Sashe 17
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"A'a yanzu dai nake saka ran zuwanta"
"Dan Allah, ki É—an bugi cikinta ki ji, yarinyar nan ta sha lemon kuwa?"
Maman khairat ta ce "In sha Allah, zan bugi cikinta zamu yi magana da ita"
"Amma ina fatan, ba ki gaya mata ko na mene ne ba"
"A'a haba Hajiya, ya ma za ayi na gaya mata, ai kin ce ko wani ma ya ci ba komai, ita É—in dai ake so ta ci, zan tambaye ta idan ta zo"
"To shikenan, na gode sai na ji ki"
*****
Ƙamshin turare ne ya cika wa Nana hanci, sai dai ba ta motsa ba ko ta buɗe idanunta ba.
Teburin da take kai, ya É—an bubbuga, sai a lokacin ta buÉ—e idonta a hankali. Dishi-dishi ta fara gani.
A hankali idonta ya washe, ta É—aga kai ta kalle shi.
Yayi murmushi ya ce "Anty ya dai ki ke bacci, ko babu lafiya ne?" A hankali ta tashi zaune, ta kalli agogon ajin nata ƙarfe biyu. Tunani ta hau yi, tun da ta shigo da safe take wannan baccin, ko kuwa?
Maganar Muhsin ce ta dawo da ita hankalinta ya ce "Anty kin ga na gama" yayi maganar yana nuna mata littafin sa, da ya cika page guda da A.
"Afuwan Anty Nana, direbansu ya yi tafiya ne, mahaifiyarsa babu lafiya, ni kuma ba ni da isasshen lokaci, na shiga wani meeting ne, shi yasa na daɗe ban zo ɗaukarsa ba, ki yi haƙuri na ɓata miki lokaci". Jinjina kai kawai ta yi ta tashi, ya ce "Mu je sai mu sauke ki a hanya" sai dai haryanzu ba ta yi magana ba, ta bi shi su ka tafi.
Jamila na zaune, tana ta zaman kashe wando a gidan maman khairat, kamar yadda ta mayar da hakan ibada, tana tayata aiki su na hira.
"Ni kuwa jiya kin ci abincin jiya Jamcy?"
Jamila ta ce "Lallai ma Anty Safiyya, me zai hana ni ci, na yi abincin kuma na kasa ci?"
"Wallahi ni gaba É—aya kasa cin abincin na yi, na ce da na sani, na ce ki tafi da shi duka"
Jamila ta ce "Subhnallah, ko dai Khairat za a yi wa ƙani"
Tayi murmushi ta ce "Rufa mini asiri, wallahi sai da ki ka tafi na ga kamar abincin ba zai ishe ku ba, kuma har su Nana duk sun samu sun ci?"
Sai da Jamila ta yi mamakin tambayar, amma ta ce "Eh mana, Nana ce ma babu lafiya, ba wani ci ta yi ba, kin san 'yar ƙi faɗi ce, sai na je da abu sau shurin masaƙi amma babu lallai ta ci"
"Eyya, to ai ba komai, mun riga mun zama É—aya Allah ya ba ta lafiya, ta sha lemon ma?"
"Eh amma ba da yawa ba"
Safiyya ta jinjina kai ta ce "Dan Allah ki yi mata sannu"
Jamila ta ɗan taɓe baki ta ce "To, za ta ji, kin san ita kullum cikin ciwo take ne, abin nata ba na ƙare bane ba"
Suka ci gaba da hira, ƙasan zuciyar Safiyya, cike da farin ciki
*****
Ƙarfe huɗu da rabi na yammaci, sannu a hankali yake ƙarewa garin kallo, duk ya kwana biyu baya garin, amma ba wani abu ne ya canza ba, amma har cikin zuciyarsa yake jin kewar Kanon dabon.
Tun daga can babban titi ya sauka, ya saɓo hanya, domin ya samu isashshiyar damar ƙarewa garin kallo, yadda yake so.
