← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 32

Sashe 24

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ga yadda ake jere masu taɓin hankali, wasu a cikin mari aka ba su abincin safe, lafiyayyen kunu da ƙosai. Gaba ɗaya suka zuro wa Nana ido. Masu ɗan sauran hankalinsu, su na ta gaida Salamatu tana amsa musu cikin sakin fuska.
Masu rashin ji a cikinsu, su ƙi cin abinci, su na ganinta suka kama kwanukan abincinsu. A gaba kaɗan kuma ɓangaren ƙananan yara ne, masu larurar ƙwaƙwalwa, da ake iƙrarin aljanu ne su ka sanya musu. Wasu ɗauke ciwukan da a turance ake cewa (Down syndrome, autism, poliomyelitis) da sauran su wato masu shan inna, galhanga da sauran su.
Suka ƙara yin gaba, suka ɓullo gurin da ake Sakiya, kamar yadda ta hango jiya da suka zo. Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, ta rintse idanunta yau ma kibiya ake sakawa a cikin magani, sai a ciro ta a saka a cikin wuta, ta yi jawur, aka ciro ana sokawa a cikin wani mutum da cikin ya kumbura tamkar zai fashe. An tara wata tasa wani irin koren ruwa yana kwararowa daga cikin nasa mai azabar wari.
Mutumin yana zaune, tamkar ba cikinsa ake hudawa ba.

Salamatu ta ce "Tsoro ki ke ji har haka? Sun je Asibiti aka ce hantarsa ta lalace, sai dai ayi masa dashen wata, su kuma iyalansa ba su da hali, aka kwatanta musu nan. Lokacin da aka kawo shi, ko tafiya ba ya iya yi, yau satinsa guda a nan yana iya takawa"

Cikin damuwa, a kuma karon farko Nana ta yi mata magana kai tsaye ta ce "Ba ya jin zafi kuma? Da me zai ji? Zafin wuta ko ciwon, ko kuma huda shin da ake yi, idan ya mutu fa?"

Salamatu ta yi murmushi ta ce "Ai ba da ka muke aikin ba, kamar yadda asibiti suke da anesthesia, magunguna da alluran kashe zafi, mu ma mu na da su, irin namu na gargajiya, ba ya jin komai. Ilimi ne ya bawa likitoci damar sanin cuta da magani mu ma kuma haka"

Nana dai ba ta gamsu ba, ta ji ne amma ba ta yarda ba.

Sai yanzu take jinjina girman gidan, su shiga nan su ɓulla can, ko ina ɗaki-ɗaki ne na marasa lafiya a gidan.

Wata ƙaramar ƙofa su ka shiga, amma ta ga sun fito wani katafaren ɗaki ƙato, ba wai kayan alatun zamani ne a ɗakin ba, kawai dai an tsara shi ne.
Ta kalli ƙasan ɗakin, an rufe shi da fatar dabbobi daban-daban, wata ta gane ta wace dabbar ce, wata kuma ba ta gane wacce ce ba.
Hatta jikin bangon É—akin, an yi masa ado da fatar dabbobi, ta damisa kawai ta iya ganewa da kura, su ma dan tana gani a tv ne wasu lokutan.
Ga kuma ƙahunhunan dabbobi su ma, an ƙawata ɗakin da su, sai kuma jakunkunan fata suma duk an rarrataye su a ɗakin. Ga curin layoyi su ma duk an yi musu guri a ɗakin.

Yana zaune a kan wata karaga, mai ɗauke da ƙwarangwal ɗin kawunan zaki, bayan karagar kuma an yi mata ado da kawunan macizai.

Nana ta yi tsuru, tana tunanin anya ma a zahiri take, ko dai kawai tarkacen mafarkin da ta saba yi ne.

