Sashe 10
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana kuwa tun da ta baro gidan, jikinta yake wata irin tsuma, zuciyarta take bugawa, haka kurum jikinta ya din ga bata akwai wani abu na ba daidai ba, a tattare da gidan, ko kuma matar da ta tarar a gidan.
"Hasbunallah wa ni'imal wakil. Wa hifzan min kulli shaÉ—anin marid " ta din ga maimaitawa cike da fatan Allah ya daidaita mata nutsuwarta.
Gaza cigaba da addu'a ta yi, bayan da ta jiyo Baba yana tambayar Jamila, wai gidan uwar É—akin nata, ba su gama abinci ba, yunwa yake ji, Gaddafi ya bayar da kuÉ—in cefane, amma an yi girki an hana shi.
Wani malulun takaici, ya turnuƙe Nana, duk wani salo na zubar da kai, Baba ya iya shi, kuma hakan shi sam baya damunsa ko kaɗan.
Tun da Gaddafi ya dawo, Nana take iya ƙoƙarinta, wurin ta kaucewa yin duk wani abu da zai haɗa su, amma hakan ba ya sanya wa, ta tsira daga zagi da cin mutuncinsa.
Wannan bai dame ta ba, kamar yadda malam Auwal ya rage shiga harkar ta, zuwan ma ya daina yi gaba ɗaya, sosai abin yake damunta, zuciyarta na ta son gazgata cewar Aljanin da yake bibiyarta ne, ya shiga tsakaninsu amma wata zuciyar ta hana ta yadda da hakan, domin malam Auwal mutum ne mai addini, kuma ta yadda duk abin da ya samu bawa muƙaddari ne daga Allah, Aljani bai isa ya hana Ubangiji ikonsa ba.
Duk da ya hanata yin kwalliya a lokacin zuwa makaranta, ko da kuwa man leɓe ne, dan haka yau ta saka jam baki, ko zata samu ya kula ta.
Ta riga kowa zuwa a ajinsu, ta ɗauki tsintsiya, ta fara share ajin, ta shimfiɗa musu tabarma, ta fito harabar makarantar ta share iya in da za ta iya.
Tana shirin komawa ajinsu, Auwal ya shigo makarantar, jinkirta tafiya aji tayi, ta tsaya ya zo zai gifta ta, ta ce "Yaya Auwal ina wuni" wani zirr ya ji a jikinsa, yanayin yadda ta gaishe shin, ya ce "Lafiya ƙalau" ya wuce ta zuciyarsa cike da damuwa, kamar ya waiwayo ya kalleta, sai jikinsa ya ba shi: shi take kallo, dan haka ya fasa waiwayowa.
Tana É—an jima a wurin a tsaye, daga bisani ta nufi ajinsu, gwiwa a sanyaye tana tunanin meyafaru Auwwal ya canza lokaci guda.
Tana ta kallon Alqur'aninta, tana son ta yi tilawa, amma zuciyarta na ta gargaÉ—inta, da tunatar da ita, halin da za ta iya shiga, muddin ta ce za ta karanta.
Tana nan zaune, 'yan ajinsu, suka taru suka fara tilawa.
Malam Auwal ne ya shigo yayi musu ƙarin Alqur'ani, sai dai da ta ɗaga kai, sai su yi ido huɗu da shi yana kallonta.
Sai dai kafin ya kammala ƙarin, ƙafafuwanta sun riƙe gam, su na yi mata wani irin zugi kamar ana karyata.
Gwargwadon ɗaga muryarsu a karatun, gwargwadon raɗaɗi da zugin da ƙafafun nata suke yi mata.
Ba a tashi ba, ta ɗauki jakarta ta bar makarantar, da ƙyar ta nufi gida, tana taka ƙafafuwan nata da kyar.
Ummi ta tarar a gidan, tare da Baba a tsakar gida.
Amsa sallamar Nana suka yi, suka tattara hankalinsu a kanta.
Ummi ta ce "Ummi ya dai na ga kina bin bango, kina tafiya a hankali?"
