← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 32

Sashe 25

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan sarkin baka ya dunƙule hannunsa, yana buɗewa sai ka ga aska, ya yi siddabarunsa ya shafa kan yaro da askar, sai ka ga ya cika hannunsa da gashin yaro.
Idan ya shafa aska a wuyan jariri, sai dai ya zira hannu a bakin yaro, ya ciro wata tsoka har ya cire belin.
Haka kaciya, sai dai da gashin jariran, da belin, duk a cikin jakar zabirarsa yake zubawa.
Sannan ya kan kama hannun yaran, ya É—aura musu laya, ko ya sanya musu tagulla.

Ya kalli wata mata ya ce "Ahh hajjaju an sauka ashe?"

Ta washe baki ta ce "Wallahi sarki, gobe ma suna"

Ya kalli yaron, da fatarsa duk ta yamutse ya ce "Ke ya aka yi ki ka bari mayya ta kama miki É—a? Tun yana ciki matar da ta aiko miki da kunu, ki ka sha ta kama miki É—a"

Cikin damuwa matar ta ce "Innalillahi wa innalillahi raziƙuna, wallahi sarki ka ga ba ya gaba yaron nan, kullum cikin kuka ba ruwan nono na rasa yacca zan yi ohh ni Sakina, amma Allah ya isa wallahi"

Daga yadda matar ta faɗi Innalillahi, Nana ta ƙara tabattar da jahilci a gurin matar, yadda suke ba wa maganganun sarkin baka ammana ba tare da musu ba har mamaki yake bata. Ya faɗi maganin da za a bata suka yi gaba.

Wani guri suka shiga, shi kuma masu ciwon suga ne, ya yi musu ya jiki suka amsa. Bayan sun gama gaisawa ya kalli masu kula da su, ya ce "Yauwwa, kar a kuskura a karya dokokin da na saka, da sassafe kafin su ci komai a ba su magani, a basu zuma cokali biyu da garin habbatussauda, sai su karya kumallo da ruwan dahuwar yaɗiya mai ɗumi, sannan su ci ganyenta. Da rana a basu faten dankalin turawa da alayyahu, a sake basu zuma da habbatussauda, sai da daddare a ba su gurji da kwaɗon rama, sai a sake ba su magani. Yau maganin cikin ɓawon gyaɗa bibbiyu za a zuba musu a ruwa su sha. Shi ne jadawalin abincin da za a ba su yau" ma'aikatan suka amsa masa da to. Nana kuwa rasa bakin magana ta yi, sai kallon ikon Allah, tamkar likita a asibiti da marasa lafiyar sa.

Sun zagaya sosai da sosai a cikin gidan, sannan suka koma wancan É—akin da suka tarar da shi da farko.

Bayan sun shiga, ya zura hannu a cikin zabirarsa ya din ga zaro gashin jariran nan, da belin da ya din ga cire musu, yana tarawa a cikin wata tasa, sai da ya cikata taf. Ya dubi Salamatu ya ce "Salameme zuba wa Fulani a randarta" Salmatu ta karɓa, ta je ta buɗe randar da bafulatanar nan ta ɗqzu sha wannan baƙin abun ta juye a ciki.

Ya kalli Nana ya ce "Za ki iya tuna daga wani lokaci, ki ka fara ganin uban duƙusa a bacci?"

"Waye hakan?" Nana ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Aljanin da yake zuwar miki"

"Wai ƙaisar?"

Ya yi murmushi ya ce "Shi"

"Ba zan iya tunawa ba" ta bashi amsa.

"Ina kallonsa a tare da ke ɗazu, shi ya yi wannan tsawar mahaukatan nan suka yi shiru, so nake ya bayyana a jikinki mu yi magana da shi, amma yaƙi. Masu ihun nan da ki ka gani, duk masu baƙaƙen aljanu ne masu taurin kai, wanda ko an ba su magani, suke lafawa su dawo daga baya. Nan gurin ɗaure su na yi, nake hukunta su da azaba kala-kala, a matsayin gargaɗi da kashedi. Akwai hayaƙin da ake yi musu safe da yamma an gama hayaƙin muka je, amma ƙaisar ya ƙi bayyana. A duniya aljanun da suke irin sa ba su da yawa". Nana ta yi tsuru tana kallonsa da saurarensa, tare da kallon maganganun sa a matsayin soki burutsu.

"Amma ke me yasa ba zaki yadda ki karɓi abin da yake gadonku ba, ki ka gwammace ya yi ta azabtar da ke?"

Take Nana ta tsuke fuska, ta tsani ta ji an danganta ta harkar bori da gadonsu, kamar wani abin arziki.

"Ni ba zan yi shirka ba"

Sarkin baka ya ce "Ba shirka ba ce ba, bayar da magani, idan bayar da magani shurka ne, Asibiti ma shirka suke yi. Ki amince sai mu haÉ—u mu ci gaba da gudanar da taimakon al'umma"

Ta girgiza kai ta ce "Ni ba zan yi ba ba na so"

"Anya? Ki yi tunani kar ki zo nan gana kina nema ido rufe fa" tayi shiru ba ta yi magana ba.

"Salamatu mayar da ita ɗakinta, a bata abinci, idan tana buƙatar wani abin a bata"

Salamatu ta jinjina kai, daga nan ta jagoranci Nana suka bar É—akin.

****

Zaune take a katafaren falonta, ta hakimce a kan kujera tana amsa waya "Hajiya Sa'a, ya mu ka ji da iftila'in nan da ya tinkaro mu, coustom sun riƙe mana kaya a Abuja?"

