← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 32

Sashe 22

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka har suka ƙarasa ƙofar gidan, Ko da su ka shiga gidan, jikin Nana ya hau rawa, sai dai hakan bai hanata gode wa Allah da halin da ga tsinci kanta. Saboda yadda ta ga wasu a cikin mari su na hauka tuburan, ban da masu ciwon galhanga, shan inna da sauransu.
ÆŠaki É—aki ne a gidan, ma'aikatan gidan, duk su na sanye da jajayen kaya, kamar ma'aikatan jinya a asibiti.
Hankalin Nana yayi mugun tashi, da ta ga ana yi wa wasu daga cikin marasa lafiya sakiya. A saka kibiya a cikin magani, sannan a sakata a cikin wuta, sai ta yi ja sannan a soka a gurin da yake da larura.

Sai da tsigar jikin Nana ta tashi, hankalinta yayi mummunan tashi.

Su na ƙoƙarin shiga ƙofar da za ta sada su, da ainihin gurin da mai maganin yake ganin marasa lafiya, idon Nana ya sauka a cikin na ɗaya daga buzaye ukun da suke ƙoƙarin fitowa daga cikin gurin.

Ji ta yi tamkar an watsa mata wuta a cikin idanunta zuwa jikinta, ƙara ta saki ta dafe kanta ta faɗi a gurin. Taku uku ya yi, ya ja ya tsaya ya waiwaya ya kalli gurin da Nana ta faɗi. Habu ya kama hannunsa suka yi waje.
Ma'aikatan gurin, su ka zo su ka É—aga Nana, su ka shiga da ita gurin mai magani, su Baba su na biye da su.
Mai maganin ya fito sanye da rigar fatar damisa, sai warki a ƙugunsa idanunsa Jawur tamkar garwashi, baƙi ƙirin da shi.

Da sauri ya ƙarasa kan Nana, tamkar likitan da aka kawowa mara lafiyan da yake buƙatar agajin gaggawa. Ya sunkuya a kanta yana kallonta sai kuma ya ɗago a gigice ya ce "Baushe, maza bi buzayen nan ka dawo da su, wataƙila ga makarin na sa ciwon a nan, maza hanzarta kar su tafi"
Su Baba dai su ka tsaya sororo su na bin sa da kallo.

Nana kuwa tari ta hau yi, tamka ƙirjinta zai buɗe, ganinta ta yi a cikin ƙura, ko tafin hannunta ba ta iya gani saboda yadda ƙurar ta turnuƙe gurin. Bayan wani lokaci ƙurar ta lafa, ta ɗaga kanta ta na kallon gurin, ita kaɗai ƙwal a cikin sahara.
Waige-waige ta hau yi, sai dai babu tsammani ta ga mutum a tsaye a bayanta, sanye da baƙin rawani da shigar fararen kaya na buzaye, hannunsa riƙe da akalar raƙuminsa.
Sai dai duk ƙoƙarin Nana a kan ta gane kamaninsa, abu ya gagara fuskarsa a rufe take da rawani.

Miƙa mata hannunsa yayi, mai ɗauke da dogwayen yatsu. Duk da a tsorace take, ta fara takawa a hankali, har ta ƙarasa gurin da yake, ta miƙa masa nata hannun.
Yana kama hannunta, ta ji an zuba mata ruwa mai matuƙar sanyi a jikinta. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, tare da buɗe idonta.

Su Baba ta gani a zaune tsuuruu, kamar mara gaskiya a hannun hukuma.

"Sannu Nana Asma'u" mai maganin ya yi maganar cikin sakin fuska.

Nana ta tashi zaune, ta koma jikin Baba, tana jin yadda haryanzu jikinta yake a sanyaye.

Mai maganin ya zura mata ido, sannan ya sake murmushi ya ce "Manya gatan wasa, wa ya isa ja da ku, idan ba wawa ba? Tuba nake uban duƙusa" dubawa Nana take ta ga da wa yake.

