Sashe 1
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002)
Bright pens 3rd batch.
(2025)
Bismillahirahmanirrahim.
*Labarin BUZU ƙirƙirarren labari ne, duk wani sashi na labarin na iya faruwa a gaske, idan ya yi kamanceceniya da rayuwar wani ko wata arashi ne.*
âš ï¸ Labarin mallakina ne, ban yarda wani ko wata, su yi amfani da shi ta kowace irin siga ba, sai da izina.
AISHA ADAM
(Ayshercool)
08081012143
Arewabooks; Ayshercool7724
Watpad: ayshercool7724
Page 1
Dare malafar rana, kowa ya bika ya shirya maka.
Danƙareriyar mota ce, ƙirar highlander baƙa, take ta kwarara gudu a saman kwalta, tamkar hanyar domin direban kawai aka yi ta.
Gefe da gefen hanyat baki É—aya babu komai, banda yashin sahara, sai busassun bishiyu jefi jefi. Kasancewar dare ne, wata ya kai kwana goma sha huÉ—u, ya haska ko ina, ga taurari sun yi wa sararin samaniyar ado.
Titin ta tsakiyar sahara ya ratsa, wadda yashin saharar ya bayar da sassanyan yanayi.
"Kilomètre nawa ce ta rage mana ne?"
Direban ya waiwayo ya kalli mai maganar wandaa fuskarsa a rufe take cikin rawani ya ce "Bai fi 95 kilomètre ba"
"Dans quelques minutes ?? (Nan da wani lokaci?)".
"Bai fi awa É—aya ya rage ba"
"Dole fa mu ƙarasa dai-dai lokacin da aka umarce mu, ni ina tsoron ma kar ya farka"
Ya yi maganar yana haska fuskar wani matashin mutum, da yake kwance a jikinsa ya haɗa gumi, cikin wani yanayi kamar bacci kamar suma, sai dai yadda yake gumi ya nuna a wahale yake baccin, babu in da yake motsi a jikinsa, sai ƙirjinsa da yake ɗagawa yana sauka lokaci zuwa lokaci, numfashinsa yana fita da ƙyar.
Ya kai hannunsa, ya ɗora a kan ƙirjin matashin, idan zuciyar sa ta buga sau ɗaya, sai ta jima kafin ta sake bugawa. Sai dai duk bugawar da za ta yi, da ƙarfi take bugawa tamkar za ta tsaga ƙirjinsa ta fito dummm!.
Cikin damuwa ya ce "Lowalli, sai ka ƙara gudu fa, kar ya mace mana, bugun zuciyarsa raguwa fa yake yi"
Lauwalli ya jinjina kai yana ƙara gudun motar.
*****
Misalin ƙarfe shida da mintuna goma sha biyar na safiyar ranar asabar, ɗaki ne madaidaici, wanda ya samu kyakkyawan ginin ƙasa ma ƙwarin gaske, duk da kasancewar sa na ƙasa, amma adon da aka yi masa ya bayyanar da darajarsa.
Can daga kusurwar ɗakin wata matashiyar mace ce, kwance a kan matsakaiciyar katifa ta yi ɗaiɗai ta na bacci, zaninta ne kawai ya kare bayyanar tsiraicinta, amma idan ta yi kyakyawan yinƙurin za ta yi tsirara.
Iya ƙarfinta take ƙoƙarin tashi daga baccin, amma abu ya gagara a sakamakon sleep paralysis, wanda a hausance da kuma fahimta ta mutane suke kira da dannau, a cewar mutane wani aljani ne mai suna dannau, yake danne mutum ya kasa motsi, alhali idanunsa biyu, kamar a zahiri haka ta din ga ganin abubuwan da suke faruwa da ita, amma ta kasa motsawa.
Tamkar an cire mata wani abu mai nauyi, haka tayi firgigit ta tashi zaune, ta na mayar da numfashi, a sakamakon fafutukar da ta sha, kafin ta samu ta iya farkawa daga nannauyan baccin da take yi mai kama da na mutuwa.
Ware ido tayi, ganin yadda gari ya yi haske, ba tare da ta gabatar da sallar asuba ba.