"Aikam, mu na nan muna ta up and down, Allah ya sa su sakar mana a kan lokaci"

"Amin ya rabb, wallahi hankalina duk a tashe yake, na haɗa kuɗin mutane da jarina duk na zuba na sayo kayan nan, ni dai fatana Allah ya sa kar su yi condeming ɗin kayan nan wallahi ban san in da zan saka raina ba, ga mutane sun fara ƙorafi"

Hajiya Sa'a ta ce "Ahha haba Sadiya, babu abin da zai faru fa, ki kwantar da hankalinki ki yi addu'a"

"To shikkenan Hajiya, na gode sosai da sosai" bayan sun yi sallama, Hajiya Sa'a ta yi murmushi ta kalli maman khairat ta ce "Safiyya mutuniyarki ce fa, Sadiya"

"Ohh Allah sarki"

"Duk hankalinta a tashe yake, batun kayan da coustom suka riƙe, ni ba ta son ko kaɗan kayan nan ba a gabana suke ba"

Safiyya ta yi dariya ta ce "Haryanzu ita kanta a tukunya yake kenan, ba ta san dawar garin ba?"

"Ina fa ta sani, a zatonta business yake tara mini kuÉ—i, duk wannan abin shige mini take son yi, ta ji sirrina".

"To hajjaju a shigo da ita sabgar mana"

Cikin sauri ta ce "A'a tana da surutu, ga ƙaryar riƙon addini, kin san kuma ƙa'idarmu, muddin aka samu mushikila akwai matsala. Ai zatonta business ɗin nan na riƙe, har take neman yin takar da ni a wasu abubuwan. Ba ta san kare yawa ne kawai ba, da kawar da hankalin mutane".

"Gaskiya ne, sabgar tana buƙatar sirri sosai"

"Safiyya kin ga an sake samun matsala, yarinyar ba ta yi amfani da turaren nan ba, wanda ya yi amfani da shi daban, ya ce wani aljani ne a kan yarinyar hatsabibin gaske ba zai bari komai ya yi tasiri ba. Kuma wallahi ya tabbatar mini idan aka yi amfani da jininta, za a samu alkhairi sosai taurarinta masu haske ne. Kuma idan aka yi wannan aikin ba za a ƙara bamu wani aikin mai wahala ba. Mun riga mun wuce gurin mun samu sa'a, sai da na ce anya ba sato ta zan saka ayi ba?"

"Na shige su ni Safiyya, kuma Jamila ta tabattar mini da ta ba ta turaren har ta na murna"

"Wallahi ba ita ta yi amfani da shi ba, an yi amfani da turaren amma ba ita ba ce ba"

"Kai wannan wace irin jaraba ce? Ga shi kuma wai ba ta nan an kaita gidan mai magani an barota a can" da sauri Hajiya Sa'a ta ce "Haba dai? A ina ne na ji ko da yadda za mu yi mu samu gurin?"

Maman khairat ta ce "Wallahi ban sani ba, sai dai idan ta zo na tambayeta"

"To ki yi mata cikin hikima dan Allah, ki nuna mata wata 'yar uwakki za a kai, kar mu bar wani trace da za a gane wani abu"

"To shikenan hajjaju bari ta zo, it ma ina daf da jawota cikin ƙungiya, za ta yi mana amfani saboda tana da mugun kwaɗayi daga ita har iyayenta"

"Aikuwa nima na gani, yanzu dai a far wannan É—in"

****
Ɓangaren Nana, ta ga abubuwan al'ajabi kala-kala a gidan sarkin baka.
A kwana uku da ta yi, tana iya fita da kanta ta zagaya tana ganin marasa lafiya har ma ta yi magana da su, ta basu shawarar su din ga zuwa asibiti. Tana yawan zuwa ganin Kubra, sai dai yanayin da take tarar da ita a ciki, ba ya yi mata daɗi, saboda wataran da sauƙi wataran kuma hauka take yi tuburan.

Kullum idan Sarkin baka zai zagayen ganin marasa lafiya, da waÉ—anda ake kawo masa su ganshi, tare yake yi da ita.
Aka kawo wata mata da tsohon ciki tana tafiya da ƙyar, cikinta har rinjayarta yake yi, wai shekarar cikin goma a jikinta, wasu lokutan ya tashi, wasu lokutan ya kwanta a neme shi a rasa.

Su na gama yi wa sarkin baka bayani, Nana tayi farat ta ce "Ba ku je asibiti ba?"

"Mun je, duk gwajin da aka yi sai ace babu ciki" babar matar ta ba wa Nana amsa.
Sarkin baka ya bushe da dariya ya ce "Asma'u ma'u, su Asibiti duk abin da suka zo muku da shi, za ku karɓa ku ce technology ne, mu kuma namu da muke yi, shi ne shirka a gurinki. Shi maganin baturen kin san da me da me ake haɗawa? Kin tabattar da ingancin halaccin sa a addinance? Shi fa ilmi siffa ce ta Ubangiji, kuma yana bayar da ita ga wanda ya so, bai keɓantar da baiwarsa ga farar fata ba kawai, ku baƙaƙen fata ne ku ka raina abin da Allah ya baku na ilmi, ku ka yi amanna da bature ne kawai ya iya"

Ya mayar da hankalinsa kan mara lafiyar ya ce  "Hajiya a da idan ki na al'ada ba ruwanki, duk gurin da ki ka samu yarda ƙunzugun jinin ki ke yi. Da ƙunzugun jinin hailarki aka yi miki sihiri, saboda a raba ki da mijinki, idan ba ki manta ba, kin yi ta zubar da jini tun yana taya ki neman magani har ya gaji ya yi aure ya rabu da ke. Da ki ka ce ki na da ciki ma rigima ku ka yi ta yi ya ce ba nasa bane ba" cike da amanna ɗari bisa ɗari suka gazgata sarki.
Chapter 25 · 0% Book details