← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 32

Sashe 18

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Akwai wani hatsabibin shaiɗani a tattare da yarinyar nan, ya lalata mana aiki gaba ɗaya. Ba a samu adadin jinin da ake buƙata a jikinta ba"

Dafe kai Hajiya Sa'a tayi, ta ce "Yanzu mene ne abin yi, ka ce akwai sa'a a tattare da yarinyar yanzu babu wata dabarar kuma? Yarinyar ce wata irin majanuniya, har kaya na bayar a kai mata, babu yadda ban yi a sake kawo mini ita gidan yarinyat Safiyya ba, dama a can na ganta wai ta ƙi yarda. Ni kuma na abin na je gidansu ba, ba na son zargi da saka ido"

"Aikuwa neman mafita ya ganki, domin wani baƙin sheɗani ne a tattare da ita, babu lallai ya bari wani ya raɓe ta, saboda wasu dalilansa, 'yar aiken tamu ma ya ƙona ta. Yanzu dole ki san yadda za ki yi, a sake ba ta maganin zamu sake tura wani ɗan aiken"

Hajiya Sa'a ta jinjina kai ta ce "Amma, ba yadda za ayi a samo jininta nata, dole sai an bata wani abin ta ci?"

"Eh dole ne, idan ba haka ba babu ta yadda za a samu jininta, ba zai bari a tunkare ta ba. Kuma ko ba haka ba, idan ba ta hanyar abincin da za a bata ba, ba kowane aljani zai iya raɓarta ba, saboda tana zama da alwala, kuma tana adduo'i shi kansa aljanin jikin nata, ba ƙaramar azaba yake sha ba. Dan haka yanzu ko dai a samu jininta ta wannan hanyar ko kuma ki janyo ta ƙungiya"

Hajiya sa'a ta ce "Ba abu ne mai sauƙi ba hakan, muguwar miskila ce, ba kamar 'yar uwatta ba, da ɗayar ce ko nan ka ce na kawo maka ita, zan kawo ta, amma babu komai zan san abin yi, dole haƙata ta cimma ruwa"

"Babu laifi"

****
A hankali jikin Nana ya ci gaba da yi mata raɗaɗi, tamkar ana kunna mata wuta, ta daure ta din ga nanata suratul jinn, tun daga farko har ƙarshe a zuciyarta.
Imaran ne ya dawo bayan sallar isha'i, hannunsa riƙe da ledoji.

"Nanawo, sannu ya jikin?" Yayi maganar bayan ya ja kujera ya zauna.

"Jiki Alhamdilillah"

"Kai Nasiru É—aukko faranti" yayi maganar yana kallon Nasir.

Ya je ya É—aukko faranti, ya zazzage musu gurasa da nama fal a kai.

Ya kalli Nana ya ce "Ina Jamila ne? Tun da na dawo Suwaiba kawai na gani, ko an yi mata aure ne?"

Nana ta ce "A'a tana maƙwabta"

Ya tsuke fuska ya ce "Har bayan sallar isha'i, kamar gidan ubanta?" Yana rufe baki ta yi sallama.

Sai dai ta tsaya da ta ga Imaran, ta ce "Imran dan Allah kai ne ko gizo idona yake yi mini?"

"Ban sani ba, tun la'asar ba kya gida kina can kina gantali a gidajen mutane"

"Haba ai ka bari mu gaisa, ina ka tafi shekara uku ba wanda ya san inda ka ke?"

"In da ki ka aike ni. ware ki wanko hannu ku zo mu ci abinci"

Ta ce "Yanzu ma kuwa"

Cikinsu ya shiga, suka rufarwa gurasar, yana kallon Nana, da ƙyar take ci. A haka Gaddafi ya shigo ɗaukar abincin dare ya tarar da su.

Imran ya kalli Nana ya ce "Wai ba za ki ci ba ne?"