Tasowa yayi jikinsa sanye da kayan fatar giwa, yana faɗaɗa murmushinsa ya ce "Barka da zuwa baƙuwa ta mussaman, lale da ke" Nana ta yi shiru tana kallonsa, duk da ta gane shi, lokacin da aka kawota ta ganshi, amma ba a wannan ɗakin ba, kuma yau baƙinsa ya ragu.

Salamatu ta ce "Sarki ga ta na kawo ta, ta tashi lafiya ƙalau"

Ya ce "Alhamdilillah Allah abin godiya, Nana Asma'u na san kin gane ni, amma ba ki sanni ba, ni ne Garba mai tagwayen baiwa, Sarkin bakar ƙasar hausa, kuma ana yi mini take da Garba ga baka ga aska. Salamatu ba ta abin zama".

Salamatu ta zura hannu a wata 'yar ƙaramar jakar fata, ta  janyo wani abu da Nana ba ta gane ko mene ne ba, shi ba kujerar tsuguno ta mata ba, shi dai ga shi nan. Tana tsaka da kallon abin ta ga yana motsi, ta ƙura ido kawai ta ga kan kunkuru ya leƙo ashe kunkuru aka ba ta a matsayin abin zama.
Babu shiri ta doka tsalle ta ja gefe tana kallon kunkurun.

Sarkin baka ya bushe da dariya, ya ce "Tuba muke, mu je ki ga yadda muke gudanar da ayyukan gidan, ko kya saki jiki ayi abin da yakamata"

Wata mata ce ta faɗo ɗakin babu ko sallama, bafulatana doguwa mai tsayi fiye da kima. Tana shigowa Nana ta ji zuciyarta ta yi wani irin gigitaccen bugu, da sai da ta zata mutuwa za ta yi. Matar ba ta ce komai ba, ta shirya ƙorran da ta shigo da su a wata ragaya.
Sarkin baka ya ce "Idan kin gama, ga saƙonki can" bafulatanar ba ta ce komai, ta buɗe wata randa ta ɗebo wani baƙin abu ta sha, ta zo za ta wuce Nana ta fita, Nana ta sunkuyar da kanta ƙasa ta fice daga ɗakin.

"Asma'u kin ga matar da ta shigo ne?" Nana ta jinjina masa kai jikinta yana rawa.

"Me ki ka gani a tare da ita?"

Da ƙyar Nana ta ce "Ba ta da ƙafafuwa, a kan iska take tafiya" tayi maganar bakinta yana rawa.

Ya É—an yi shiru, Salamatu ta ce "Ya buÉ—e mata ido kenan tana ganin komai"

Sarkin baka ya jinjina kai, ya ce "Taho muje" ya tashi ya yi gaba su ka bi shi a baya.

Wani guri suka nufa, sai da suka je daf da wata ƙofa, ta fara jiyo ihu mara daɗin ji. Ya buɗe ƙofar ya shiga, sai dai Nana ta kasa shiga.

Salamatu ta ja hannun Nana da ƙarfi, su ka shiga, sai gurin ya rikiɗewa Nana tamkar a film, mahaukata ne a ɗaki-ɗaki, tamkar a prison, su na ta kurma ihu sai ta ga ashe waɗanda ta gani da farko ba hauka suke yi ba, wannan ne masu yin hauka na gaske. Tamkar shirin fina-finan zombie, haka suke ihu su na ziro hannayen su. Nana tsigar jikinta ta din ga tashi, tana jin tamkar ita ma ta fasa ihu saboda rawar da jikinta yake yi, da wani irin azabar ciwo da kanta yake yi.
Hatta haƙoranta da laɓɓanta rawa suke yi, ya yin da sautin ihu da kururwar mahaukatan, ya ci gaba da amsa kuwwa a cikin kunnuwanta, ta rintse idanunta tana sauraron bugun zuciyarta a cikin kunnuwanta dummm dummm da ƙarfin gaske.

Tsawa Nana ta yi hakan ya sanya gaba É—aya su ka yi shiru, su na kallonta, tamkar an yi ruwa an É—auke, a hankali ta buÉ—e idanunta domin ta ga tsawar da ta yi ce ta sanya su yin shiru, ko kuwa?.

