Sashe 6
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sosai Nana take kuka, tamkar ranta zai fita, ta rasa dalilin da ya sanya abin da ya haɗa su, ya shafe ta yake aibata mata uwa a gaban kowa, yana cin mutuncin ta, ita fa uwa uwa ce, mece ce ribarsa idan ya raba alaƙarta da mahaifiyar ta?. Wucewa ɗaki ta yi tana ci gaba da kuka, masifa goma da ashirin, ga yunwa ga yarfata da Baba yayi a gaban ya sayyadi, ga kuma abin da ya fi ci mata tuwo a ƙwarya, cin zarafin mahaifiyar ta.
Ko hijjabin jikinta ba ta cire ba, kawai ta kwanta tana kuka, ji take tamkar ta kurma ihu ko za ta ji sanyi a ranta, shiru ta yi hawaye na zuba daga idanunta, tana sheshsheƙar kuka, ga kanta ya fara sara mata da wani irin matsanancin ciwo.
Ba ta san iya adadin lokacin da ta shafe a haka ba, ta ji Jamila ta taɓa ta, ta ɗago ta kalli Jamila.
"Ungo rabu da shi, kirata ku yi magana"
Jiki a sanyaye ta girgiza wa Jamila kai, alamar ba zata karɓa ba.
Jamila ta yi ƙasa da murya ta ce "Ya tafi ya kwanta fa, ki kira ta bari na kira miki ita, ai ban san ki na da lambarta ba, ai da kin din ga karɓa ki na kiranta" tayi maganar tana danna lambar, sai dai layin yaƙi shiga.
"Ba komai Jamila na gode sosai kar ki damu" ta koma ta kwanta.
Ƙoƙarin yin tunani take yi, amma kanta ya ci gaba da sara mata, ba ta san ya aka yi ba, bacci mai nauyin gaske ya ɗauke ta ba.
Tana tsaye a wani ɗakin library, amma yanayin wurin kamar a wani zamani ne na daban, litattafan wurin duk sun yi ƙura, wasu litattafan duk yana ta yane su, ga ƙauri wurin yake yi, da ta kasa gane wani irin ƙauri ne. Tari ta fara yi saboda ƙaurin ya fara damunta, babu tsammani ta ɗaga kai ta ga wani zanƙalelen mutum, da tsawonsa ya kusa danganawa da rufin ɗakin.
Sai yanzu ta lura, ginin É—akin ma tsawo ne da shi sosai. A hankali yake tafiya, yana zazzaro litattafai yana duddubawa.
Duk iya ƙoƙarin da Nana tayi, domin karanto addu'a, ta kasa ta fara ja da baya tana waige-waige ko za ta samu hanyar guduwa, amma ta kasa samu.
Ta sake ɗaga kai a dubi in da yake, amma taga ba ya wurin, ta yinƙura za ta tashi, amma ta ji tamkar an ɗaureta a cikin sarƙa.
Ajiyar zuciya ta ji an yi a gefenta, ta waiwaya da sauri, ganinsa ta yi zaune a kusa da ita.
Zuciyarta ce take dukan uku-uku, "Kwana da yawa" yayi maganar yana sanya dogayen faratansa a gefen wuyanta, ya tsaga jini ya fara tsatstsafowa.
Ta kalle shi, amma ta kasa kallon idanunsa.
Yayi gyaran murya ya ce "Yaya maganarmu ne, har yanzu babu abin da ki ka yanke a kai? Kar malaminku ya shiga gonata, saboda shi kashe shi zan yi, ba iya korarsa zan yi ba. Ba na son alaƙar ki da shi"
Cikin ƙwarin gwiwa ta ce "Wallahi ba zan yi abin da ka ke so ba, kuma ba ka isa ka hana Ubangiji ikonsa a kaina ba, ko da me ka ke taƙama kuwa" tayi maganar tana jin kamar zuciyarta za ta fito.
Ya ɗan ɗage kafaɗarsa ya ce "Ke ko kewata ba ki yi ba ne? Yaushe rabon da na kawo miki ziyara, na je na yi jinyar abin da ki ka yi mini, na dawo da ƙarfina, mu ci gaba da fafatawa"
A raunane ta ce "Wai dan Allah me na yi maka, me ka ke nema a wurina ne?"
"Kin fi ni sani Nana"
"Ni ba zan yi abin da ka ke so ba, ka nemi wani yayi maka, ni ba zan iya ba"
"Ke aka bani, dan haka ke za ki yi aikin Nana, idan har ki ka amince, zan daina damun ki, zan ma iya barinki ki yi auren ki, amma idan ki ka ci gaba da gardama, wallahi wataran zaki iya tsintar kanki a gidan mahaukata, sai na haukata ki tuburan na hana kowa ya raɓe ki"
Nana tana kuka ta ce "Ba zan yi abin da ka ce ba, ni ba zan yi shirka ba"
"Ni ban ce ki yi shirka ba, bayar da magani za ki yi, wannan shi ne gado da sana'ar gidanku. Waɗannan litattafan duk tarihi ne, na waɗanda na yi wa aiki. Kakar mahaifinki 'yar bori ce, kuma duk wanda aka haifa da irin burujin ki, sai ya yi wannan aikin, ba a samu wanda yake da irin burujin ba wato mai irin tauraronki ba, sai a kanki, abin da baki sani ba, na sadaukar da mahaifina domin kare ki, baban ki yana matuƙar ƙaunarki, a 'yan uwansa waɗanda ba sa shiri, an bayar da jininki a yi masa tsafin kuɗi da ke, muka yi yarjejeniya da aljanin da aka sadaukarwa da jininki, na bashi mahaifina da ya tsufa a matsayin bawa, ya rabu da ke, ke kuma yanzu ki ce ba zaki yi abin da na kare ki saboda shi ba? Ba zai yiwu ba"
"Wallahi ƙarya ka ke yi, dama ai ku babu gaskiya a cikin zantukanku"
"Na yadda, amma ni ba ƙarya nake yi miki ba, samun kyakyawar rayuwarki, yana hannunki Nana" yayi maganar yana kai hannunsa jikinta. Iya ƙarfinta take kai masa duka, tana son ta yi addu'a amma ta kasa sai gurnani, da surutun"Allah ya fika, ba zaka yi galaba a kaina ba, kuma Allah ya isa tsakanina da wadda ta gada mini wannan masifar ni ba mushrika ba ce ba".