Ta yinƙura za ta sauka daga kan katifar, ta ji duk gaɓoɓinta na yi mata ciwo, jikinta kamar wadda aka yi wa dukan tsiya, zanin jikinta ya yaye.
Shiru ta yi ta na ƙoƙarin tuna abin da ya faru a daren jiya, a iya saninta ninkin kaya take yi, ba ta kai ga kwanciya ba, daga nan ba ta san abin da ya faru ba.
Ita dai ta san sanye take cikin suturarta, amma yanayin da take ganinta a ciki, yana sanya mata wasi-wasi.
A hankali ta tashi ta gyara zaman zanin ta nufi banÉ—akin da yake cikin É—akin, domin ta kintsa jikinta ta gabatar da sallar asuba.
*****
Sannu a hankali yake buɗe idanunsa, da suke yi masa wani irin zugi saboda hasken da ya cika masa su, sai ya ji tamkar hasken wani baƙon abu ne a cikin idanun nasa. Yanayin ya yi masa kama da farkawa cikin wata duniya ta daban.
A hankali ya daina jin zugin da idanun suke yi masa, ya buɗe su tanagrau, ya ƙurawa wurin da yake ido, yana ƙoƙarin gano a ina yake.
Wani dogon mutum ne baƙi, fuskarsa ɗauke da jan rawani hannunsa rike da ɗan ƙaramin kofi, ya shigo cikin tantin.
Jifa yayi da kofin hannunsa, ya nufi mutumin da yake kwance da matuƙar hanzari.
Taimaka masa yayi ya tashi zaune, fari ne amma ba tas ba, irin mai sirkin yellown nan, ya na da É—an siririn hanci, dai-dai da siririyar fuskarsa, sai gashin baki kaÉ—an da ya haÉ—e da É—an madaidaicin gemunsa, sai kuma manyan idanuwa da yake da su, da su ka kaÉ—a su ka yi jawur tamkar jini zai kwararo daga cikinsu.
Zaman da ya yi, ya bawa gashin kansa damar kwanciya a kafaÉ—arsa zuwa bayansa, tamakar mace.
A hankali É—ayan ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Sannu ya jikin naka?" Maimakon ya bashi amsa, sai ya yi shiru ya na bin sa da kallo.
"Akwai abin da yake yi maka ciwo ne?"
A hankali ya motsa bakinsa ya ce "Ina ne nan?"
Baƙin ya kalli gurin sannan ya mayar da idonsa kan shi ya ce "Mun shigo Nigeria ne yanzu haka"
"Nigeria?" Ya maimaita.
"Eh Nigeria" ya amsa masa.
Ya yi shiru ya na ƙoƙarin tuna a ina ma ya taɓa jin sunan.
"Ya na ga ka yi shiru ne? Ka gane ni ma kuwa?" Ya É—ago ya kalle shi a hankali ya girgiza masa kai alamar a'a.
"Innalillahi wa innalillahi raji'un, ba ka sanni ba ka ke nufi?" Ya jinjina masa kai.
"To ka san sunanka?"
Yayi shiru yana ƙoƙarin yin tunani, amma ya gaza tuna komai, sai ma wani irin rugugi da ya ji a cikin kansa tamkar an yi aradu, hakan ya tilasta masa dafe kansa yana rintse idanunsa.
"Shi kenan ya isa, ba sai ka tuna ba, amma ka san alwala da salla?"
Ya É—aga masa kai alamar eh, ba tare da ya yi magana ba.
"Sallar asuba raka'a nawa ce?" Ya É—aga masa yatsunsa guda biyu.
"Azahar fa?" Ya nuna masa huÉ—u.
"Ka san salla, amma ba za ka iya tuna komai ba bayan haka?"
"Eh" ya amsa a taƙaice.
"Shikenan, ka zo ka yi alwala sai ka rama sallolin da suke kanka, ka yi ƙasaru, tun da mun yi tafiya mai nisa daga Nijar".
Shiru ya yi ya na son tuna a ina kuma ya taɓa jin sunan Nijar, sai kawai ya bar shi a sunan da ya ji ya faɗa ɗazu ne Nigeria.