Sai dai ta ga tabbas ita É—in ce ba wani ba.

Sarkin baka ya kalleta tare da sakin wani irin ƙasaitaccen murmushi da shikaɗai ya san ma'anarsa.

Wannan littafin 1k ne a telegram, ta wannan account É—in 0069685771
Aisha Adam stanbic ibtc bank
Sai shaidar biya ta 08081012143
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA 002

P13

Ya sake duban Nana ya ce "Manya gatan wasa, uban duƙusa uban haɗari, ai shikenan tun da haka zamu yi da kai"

Ya yi gaba yana ci gaba da murmushi, ya din ga bayar da umarnin abin da za a yi wa marasa lafiya, tare da yi wa Nana bayanin aljanun da kowanne yake É—auke da shi, da dalilin da yasa ya kama mutum.
Nana ta sha mamaki, wasu a dalilin harkar bokanci, da ta'amalli da aljanun ya sanya suka haukace, wasu kuma sun yi ƙoƙarin amfani da aljanun ne dan su yi kuɗi, su ma suka haukata su. Wasu kuma sharuɗɗan da aljanun suka saka musu, suka gaza cikawa ya sanya suka haukata su.
Ya nuna mata wasu hamashaƙan 'yan kasuwa ne, da masu kuɗi a ka yi musu sihiri da aljanun da suka haukata su.
Babban abin da ya bawa Nana tausayi, har da wata matashiyar budurwa, da ta zubowa Nana ido, tamkar ta haɗiye ta. A hankali Nana ta taka ta nufe ta. Ta zuro hannunta ta tsakanin ƙofar ɗakin, tana miƙowa Nana.
Nana ta miƙa mata nata, ta din ga shafa hannun Nana sannan ta ce "Kin san tazarar da ke tsakanin ƙasa da iya gejin da jirgi yake zuwa a sama? Nigeria mu na da tarin karatu, goyon bayan ƙasar mu kawai muke buƙata, mu je in da zato bai taɓa zato ba. Ina da burin ina raye kafin na mutu, na kasance cikin waɗanda za su ƙera wa Nigeria jirgin sama nata na kanta. Dan Allah ki saka baki na je ƙaro karatun nan, na warke fa ki ce ya sake ni" ta yi maganar tana kuka.

Sarkin baka ya ce "Kubra Yusuf, in sha Allah burin nan naki zai cika da zarar kin warke"

Cikin kuka ta ce "Ai na warke dan Allah ka kira Daddy a mayar da ni gida na tafi karatun nan, kar na yi missing Flight"

Cikin damuwa Nana ta ce "Dan Allah a fito da ita daga É—akin nan, kamar ta warke fa"

Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Ai ba da baki ake gane wanda ya warke ba, yanzu ana buɗe ta, sai ta kusa hallaka ki a gurin nan. Ainihin ta 'yar makaranta ce, degree ne da ita a engineering, kuma ita ce overaller a department ɗin su. Ta fita da makin da ba a taɓa samu ba a tarihin department ɗin su. Gwamnatin tarayya ta biya musu kuɗi su je su ƙaro karatu a kan fsahar ƙere-ƙere su biyar, ita kaɗai ce mace daga arewa. Shi ne aka yi mata asiri da wani baƙin aljani, aka ba shi jinin mutum, ta taso daga makaranta ta ba shi sadaka, shi yake ta azabtar da ita, a hakan ma zamanta a gidan nan, an rage ƙarfin tasirinsa.
Cikin tausayawa Nana ta din ga kallon yadda ta koma gefe, ta zauna tana ta kuka da ƙarfinta. Haka suka wuce ta.

Bayan sun baro gurin, suka tafi wani guri, shi kuma jarirai ake kawo wa sabuwar haihuwa, domin yi musu aski, kaciya da cire beli.
Chapter 24 · 0% Book details