Ummi ta kalli ƙafafuwanta ta ce "Ƙafafuwana ne suke yi mini ciwo, ba a tashi ba ma na taho gida"
Baba yayi caraf ya ce "Haka dai, kullum cikin ciwo ki ke Nana, yau ƙafa in anjima ciwon kai, gobe kuma ciwon ciki, idan ki ka ƙoshi kuma sai ihu da kururuwa, ni wannan lamarin ciwon naki ya ishe ni wallahi. Can a dangin babarki ki ka kwaso wannan jarabar, ni dangina babu irin wannan"
Ummi ta ce "Baba aka ce mahaifiyar Inna 'yar bori ce "
"In ji uban wa? Ƙarya ne bayar da magani kawai tayi"
Ummi ta yi murmushi, ta ce "Nana ƙaraso magana zamu yi"
Nana ta so wucewa ɗaki, ta kwanta, duk da ta yi murnar zuwan Ummi gidan, amma soki burutsun da Baba ya fara ya sanya duk ta ji komai yayi mata zafi. To idan ubanta mahaifi ya gaza da larurarta ina ga miji, da za su haɗu rana tsaka su yi aure?" Ta zauna a hankali, tana jin yadda ƙafafuwan nata suke yi mata zugi.
"Yaya magungunan da muka karɓo a wurin mutumin nan, kin yi su kuwa?"
Nana ta jinjina kai alamar eh.
"To yaya ki ka ji, akwai sauƙi?"
Da ƙyar Nana ta ce "Eh akwai"
Baba ya ce "Ina fa wani sauƙi, babu sauƙi ko kaɗan sai wurin Allah. Nan na ɗaukko malamin nan na almajiran gangare, yayi mata ruƙiyya wai aljanun suka ƙi magana, ba ki ga dukan da ta ci ba, sai da ta ba ni tausayi amma jiya i yau. Shiyasa duk na damu na aurar da ita, ko na huta. Ai ni wannan zancen da ki ka zo mini da shi, ba ƙaramin daɗi yayi mini ba, Allah ya tabattar da alkhairi tun da shi wancan yaƙi cewa komai".
Cikin mamaki da rashin fahimta, Nana ta ce "Wane zancen ne?"
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM (Ayshercool)
Arewabooks Ayshercool7724
Watpad Ayshercool7724
YOTA 002
BRIGHT PENS 3rd batch
P6
Ummi ta yi murmushi, ta tura wa Nana wata leda gabanta. Nana ta kalli ledar, daga saman ledar take iya hango sabulun wanka da man shafawa.
"Saleh ne ya aiko ni, tun ranar da ki ka je gidana, yake bibiyata shi fa son ki yake yi, auren ki zai yi" take Nana gabanta ya faɗi, damuwa ta bayyana ƙarara a fuskarta ta ce "Anty Ummi, Saleh kuma?"
Baba ya ce "Shi fa, ƙanin mijin Ummi ba yaron kirki"
Jiki a sanyaye Nana ta ce "To Baba Auwwal É—in fa, da ka ce masa ya turo?"
Sai Baba ya hau faɗa ya ce "To ina na ganshi? Tun da na ce ya fito ɗin ya fito? Da a bawa bare ke, ba gara shi ba, tun da ya san larurar ki, idan aka yi auren ba ruwanmu da kayan ɗaki, ya ɗauke ki ya tafi da ke can Ikkon, wurin neman kuɗinsa ba, ɗaki ɗaya ya ishe ku kafin Allah ya yassare masa ku tara zuriya ba. Nana wannan iskokan duk aure ki ke buƙata da kin yi shikenan za su daina damun ki".
Har Nana za ta yi shiru, amma ta kasa ta ce "Baba to idan iyayen malam Auwal É—in suka turo fa?"
Ummi ta ce "Nana wai ƙanin mijin nawa ne ba kya so ko kuwa?"