Dandazon mutane ya hango a wani wuri, mutane na ta surutu da hayaniya.
Har ya yi gaba, kawai ya dawo da baya domin ganewa idanunsa abin da ya tara wannan cincirindon al'ummar.
Ya din ga kutsawa, yana ture mutane.
Kawai ya tarar da wata matashiyar budurwa a kwance a wurin, sai dai ta juyar da fuskarta ba a iya ganin fuskarta.
Ya taɓa wani mutum ya ce "Malam lafiya, me ya faru don Allah?"
Mutumin ya ce "Wallahi tun azahar, muka ganta a kwance a wurin nan, an zata ma ko ba ta da hankali, ko kuma ba ta da lafiya, amma jikinta fes babu datti ba alamar hauka a tare da ita. An yi anyi ta tashi ko motsi ba ta yi, kuma tana da rai. An duba jakarta babu waya sai maka da kuÉ—i, yanzu ma dai an kirawo 'yan sanda".
Bai ce uffan ba, cikin azama ya nufi kanta, mutane na ƙoƙarin hana shi, amma bai saurari kowa ya je kanta ya ɗago ta.
Idanunta a rufe, sai dai hawaye da yake ta fita ta gefen idonta, ga jikinta zafi tamkar wuta.
A sanyaye ya ce "Nana" shiru ba ta amsa ba.
Miƙewa yayi yana ƙoƙarin ɗaukarta, wani ya ce "Malam lafiya, ina zaka kaita?"
"Ƙanwata ce" ya faɗa a taƙaice, ya fita ya taro adaidaita sahu. Bai sake tsayawa yi wa kowa bayani ba, ya saɓa Nana ya shiga adaidaita sahu, ya tafi da ita.
Mama na tsakar gida tana tankaÉ—en tuwo, sai ganinsa tayi a tsakiyar tsakar gida.
Suwaiba da take jan ruwa ya kalla ya ce, "ShimfiÉ—a mini tabarma a tsakar gida"
Ta ajiye gugan, ta É—aukko tabarma, ya kwantar da Nana a kai.
Ya ɗebo ruwa a kofi, ya zo ya zauna a kusa da ita, yana ƙare mata kallo, gaba ɗaya ta rame sosai da sosai.
Cirko-cirko mutanen gidan suka yi, su na bin sa da kallo, kowa da magana a bakinsa, amma babu damar furtawa.
Ya tofa ayatul kursiyyu, da falaqi da nasi, kowacce da bismillah, ya shafa mata ruwan a fuskarta, da tafukan hannayenta. A hankali yake bin jikint da kallo, yana mamakin shaidar duka ce, ko ta ƙonuwa a jikinta.
"Nana" ya kira sunanta. Cikin sa'a sai ta buÉ—e idonta a hankali, ta sauke a kan fuskarsa.
Shiru ta yi tana kallon sa, kamar ba ta taɓa ganin sa ba, zuciyarta na raya mata kawai tarkacen mafarkin da take yi ne. Ta yi shiru, ta tuna ta shiga motar baban Muhsin, su na tafe a hanya, a kunnenta ta ji ana ce mata, ga Auwal can a marrraba, nan da mintuna goma tirela za ta taka shi.
Babu shiri ta tsayar da baban Muhsin, bai gama parking ba, ta buÉ—e motar ta fita daga nan kuma, sai ta É—imauce ta rasa gane gaba da baya.
Mayar da idanunta tayi ta sake lunshewa.
"Ma'u" ya kuma kiranta yana matsa hannunta.
Ta sake kallonsa a hankali ta ce "Wai da gaske kai ne?"
"To da waye? Dama haryanzu ba ki warke ba, ki na wannan ciwon Nana? Kuma uban waye ya dake ki duk jikin ki ya tashi haka?" Ta yinƙura ta tashi zaune, kawai ta fashe da kuka.
"To kukan uban me ki ke yi kuma? Na ce uban wa ya dake ki?"