Cif ya jera sallolin kamar yadda wanda suke tare da shi, ya gaya masa waÉ—anda su ka tsere masa.
Ya ɗaukko abinci ya bashi, ya saka hannu ya karɓa ya fara ci.
Bayan ya kammala cin abincin, ya tsiyaya masa shayin da ya dafa a cikin ɗan ƙaramin kofi ya miƙa masa.
Ya karɓi shayin ya fara sha, hakan ya sanya shi fara ƙoƙarin tuna wani abu, amma abu ya ci tura. Bayan ya gama shan bunun, ɗayan ya fito da wani ƙyalle ya tattare masa dogon gashinsa, ya naɗe masa shi, sannan ya naɗa masa rawani ya kamo hannunsa su ka fito daga cikin tantin.
Tsayawa yayi, ya yi wa wurin ƙuri da ido, jeji ne babu kowa a wurin, sai bishiyu sai kuma wani raƙumi da yake gefe a ɗaure ya na ta taune-taune.
Ya tafi ya kwanto raƙumin, ya janyo akalarsa zuwa gabansa, ya kalle shi ya ce "Ka san menene wannan?"
Ya jinjina kai.
"Mene ne shi?"
"*Le chameau*" (Camel/ raƙumi ne)
Yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce "Hau mu tafi" ya taimaka masa, ya hau kan raƙumin, shi kuma ya ja akalar raƙumin su ka tafi.
*****
Tafe take sannu a hankali, ta na ratsa matsakaitan gidajen da su ka haɗu suka samar da rukunin gidajen da suka samar da wani ɓangare na unguwar.
Mamakon ruwan saman da aka tafka kamar da bakin ƙwarya awanni kaɗan da suka shuɗe, ya wanko datti da ƙazanta daga mabanbanta wurare, sai dai rashin kyakyawar hanya da magudanan ruwa, ya sanya ruwan shiga gidajen mutane, wani kuma ya kwanta a cikin layuka, ta yadda ba a iya banbance kwata da hanya, duk sun haɗu sun shafe.
Gabanta ne yayi mummunar faÉ—uwa, abin da take tsoro da fargaba ta tarar, tun da hadarin nan ya taso aka fara ruwa, hankalinta ya kasa kwanciya.
Daga in da take ta na hango tsakiyar tsakar gidansu, a sakamakon fiye da rabin katangarsu ta zube.
Ta lallaɓa ta ƙarasa, duk mutanen gidan su na tsaye sun yi cirko-cirko su na jajanta abin da ya faru.
Sai dai abin da ta tarar ya fi wanda ta hanga daga nesa, domin ƙarasawarta gidan ke da wuya, ta tarar rijiyar gidan ta burma, ta haɗe da masai kasancewar daf da juna suke, daga in da aka yi rijiyar babu tazara.
Wani babban mutum ne ya fito daga cikin banÉ—akin, ya dubi matashiyar ya ce "Nana kin dawo?"
Jiki a sanyaye ta amsa ta ce "Eh Baba"
"Kin ga abin da ya faru ko"
Nana ta ce "Eh baba, tun ina makaranta da aka fara ruwan nan, hankalina yake tashe nake a tsorace"
"Ai mu na cikin jarrabawa, yanzu lalubawa zaki yi, É—an abin da aka samu a hannunki, ki kawo a samu ko katangar a fara tayarwa".
Saroro Nana ta yi baki buɗe tana bin Baba da kallo, duk da ba abin mamaki bane ba, jin hakan daga bakinsa, cikin ƙarfin hali ta ce "Baba dubu bakwai ne fa albashin nawa, kuma yau goma sha ɗaya ga wata, ko sisi ba ni da ita ka manta dubu biyar ka karɓa ka bani dubu biyu"
"Kai Nana, ina ki ke kai kuɗi ne? kullum da an taɓa ki babu, ai shikenan sai ku zauna haka, duk wanda ya ji turotso sai ku bi maƙwabta ko ku tafi jeji ku yi, ni ba ni da yadda zan yi"