A hankali ta buÉ—e idonta, ta ganta tana ta kaiwa iska naushi tana surutu a fili.
Shiru tayi tana waige-waige, ta duba shimfiɗar su Jamila ta ga basa nan, ta ga ƙofar ɗakinsu a rufe, wani irin zafi ta ji a wuyanta, ta kai hannu ta shafa, ta ga jini, a gurin da ya karce ta da farcen sa. Ta nufi ƙofar ɗakin da nufin ta buɗe, amma ta ji a rufe, ta jijjiga amma taƙi buɗuwa.
Gari ya yi haske ba ta yi sallar asuba ba.
"Suwaiba, suwaiba, mama dan Allah ku buɗe mini ƙofa, waye ya kulle ni, ban yi sallar asuba ba fa" shiru babu wanda ya amsa mata.
"Nasiru wai ba kowa a gidan ne, dan Allah ku buɗe mini ƙofa, ban yi salla ba"
Nasiru ne ya leƙo daga soro, ta jiyo muryar Mama daga ɗaki tana faɗin "Kai Nasiru ba ka na leƙowa ba, wallahi ka buɗe mata sai na ci ubanka"
Nasiru ya ce "Mama wallahi ta dawo daidai, ba ki ji tana maganarta normal ba"
"Wallahi ba zaka buɗe ta tana wannan tamɓmelen ba"
A raunane Nana ta ce "Dan Allah mama salla zan yi fa" banza ta yi mata, Nana ta gaji ta koma ta nemi wuri ta zauna, ta na tuna mafarkin da ta yi.
Sallamar baba ta ji a tsakar gida, da alama shi da wasu ne, saboda ba muryarsa kawai ta ji ba.
"Ga ɗakin nan malam, wallahi bamu yi bacci ba, daga mu har maƙwabata, kwana ta yi tana iface-iface, dan kawai na yi mata faɗa kafin ta kwanta, da 'yan shekarun nan, abin nata ya lafa, amma kwanan nan, abin ya dawo tuburan dan kwananta biyu ma, bamu san in da ta tafi ba"
"Kar ka damu, in sha Allah koma menene a jikinta, yau sai ya fita"
Ita dai Nana ta zubawa ƙofa ido, tana jiran abin da zai faru.
Aka buɗe ƙofar, ta ga Baba da wani malamin makarantar allo, da garadan almajirai mutum uku, da wata irin zabgegiyar bulala a hannun malamin, ba shiri ta miƙe tsaye tana zazzare ido ta fara ja da baya.
Malamin ya kalli Nana ya ce "Zaka gane kurenka munafuki, yau sai ka fita daga jikinta, ya tunkaro Nana da wannan zabgegiyar bulala.
A gigice ta ce "Baba, dan Allah lafiyata ƙalau dan Allah kar ka bari ya dake ni, wallahi ni ba aljani ba ce."
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA 002)
BRIGHT PENS 3rd BATCH.
P4
Baba ya tsaya daga bakin ƙofa, yana leƙowa.
Kuka Nana ta fara yi, tana "Dan Allah kar ka dake ni, wallahi a hayyacina nake nice"
"Ƙarya ka ke yi, babu irin aljanin da ban yi karo da shi ba, duk wani siddabarunku na sani" yayi maganar yana riƙe kan Nana, ya fara tofa mata ayoyin Alkur'ani.
Nana ta rasa me yakamata ta yi, ita dai ta san a hayyacinta take, ba ta da zaɓin da ya wuce, ta nutsu ta yi shiru, kar ta yi wani abu, ace aljanin ne. Sai dai jikinta yana ta tsuma, dan tsoron kar malam ya dake ta da bulalar nan.
Sai dai ba ta tsira ba, babu tsammani ya zuba mata bulalar nan a jikinta, sai da ta gantsare ta kurma wani irin gigitaccen ihu, ta zube a ƙasa ta gigice. Yana karanta mata Alqur'ani ya ƙara zuba mata bulalar nan tamkar ta dukan doki.
Ta yinƙura zata gudu, gardi ɗaya ya danƙo ta yayi ciki da ita, suka kewaye ta su na yi mata karatu, malam yana zuba mata bulala yana cewa "Zaka yi magana ko ba zaka yi ba?"
Cikin kuka da ƙaraji ta ce "Ni ba aljani ba ce ba, nice a hayyacina nake, Baba dan Allah ka taimake ni ka ce ya daina duka na" sai jikin Baba yayi sanyi ya ce "Malam ɗayyabu, ba za ayi karatun nan babu duka ba, na ga kamar ita ake duka"
Malam ɗayyabu ya ce "A'a kar ka damu, ka yi haƙuri ka je ka jira mu a waje, ai wannan aikina ne, ba ita ake duka ba, ka jira mu mu gama" ganin Baba zai tafi ya bar ta a cikin maza daga ita sai su, ya sanya ta ƙara fashewa da kuka, ga raɗaɗin bulala da fatarta take yi.