"Ba dukana aka yi ba" ta bashi amsa tana share hawayenta.
"To me ya kai ki yin bacci a titi, maza sun baibaye ki, kamar ƙudaje sun ga mangwaron Binta suga"
Ba ta bashi amsa ba, ta ci gaba da kuka.
Ya tsuke fuska ya ce "Dalla yi mini shiru, ina yi miki magana ki na wani kukan banza"
"Me yasa ka tafi ka bar ni?" Ta yi magana cikin kuka.
Guntun tsaki yayi, ya ce "To dai ba ga ni na dawo ba? Uban me ake tsinana mini a gidan idan na zauna, yanzun ma tunaninki ne ya addabe ni, nake ta mafarkinki shiyasa na taho, kuma ina zuwa na tarar da dandazon mutane, ina dubawa na ga ke ce. Allah dai ya tsinewa wannan matsiyatan aljanun naki banzaye marasa imani"
Za ta yi magana, Baba yayi sallama suka amsa, sai dai ya ja tunga ya tsaya, ganin wanda bai taɓa zato ba a gidan.
"Kai imrana, uban me ka ke yi mini a gida? Me ya kawo ka gidana?" Tsuke fuska ya yi ya ce "Kamar yaya? Ya ka ke magana kamar wani shege ba kai ka haife ni ba? Gidan ubana na zo, kuma wurin 'yar uwata na zo"
"Ban yi maka iyaka da gidana ba? Ki na me ki ka bari ya shigo mini gida?" Yayi maganar yana kallon mama.
A ƙufule ta ce "Au to kokawa ka ke so na yi da shi? Ko saɓa shi zan yi na jefa waje, tun da kai ka dawo sai ka fita da shi ai"
Ya sake kallon imrana ya ce "Ba magana nake yi maka ba? Ban hanaka zuwar mini gida ba?"
Cikin rashin É—a'a Imaran ya ce "Sai ka ce wani gidan kirki, to ka mayar da ni in da na fito, cikin uwata ta mayar maka da ni"
Nana ta ce "Imarana Baba ne fa"
"Shi ɗin, shekaru uku ba ka ga ɗanka ba, da haka yakamata ya karɓe ni komai girman laifin da na yi masa? Ba azabtarwa da ake yi mana ne ya tilasta mini barin gidan nan ba"
Gaddafi ne ya shigo, bayan dawowarsa ya jiyo hayaniya daga cikin gidan ya shigo, domin duba abin da yake faruwa.
Shi kansa mamaki ne ya kama shi, ganin Imran a gidan.
Baba kamar ya fashe da kuka ya ce "Imrana ni ka ke gaya wa haka? Ka tashi ka fita ka bar mini gida na ce maka"
"Idan na bar gidan shege nake, wallahi sai na gama kwanakin da zan yi. Ke Nana ga jakata nan zan je na dawo.
Nana ta tashi ta É—auki jakar, ta nufi É—akinsu da ita, Baba ya daka mata tsawa ya ce "Bashi jakarsa ya bar mini gida"
Cikin kuka Nana ta marairaice ta ce "Dan Allah Baba ka yi haƙuri, tun da ya ce idan ya gama kwanakinsa tafiya zai yi. Shekara uku ban ganshi ba, dan Allah ka yi haƙuri"
"Au Nana kin fi son É—an uwanki da ni ko? Amma yana sane da mu, ya kama gabansa ya tafi gantalinsa har shekaru uku, yana gararamba bai waiwayo gida ba, sai yanzu saboda ya mayar da ni É—an iska zai dawo mini gida?"
Imaran ya nufi Nana, ya karɓi jakarsa, ya kaita wani ɗan lungu ya ajiye, ya fice ya bar gidan. Shi kansa Gaddafi kasa magana ya yi, saboda tsagwaron zunzurutun tsageranci kawai yake iya ganowa a cikin idon Imran ɗin.
*****
"Hajiya Sa'a aiki ya lalace fa"
"Ban gane ba, kamar yaya?"