Ya ci gaba da cewa "Asma'u, ki na ganin wani mutum a mafarki, ku na magana ko?" Nana ta yi shiru ba ta ce komai ba.

"Za ki iya tuna me da me yake ce miki?" Still ta yi shiru ba ta yi magana ba.

Ya sake murmusawa ya ce "Malam, gidanmu wanzamai ne, na kuma yi ƙarfa-ƙarfa a kan farauta, duk da mahaifiyata sun gaji farauta . Na daɗe ina hatsabibanci, har na zo na fara bayar da magani, na daɗe ban ga abin mamaki ba kamar yau. Aljanin da yake ɗawainiya da yarinyarka hadiminta ne, tun zamanin kakaninka ai 'yan bori ne. Kuma tun daga kansu ba a kuma samun haihuwar mai irin tauraronta ba, sai da aka haifeta dan haka dole ya yi mata hidima, ita kuma taƙi yadda shiyasa yake ta azabtar da ita. Duk ba wannan ba yanzun nan aka tafi da wani buzu, shi dama na gaya musu ba ni da maganin larurarsa, sai dai a shigowar ku, na ga wani abin mamaki da na daɗe ban gani ba, ina kyautata zaton wataƙila maganin nasa ciwon na da alaƙa da nata.
Kodayake ba a kan wannan gaɓar muke ba. Yanzu ita Nana Asma'u za ku bar ta a nan, sai bayan kwana goma sha huɗu zaku dawo, aljaninta sai dai ayi sulhu da shi idan aka takura shi, ba ita ba ni kaina zai iya halaka ni."

Kallonsa Nana tayi, gaba É—aya maganganun mutumin nan ko gaske ne, mushiriki ne shi ma, jira take ta ji me su Baba za su ce, ko me za ayi ba za ta yarda a bar ta a gurin nan ba.

Baba ya ce "Mu tafi mu bar ta har mako biyu kuma, itakaÉ—ai?"

Gaddafi ya ce "Ba magani ake mema ba? Ma samu mu huta kwana biyu mu ma, da wannan tamɓelen da take yi ai gara a batta ɗin, Allah ya kaimu makwanni biyun"

Yanayin Baba ya nuna ba haka ya so ba.

Nana ta buɗe baki za ta yi magana, ta ji kamar an saka dutse a maƙogwaronta, tayi tayi amma magana ta gagara.

Ta dage iya ƙarfinta ta miƙe tsaye, amma jiri ya kwashe ta, tana ji tana gani, masu jajayen kayan nan, suka zo suka ɗauke ta, tana fizge-fizge tana komai aka kaita wani ɗaki aka kulle.

Littafin BUZU 1k ne a telegram.
0069685771
Aisha Adam
Stanbic ibtc
Sai shaidar biya
https://wa.me/2348081012143

Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL

YOTA/002

(Bright pens 3rd batch)

P12

Imaran tun yana jiran dawowar su Baba da daɗin rai, har ransa ya gama ɓaci, zuciyar sa ta din ga tafasa.

Mama kuwa tuni ta din ga kiran 'yan uwanta tana gaya musu, abin da ya faru da Suwaiba. Suwaiba kuwa ko a jikinta, sabgoginta kawai take yi. Ƙarshe ma da yamma, ta sha wanka za ta fita zance, ta ga turaren nan a kan kayan Nana, ta ɗauki abin ta ta ƙara fesawa ta fice.

Bayan sallar magariba, Imran yana zaune a waje, sai ga taxi har ƙofar gidansu, su Baba sun dawo.

Bai motsa daga gurin da yake ba, sai da ya ga duk sun fito daga motar, amma babu Nana.

Su na shiga gida, ya tashi ya bi bayansu.

"Wai ina Nanan take? Ya ku ka dawo babu ita?" Daga Baba har Gaddafi babu wanda ya kula shi.

Ransa ya fara ɓaci ya ce "Baba ka yi magana, ina ku kai mini Nana?"