Gaddafi da yake gefe, tun da ake maganar bai ce uffan ba, ya na ta faman gyara wata radio ya ce "Ai dama ke Ummi ke ce ki ke tausayin yarinyar nan, ita ba tausayin kanta take yi ba"
Nana ta yi shiru ta rasa abin da yake yi mata daÉ—i, ya ma za ayi Ummi ta yi mata haka, ta ce zata haÉ—a ta da wani Saleh, mutumin da ba nutsuwa ce da shi ba, ga shaye-shaye da yake yi, askin da yake kansa kaÉ—ai ya isa ya bayyana maka, abin da yake aikatawa a Lagos É—in.
Ummi ta taɓa ta ta ce "Nana kin yi shiru"
"To me zan ce, Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alkhairi"
Baba ya amsa da Amin.
Nana ta miƙe ta nufi ɗakinsu, zuciyarta babu daɗi, addu'a take yi da fatan, Ubangiji Allah ya sa Auwal ya fito, amma Saleh kam, ba ta tunanin ko me za ayi mata, zata iya aurensa. Dan ko Suleiman da aka fasa aurensu ya fi dama dama a kan Saleh.
Ji tayi jiri yana É—ibar ta, dan haka ta samu wuri ta kwanta, ta din ga yi wa Allah kirari, tana magiyar Allah ya daidaita ta da Auwwal ya fito ya turo iyayensa.
Ummi ta leƙo tayi mata sallama, amma ta ganta a kwance, ta ce "Nana bacci da yammacin nan, ni dai na tafi, in sha Allah zai zo ku gaisa". Nana na jin Ummi, amma tayi banza da ita. Shikenan dan ana so ka yi aure, sai a ace ka auri mutumin banza.
Ranar dai haka ta ƙarasa wunin ranar sukuku, dare ma yayi bacci ya ƙaurace wa idanunta, sai wani azababben ciwon kai da ya kama ta.
A hankali ta din ga juyi a kan shimfiÉ—arta, amma babu bacci babu alamarsa, sai wannan ciwon kan, da take jin tamkar ana sara mata kan da gatari.
A hankali kuma ta din ga jin, tamkar ana ɗaɗɗaureta da sarƙa, ambaton Allah take ƙoƙarin yi, amma ta kasa sai a zuciyarta.
Ta saka hannun tana laluben hularta, domin ta saka a bakinta ta toshe, kar ta yi ihu cikin dare, ta hana mutane bacci.
Ji ta yi an kira sunanta a tsakar gida, duk da ba ta san muryar ba, amma ta amsa a wahale.
Jin an ci gaba da kiran sunanta, ya sanya ta yinƙura da ƙyar ta tashi, kanta babu ɗankwali, ta fito tsakar gida neman mai kiranta.
Kallon tsakar gidan tayi, taga duhun ya ninka na dare, ba ta iya gane komai a tsakar gidan. Ta juya don ta koma cikin É—aki, amma ta rasa hanya, saboda duhu ba ta ganin komai.
Ji ta yi an ci gaba da kiran sunan ta, kawai ta hau tinkarar wurin da take jin ana kiranta.
Gaddafi yana shagonsa a ƙofar gida, ya ji an buɗe gida, ya duba agogon wayarsa, ƙarfe biyu saura mintuna tara na dare.
Tashi yayi ya leƙo, ya ga Nana ta fito, daga ita sai zani da vest kanta ko ɗan kwali babu.
Sai da ya bari ta yi nisa, sannan ya fito ya bi bayanta, a zaton sa ko wani yawon banzan take, sai dai ga mamakinsa kawai tafiya take yi.
Ganin tafiyar ta ƙi ƙarewa ya sanya ya ce "Ke dan ubanki ina za ki je a tsohon daren nan?" can kamar a wata duniyar, haka take jiyo muryarsa. Ba ta tsaya ba, kuma ba ta yi magana ba, ta cigaba da tafiya.
Danƙo hannunta yayi, ya din ga jan ta har zuwa gida, sai dai ba ta yi masa musu ba, bin sa kawai take yi, dan ta kasa tantance bacci take yi, ko kuma a zahiri ne.