"Imrana ba a É—ebarwa Baba ba, Mama ba a bata ba"

Haushi ne ya kama shi ya ce "Wallahi ba zai ci ba, da na zo ko ruwan gidansa ya bani, ba kora ta ma ya yi ba? Kar Allah ya sa ki mayar da hankali ki ci"

Abinka da 'yan uwa, haka suka kewaye Imran.

Jamila ta ce "Wai dan Allah tsawon wannan lokacin, ina ka tafi?"

"Duniya na shiga mana, tun da an kore ni an ce ba a buƙata ta a gidan"

Baba yayi sallama, suka amsa masa gaba É—aya.

"Imarana ban ce ka bar mini gida ba wai?"

"Wallahi Baba ba zan bar gidan nan ba, sai na gama abin da nake yi"

A fusace Gaddafi ya ce "Wai kai baban  ka ke yi wa magana a haka?"

Imran ya kalle shi ya ce "Kai kuma ina ruwanka da ni? Kai a yaya ne baka yi masa magana, ya taɓa korarka ne? Ka ga tun da na zo ban kula ba kar ka shiga harkata ehee"

A fusace Gaddafi ya yo kan Imran, Imaran ya miƙe tsaye ya ce "Wallahi yanzu ba da ba ce, wallahi ka taɓa ni sai na soka maka ƙarfe".

Baba ya tare Gaddafi ya ce "Rabu da shi, kar ya yi maka rauni, alamu sun nuna haryanzu yana shaye-shaye"

"Wallahi Baba ko uban me yake sha, dai-dai nake da shi, ka bari na sauke masa tsagerancin da yake kansa"

"A'a gara dai ya riƙeka, dan wallahi ka taɓa ni sai na buga ka da ƙasa ba abin da ya dame ni" ya kaɗe rigarsa ya fice.

Nana ta dafe kanta, ta rasa abin da yake yi mata daÉ—i, tun tsaowar su Baba ba sa shiri da Imran ko kaÉ—an, tabbas a baya babu wanda suke tsoro sama da Gaddafi sun daku a hannunsa, saboda ya ce babar su ce ta yi sanadin da aka saki babarsa, kuma har ta mutu Baba bai dawo da ita ba.

Ta yi alwala ta yi sallar isha'i ta kwanta, ba dan tana jin bacci ba.

Kwanciyarta ke da wuya, ta lumshe idanaunta, ta lula duniyar tunani, ta buÉ—e idonta domin juyi ta gyara kwanciyarta, kawai ta ganta a bakin wani ruwa a zaune.

Ta É—aga kai ta waiwaya, ba kowa a wurin, sai dogwayen bashiyu koraye shar, ruwan gabanta kuma sai tambal-tambal yake yi tamkar zai yi ambaliya.

Ta kalli jikinta, ta ga babu kaya a jikinta, sai wani ɗan mayafi da aka rufe mata ƙirjinta, zuwa al'aurarta.
Jikinta duk ya ɗuri ruwa, ya kwaile saboda ƙuna.

Ta yinƙura za ta ja ƙafafuwanta, ta tashi ta gansu ɗaure a jikin sarƙa.

Free pages na daf da ƙarewa. Contact me to subscribe yours.
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU
YOTA/002
AYSHERCOOL

P10

Ta waiwaya jin maganganun su Suwaiba, a kusa da ita, har su na faɗa a kan charger, amma ba ta ganinsu sai ita ƙwal a wurin.

Ta rintse idanunta, tana faɗin "La haula wala ƙuwwata illa billah"

Ji ta yi an taɓa ta, ta buɗe idonta tana tsammanin ganinta a ɗakinsu, amma ta ganta dai a wurin a zaune.

Ya durƙusa ya kwance sarƙar ƙafarta, sannan ya kalleta, ba ta iya kallonsa, duk da a suffar mutum ya bayyanar mata, duk da dogwayen yatsunsa masu ɗauke da zaƙo zaƙon farata sun fallasa bambancin da yake da shi da bil adama.

