← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 32

Sashe 26

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana ta ce "To kai ya aka yi ka sani, bayan baka nan aka yi?"

Ya kalli Nana bai ce mata komai ba ya tashi ya nufi kan matar. Ya saka Salamatu ta É—ebo ruwan magani, aka bawa matar ta sha.
Ya dunƙule hannunsa ya buɗe tafukansa aska ta fito, ya saka aka buɗe cikin matar, ya din ga yi mata ƙananan tsagu da askar. Wannan karon sanho ne a jikinsa, (jakar magunguna) zabira (Jakar wanzamai ta kayan aski)

A wannan ƙaramar jakar, ya ciro garwashi jawur, ya ɗora a kasko ya zuba wani magani a kai.

Take matar ta hau tari, ya kama cikin ya lailaya ya tattara shi guri guda, sai ga wani jini baƙi ƙirin guda-guda yana fitowa daga cikin.
Sai da jinin ya gama fita, ya tattare guri guda ya zama wani baƙin muzuru. A take cikin ya baje, Sarkin baka ya danƙi muzurun ya jefa a cikin sanhonsa ya ce "Aljani ne yake ta yi mata wannan siddabarun. Salamatu a kaita gurin su 'yar ƙashi ɗaya, a tsumata zuwa jibi a sallame ta" Sai da Nana ta razana da abin da ta gani.

Bayan fitarsu ya kalli Nana ya ce "Idan ki ka kuma ƙaryata ni a gaban mutane, sai na je na ɗaure ki a cikin mahaukatan nan kema"

Nana ta ce "Amma ka ce ƙaisar ba zai kamu ba"

Ya ce "Zai kamu, ban yi niyyar kama shi bane"

Ta sake cewa "Amma ya ake ka ke wannan abubuwan haka? Ta ya ya ka ke sanin abin da baka nan aka yi?"

"'yan aike ne suke gaya mini "

"Aljnu kenan ko? Haramun ne fa hakan shirka kenan"
"Ba shirka ba ne, taimakon al'umma muke yi"

"Wallahi shirka ce, har fa tsafi ka ke yi "

Dariya ya yi ya ce "A ina na yi tsafin?"

"Ga shi nan ina gani kana yi, ya aka yi mage ya fito daga cikin mutum, kuma ya ake yi ka ke tura abubuwa da yawa a cikin 'yar ƙarama jakar nan?"

Sarki ya ce "Aljihuna ne da yawa a cikin jakar"

"To buɗe in gani" ya yi murmushi ya miƙa mata jakar ya ce "Buɗe da kanki" cike da ƙwarin gwiwa ta karɓi jakar, babu fargabar komai ta fara dubawa. Ya zuba mata ido yana dariya.

Sai dai ta zazzage jakar babu komai a ciki.

Ta kalle shi ta ce "Wallahi tsafi ne ina magen da ka saka a ciki ya tafi?" Ita kanta Nana tana mamakin yadda ta daina kewar gida gaba É—aya, take jin kamar ta daÉ—e da sanin sarkin baka.

"Idan kin yadda ki bayar da magani, zan nuna miki yadda nake komai, ki koma gida ki taimaki mutane"

Ta girgiza kai ta ajiye masa jakarsa.

"Ki je ki huta, anjima tare za mu fita farauta da ke, ki je ki yi bacci yanzu"

Ta waro ido ta ce "Da wa za ayi farautar? Amma dai ba ni ba ko?"

"Eh ba ke ba" ya bata amsa

Ta juya da baya da baya, ta fita. Tana zuwa ɗakin da take, ta ga hayaƙi da wani irin ƙauri mara daɗi, cikin abin da bai fi mintuna uku ba, bacci ya kwashe ta.

Da Ƙaisar ta fara tozali, zaune a kan wani dutse a cikin wani rafi, ya miƙe ƙafafuwansa a cikin ruwan masu azabar tsayi kamar itacen dogon yaro.
Duk da ta riga ta saba da ganinsa, ba ta fiye razana dan ta gan shi ba, amma biyo bayan tuna mafarkin da ta yi da shi, a cikin sahara ya sanya ta zura da gudu tana neman hanyar guduwa.

Ta yi gudu mai nisan gaske, ta ga wani gida, kawai ta faÉ—a gidan, tana addu'a a zuciyarta amma ta kasa furta ta, a bakinta.
Sai dai bayan shigarta gidan, ta nemi hanyar fita ta rasa, kofofi kashi kashi a gidan, duk ƙofar da ta bi babu hanya sai dai ta sake dawowa guri ɗaya.

Ta dinga buɗe ƙofofin amma ta rasa hanya.

"Ina za ki ne?" Ya tambayeta bayan ya ajiye wata kwalba, jikinsa sanye da fararen kaya yana É—igar da ruwa.

"Yau kuma tsoro na baki? Ko ba ki yi zaton ganina yanzu ba?"

Kuka Nana ta saka ta ce "Dan Allah ka yi haƙuri, kar ka ƙona ni yau ma, dan Allah"

"Yaushe na ƙona ki?"

Nana ta ce"Ranar da ka zama tsoho ka koma raƙumi, ka yi haƙuri dan Allah"

Ya girgiza kai ya ce "Ba ni bane"

"Wallahi kai ne"

"Ni ban yi wannan tsufan ba ai, ba ni bane"

Cikin kuka ta ce "Kai na gani a sahara, ka zama raƙumi kana feso mini wuta"

Ya sake cewa "Ba ni bane ba, tawagar buzayen da ki ka gani ne lokacin da ku ka shiga gidan. Ni ban yi wannan tsufan ba dudu sheruna nawa ban fi É—ari biyar da goma ba, yaro ne ni"

Galala Nana ta saki baki tana kallonsa, shekara É—ari biyar da goman ne yaro. Tambayoyi ne fal a cikinta amma tana tsoron ta tambaye shi ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Kalli can" ta kalli gurin da ya nuna mata.

