauna da ƙawarta Amira, a wuri ɗaya suka ɗauki karatu.
Amira ta so tambayar Nana, ina ta tafi aka yi ta nemanta, amma ta fasa, saboda kar ta tsokanota ta burkice.
Duk damuwar da Nana take ciki, da zarar ta fito makaranta, aka yi karatu, ta haɗu da ƙawayenta, sai damuwar ta ragu, sai ta kamo hanyar gida tukuna. Sai dai tana jin babu daɗi yadda wasu lokutan ƙawayen nata, suke gudunta, saboda larurarta.
*****
"Yanzu kai Habu yaya zamu yi da wannan mutumin, kana ganin mutum kamar katako, baya gane komai, ni anya ma ba hauka ne yake damunsa ba?"
Habu ya ce "Ashsha! Na gaya maka É—an uwana ne, ba shi da cikakkiyar lafiya ne, magani nake nema masa, da ya warke shikenan"
"Ikon Allah, Allah ya bashi lafiya, ga mutum har mutum a haka, amma ba ya gane komai, Allah ya bashi lafiya"
Habu ya amsa da Amin, tare da kallon wurin da wanda suke maganar a kansa yake.
Yana ta wasa da zobunan hannunsa, manya manyan azurfa, da kuma tagulla.