Sashe 20
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imran ya ce "Baba neman kan da ka ke yi da Nana ba daidai ba ne ba, Allah ya É—ora mata larura alhakinka ne nema mata magani, ba neman kai da ita ba, amma shikenan 'yar ka ce, duk matakin da ka É—auka a kanta daidai ne" yayi maganar yana barin gurin.
Baba ya kalli Saleh ya ce "Dan Allah malam Saleh ka yi haƙuri, yaron nan ba cikakken saiti ne da shi ba, ka san idan mutum yana shaye-shaye sai a hankali ka yi haƙuri. Nana 'ya ta ce kuma na isa da ita, ka je ka turo magabatanka kawai kar ka ɓata lokaci kamar yadda wancan yayi"
Saleh ya ce "In sha Allah Baba na gode sosai"
"Yauwwa yi tafiyarka, kar ya zo ya yi maka wani haukan a ka" Saleh ya so keɓewa da Nana, amma Imran ya wargaza komai.
An fara kiraye-kirayen sallar magariba, Jamila ta shigo Nana ta fara nema, Nana ta ce "Wannan kiran fa ta samu ne?"
"Wai dan Allah ina kayan da Hajiya ta bani na kawo miki, ko sau É—aya ba ki saka ba, balle na yi miki hoto na tura mata, tun da na san ba za ki je ta gani ba"
Nana ta ce "Zan saka ne, kawai ni ban san dalilin da ya sanya ta bani kayan ba ne, amma zan saka in sha Allah"
Jamila ta ce 'Ai mace ce mai kyauta, babbar 'yar kasuwa ce fa, kwanan za ta fara bani kaya ina ɗora nawa nima, kin ga turare ta bani na kawo miki " ta yi maganar tana miƙa wa Nana wani turare.
Nana ta karɓa tana murmushi, kasancewar tana son ƙamshi sosai. Ta sunsuna turaren ta kalli Jamila cikin murmushi ta ce "Amma ƙamshin turaren nan yayi daɗi sosai, ki ce mata na gode sosai"
Nana ta fara ƙoƙarin fesa turaren a hannunta, amma idan ta fesa babu abin da yake fitowa, ga kuma turaren tana gani cikin kwalba. Tayi tayi amma abu ya gagara.
Suwaiba da ta fito daga banÉ—ki ta ce "Wai ke Jamila ba ki gaya wa hajiyar, ki na da 'yar uwa da ku ke uwa É—aya uba É—aya ba, ni ba zata bayar da komai a kawo mini ba sai wata Nana da uba kawai ku ka haÉ—a?"
Suwaiba ta ƙaraso, ta karɓi turaren hannun Nana, ta fesa a hannunta ta sunsuna.
Wurin da ta fesa turaren Nana ta ga duk ya ɓuɓɓule, kamar an caccaka allura jini ya fara fitowa. Sai dai ta ga Suwaiba normal, ba ta nuna wata alama na ta ga abin da ya faru ba, hakan ya tabattar wa Nana, ita kaɗai take gani.
Suwaiba cike da mugunta, ta feshe rigar material ɗin jikinta milk. Nana ta ɗan ja da baya ganin jini, ya ɓata rigar maimakon ruwan turare.
Suwaiba kuma ta ce "Amma turaren yayi ƙamshi" tana sake feshe jikinta da shi. Sai dai duk in da turaren ya taɓa a fatarta ɓulewa yake jini ya fara zubowa.
Ta gama fesawa, ta bawa Nana turaren ta ci gaba da sabgoginta.
Mama ma masifa ta hau yi, wai tana uwar Jamila ba a bayar da komai a kawo mata ba sai wata Nana.
Jiki a sanyaye Nana ta shiga ɗakinsu, tana sake kallon kwalbar turaren. Ta buɗe ta ƙara fesawa a jikinta da hannunta, amma yaƙi fitowa.
Ta ajiye turaren tana tunanin ko sharrin ƙaisar ne.
Ta sake fitowa yin alwala, Baba ya zaunar da Gaddafi yana ta gaya masa abin da Imran yayi, tare da ƙorafin ya gaji da rashin mutuncin da yake aikatawa.