Suwaiba ta gani tana ta ihu ana danneta, mama na kuka tana tofa mata addu'a, sai fizge-fizge take yi tana kiran sunan Nana.

Cikin damuwa Nana ta ce "wai me ya sa take kiran sunana, ba fa ni ba ce ba, ni me na yi mata?"

Ya watsa wani abu daga hannunsa a gurin da take ganin su Suwaiba, sai ga wannan bararojin, tana ta zuƙar jinin Suwaiba, sannan jikin Suwaiba na ci gaba da zubar da jini ta huda-hudar nan da jikinta ya yi da ta fesa turare.

Ɗif ta daina ganinsu, ta juyo gurin ƙaisar cikin damuwa, sai dai ba ta yi magana ba.

"Kin san dalilin da ya sa na ƙyale mutumin nan, da ki ke gidansa? Wasu dalilai ne, ki gaya masa har yanzu bai san ni ba, duk hatsabibancinsa akwai sararin da bai isa ya jefe ƙafarsa ba. Na zuba masa ido ne na ga iya gudun ruwansa, amma dole sai na nuna masa iyakarsa, kuma zan gani tsakanin ni da shi waye zai yi maganin wani, kuma wannan abubuwan da yake yi miki akwai wani abu a ransa za ki ce na gaya miki "

"Mene ne a ran nasa?"

"Za ki gani, ya ce yau zai tafi da ke farauta, zai ci gaba da nuna miki magunguna. Zan ga iya ƙarshen hatsabibancinsa"

Nana ta yi sororo tana kallonsa, duk da tana son tambayarsa, amma tana tsoron ya ce ta ba shi umarni ya zama hadiminta.

Ya ce "Wuce ki tafi"

"Ai na rasa ƙofar fita"

"Bi waccan" ya yi maganar yana nuna mata hanya. Tana fita ta ganta a tsaye a ƙofar ɗakin da take tare da sarkin baka. Yana sanye da shigar hargi(irin shigar da maharba suke yi)
Bayansa rataye da kwari da baka.

Ba ta iya musa masa ba, ko jin tsoro ko makamancin haka ba, kawai ta saka kai ta bi shi. Daga shi sai ita yana gaba tana bin sa a baya hannunsa da fitila.
Wata ƙofa suka je, ya ɗaga asabarin ya shiga, Nana ma ta bi bayansa. Suna shiga ƙofar ta gansu a dokar daji.

Sai a lokacin jikin Nana ya hau rawa, tsoro ya kama ta, ta ja da baya ta domin koma amma ta ga babu ƙofar da suka shigo.
Ya kalle ta ya ce "Kar ki tsorata, babu abin da zan yi miki, bari na É—aure dajin"

"Ina ne nan?" Tayi maganar cikin tsoro.

"Dajin igbele ne, na jihar delta"

Ta waro ido cikin kiÉ—ima ta ce "Delta kuma? Daga Kanon mu ka zo delta?"

Sarki ya ce "Eh, wata kububuwa nake son kamawa zan yi magani da dafinta. Daji ne mai haÉ—ari ana tsafi iri iri a dajin, amma da na kama Kububuwar za mu tafi" ya yi maganar yana haÉ—a wuta a gurin, ya zuba wani turare yana kewaye wutar. Ita dai Nana ta yi shiru tana kallonsa.

Sai da ya gama sannan ya yi gaba, ta bi bayansa.

Gurin wani dutse suka nufa, daidai jikin dutsen akwai wani kogo, ya ajiye fitilarsa ya watsa wani abu a bakin kogon. Ya ciro wata raga a cikin sanhonsa ya kafa a gurin. Nana tana tsaye tana kallon ikon Allah.

Ya gama ya ce "Mu je wani dajin na nuna miki wasu abubuwan"

Al'ajabi ya hana Nana magana, suna tafe yana nuna mata wasu tsirran yana gaya mata amfaninsu.

"Kin ga idan ki ka samu kashin giwa, da hauren toronta, wato namijin giwa, da kashin ungulu, ki ka haɗa su da kaucin kuka, da tazargade da garin ganyen kuka, da ganyen magarya arba'in ki haɗa jan miski, a haɗe su guri guda. Idan aka yi hayaƙin su, duk wani ƙaramin shaiɗani sai ya gudu, ke babban ma sai ya sha wahala wallahi, kuma aljani sai dai ya ganki ya bar ki"

Nana ta dube shi ta ce "To ta yaya mutum zai samu wannan abun, duk sai mutum ya yi wannan wahalar? Najasar dabbobi ce za ta hana aljanu shafarsa? Bayan ga azkar da Alqur'ani"

Sarkin baka ya yi murmushi, yana son ƙi faɗin Nana ƙwarin gwiwar ta na burge shi ya ce "Hala ke da Ƙaisar yake tare da ke, ba kya azkar da karatun Alqur'ani"

Cikin damuwa ta ce "Ina yi mana, amma wasu lokutan idan ban yi ba na fi zama lafiya ma, na fara tsorata kar hakan ya sanya imanina ya yi rauni".

Ya yi murmushi ya ce "Magani fa ba ƙarya ba ne ba, kin yarda bature ya baki maganin ciwon kai ki sha ki warke, wannan ba shirka ba ce ko, wannan technology ku ke wa ko?" Sai kuma ta ɗan yi shiru.

Ja ya yi ya tsaya, ita ma ta tsaya, hasken wuta ta hango daga nesa, a hankali suka ƙarasa daf da gurin, suka tsaya, amma su na iya hango komai.
Chapter 26 · 0% Book details