"Kalli jikin ki, kalli irin raunukan da suke jikin ki, saboda azabar taurin kan ki da dan halin ki zan bi, da sai dai ciwon nan yayi ajalinki"

Nana ta É—an kalle shi, ta kawar da kanta ta ce "kai ne fa ka yi mini raunin, da tartsatsin wutar da ya din ga fitowa daga bakinka"

Ya dube ta ya ce "Ba zan yi miki irin wannan illar ina sane ba, kafofin da za a din ga zuƙar jininki ake so. Ina sake jaddada miki ki karɓi abin da ƙaddara ta zana miki. Ni hadiminki ne zan zama mai biyayya a gare ki, idan kuma ki ci gaba da bujirewa zan ci gaba da azabtar da ke, dan rayuwata ba za ta salwanta a banza a kan ƙoƙarin kare ki da baiwarki ba, ba wannan aikin na karɓi yi daga wurin kakaninki ba".

Ta ɗan ɗago ta ce "Wani irin aiki ka karɓa a kaina, kuma meyasa ka dage lallai ni zan yi harkar bori? Kai ba ka ga ilimin addini ya yawaita ba yanzu? Su ma na yi imani da Allah, rashin ilimi ne ya sanya su ka yi wannan harkar. Kuma duk sauran mutanen dangin babu wanda za ka matsawa ya yi harkar shirka sai ni?"

"Ba ni da lokacin da zan tsaya yi miki wani dogon bayani, amma ina mai tabbatar miki tashin hankali da masifun rayuwa yanzu a ka fara, ko ƙafa ba ki saka ba domin ba ayi komai ba".

Nana ta ce "Abin da Allah ya ƙaddara ya zai same ni ne kawai zai faru da ni, na zan taɓa yadda da duk wata tatsuniya da za ka karanta mini ba"

"Shikenan, ba na buƙatar dama ki yarda, zan cire hannuna na ja da baya na zura miki ido, da kan ki za ki neme ni".

"Da ni da kai duk bayin Allah ne, dan haka babu yadda za ayi na nemi taimakon ka. Ko da ka tare mini wani abu, Allah ne ya tare mini kai sila kawai za ka zama" Ta yi maganar cike da ƙwarin gwiwa.

Yayi mata shiru, ya juya ya kalli ruwan nan, ya fara fito da wata baƙar iska daga bakinsa yana hurawa ruwan. A take iskar ta dinga tafasa ruwan har da tururi. Ya kwantar da Nana, ita kuwa ta zuba wa sarautar Allah ido.

Ya ce "Maganin da matar nan ta baki ki ka sha, ta samu damar tsinka wata jijiya a mararki, shi ne ki ke wannan fitsarin jinin kuma sun samu sun tara, duk da bai ishe su ba.
Wannan ciwon na jikinki, ba ƙonuwa ba ce ramuka suka yi miki, jininki na zubowa ta ramukan sai dai ba za su iya amfani da shi ba, saboda yana jikin fatarki ne kuma ba za su iya raɓarki a haka ba" Nana jin sa kawai take yi, ba wai dan tana yadda da maganganun na sa ba.

Ya din ga ɗebo ruwan tekun nan, yana zuba wa Nana a jikinta. Ta rintse idanunta tana jin yadda wani irin zafi yake ratsata har cikin ƙashinta.
Ya zira hannunsa a cikin bakinsa, ya zaro wata doguwar allura, ya shammaci Nana ya caka mata a mararta. Ta kurma ihu sai da gaba É—aya dajin ya É—auka.

A zahiri kuwa, tun da ta lumshe idonta, jikinta yake rawa haƙoranka suna karo da juna, idanunta suka kakkafe.

Su Jamila suka fito suka bar mata ɗakin,  zuba mata ruwan nan da ƙaisar yake yi, a zahiri ihu take yi.
Gaddafi ya je ƙofar ɗakin ya tsaya yana bala'i.
Chapter 18 · 0% Book details