"Tana gidan Atine" ya bashi amsa a gajiye, saboda sun kwaso gajiya.

"To me yasa za a kaita gidan Yaya Atine? Me yasa ba ku dawo da ita gidan nan ba?" Ganin Baba ba zai ba shi cikakken lokacinsa ba, balle ya yi masa bayani, kawai ya fice ya nufi gidan Yaya Atine.

Yaya Atine, ta mimmiƙe tana cin tuwon dare, saboda wahalar da suka sha.
Kamar an jefo Imran ta ji sallamarsa.

Ta amsa masa, ba tare da ya ko gaisheta ba ya ce "Ina Nana?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wace Nanan?"

"Baba ya ce mini tana gidan nan?"

"Kuma saboda rashin É—a'a, ko gaishe ni ba za ka yi ba, ka zo kana tambayata wata Nana, to mun sayar da ita"

Ya ce "Yi haƙuri, a ruɗe nake ne"

Yaya Atine ta ce "Ba wani haƙuri da zan yi, gidan uban wa ka tafi tsawon shekarun nan?"

Duk da ya fara ƙuluwa ya maze ya ce "Kudu na tafi neman kuɗi, tana ina?"

"Kai ban sani ba, ni ba ta gidan nan, ka koma ka tambayi uban naka"

Imran ya kalle ta ya ce "Kamar yaya? Shi fa ya ce mini tana nan"

"A'a tana gidan mai magani, sai nan da mako biyu za aje a taho da ita"

Ashar Imaran ya yi ya ce "Wane irin magani ne, sai an kai mutum a baro shi, to ai ko asibiti ana barin É—an jinya, balle wani shashasha da bai shiga aji ba, aje a ajiye masa yarinya shi ba muharamminta ba".

"To ai ubanka za ka je ka yi wa ba ni ba. Kuma ba fin mu hankali da tunani ka yi ba, gurin akwai ma'aikata mata da suke kula da mata marasa lafiya " Imran ji ya yi kamar ya kifa wa yaya Atine mari, wannan ai ganganci ne da rashin hankali.

Takalmansa ya shura, ya fita daga gidan zuciyarsa kamar ya fashe saboda takaici.

Gida ya koma cikin takaici, sai dai ya tarar Baba baya nan.

Labarin mutuwar malam Auwal ya karaÉ—e ciki da wajen unguwar su Nana, saboda an san shi sosai, saboda ya kan ja salla a masallatai daban-daban.
Ga koyarwar da yake yi a islamiyya, kowa yayi masa shaidar mutumin kirki ne shi. 'yan unguwa suka yi alwashin tsayawa tsayin daka, gurin bibiyar jam'i an tsaro da tabattar da an kama waÉ—anda suka aikata masa haka.

Cike da jimami Nasir ƙanin su Nana yake ta nanata mutuwar malam Auwal, ya ce "Allah sarki Nana, ko ya za ta ji idan aka ce mata malam Auwal ya mutu an kashe shi?" Duk da Baba yana cike da takaicin wasa da hankali da malam Auwal ya yi masa, na ƙin fitowa ya auri Nana, amma hankalinsa ya tashi bayan dawowarsu daga kai Nana gurin mai magani ya samu labarin mutuwar.
Yana tsaka da jimamin mutuwar, ana tattaunawa a masallaci bayan sallar isha'i, Nasiru ya zo ya kira Baba ya ce ana nemansa a gida.

Ko da ya je gida, ya tarar an daddane Suwaiba, tana ta kurma ihun Nana na sha mata jini.

Cikin kuka mama ta ce "Ka gani ko? Kalli halin da Suwaiba take ciki, wallahi an cuce ni ban yafe ba, kuma wallahi ko ka ɗauki mataki ko ni na ɗauka. Dan baƙin bala'i a gaban saurayi ta faɗi tana wannan kururwar fa"
Chapter 22 · 0% Book details