Nana hankalinta ba ya kan abin da suke faÉ—a, hankalinta yana kan Suwaiba, da jini yake ta gangarowa daga hudar jikinta, kuma rigar jikinta ta rine zuwa jini. Amma normal suwaiba na ta ayyukanta.
Nana ta ware a gefe, tana ta jan "wa hifzan min kulli shaiÉ—anin marid"
Sam jikin Nana ba ƙwari ta kwanta, duk addu'a da ta zo bakinta yi take yi, ta waiwaya ta kalli in da Suwaiba take, ta jiƙe jagab da jini ga ƙarnin jinin ya cika ɗakin babu daɗin ji.
Suwaiba na ta kallon kaɗe-kaɗenta a waya, har bacci ya kwashe ta. Nana ko kyakyawan ƙifta ido ta kasa yi, ganin yadda jinin ya jiƙa katifar da Jamila da Suwaiba su ke kai, ya gangaro ƙasa.
Ana haka Suwaiba ta kurma wani irin uban ihu, Nana ta razana, ganin wannan bararojin da ta ba ta magani ta lasa, jikinta baƙi ƙirin ta koma kamar gawayi, fuskarta ce kawai ba a ƙone ba sai gashinta, ta tsaya a kan Suwaiba ta kafa haƙoranta a wuyan Suwaiba tana zuƙar jini. Maimakon Nana ta yi addu'a kawai ita ma sai ta saka ihu ta suma a gurin.
Cikin ihu da kururuwa Suwaiba ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Mama Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, Nana tana shan jinina dan Allah ku yi mini rai Nana na shan jinina!!!
Ku tuntuɓe ni kai tsaye, domin fara biyan naku kuɗin littafin.
https://wa.me/2348081012143
Ayshercool
08081012143
Ko kuma ku kasance da ni a kan manhajar arewabooks @ayshercool7724
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002
P11
ÆŠungurungum, page É—in yau naku ne, YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION, Tare da 'yan Ayshercool media, ina godiya sosai da sosai.
A wannan karon Mama ce ta fito da gudu, jin muryar Suwaiba tana ihu.
Sai dai ta tarar da Nana a gefe, tana bacci.
Ta ɗago Suwaiba tana kiran sunanta, sai dai Suwaiba ta rirriƙe wuyanta, tana numfashi da ƙyar tana cewa "Nana ce, Mama ki taimake ni za ta kashe ni"
Cikin kuka maman ta fara ƙwalawa Baba kira "Malam Isa ka zo Nana za ta kashe mini 'ya, na daɗe ina faragbar kar ta cutar mini da yara, gashi za ta kashe Suwaiba"
Jamila ma tuni ta tashi, ta ja gefe, domin ita ma a tsorace ta tashi, saboda mummunan mafarkin da ta yi da Hajiya sa'a tana ƙoƙarin shaƙe ta, ta caka mata wata wuƙa.
Baba ya ce "Wani irin Nana za ta kashe ta kuma? Ba ga Nanan a gefe tana bacci ba?"
Cikin fushi da tsawa ta ce "To ka ƙaraso mana ka ga abin da take yi"
Ya ƙarasa ya ga Suwaiba, ta rirriƙe wuyanta, idanunta duk sun fito waje sai kakari take, da ƙyar take furta Nana za ta kasheta.
Baba ya ce "Suwaiban Baba, buÉ—e ido ki ganni, Nana bacci take yi me ki ke gani?"
Cikin kuka da kakari Ta ce "Baba wallahi Nana ce, jinina take sha, ka hana ta zan mutu"
Baba ya koma gurin da Nana take, ya kai hannunsa ya juyota, idanunta a buɗe, amma babu baƙar ƙwayar idonta, sai farar kawai. Jikinta kuma sanyi ƙalau kamar gawa.
"Ni wannan wane irin abu ne haka?"
"Ke Jamila, je ki ki taso mini Gaddafi" Jamila ta tashi jiki a sanyaye ta fita ƙofar gida, ta ƙwanƙwasa wa Gaddafi ɗaki.
Tare suka dawo, yana tsaki yana bala'in shi tattarawa zai yi ya koma in da ya fito, ya gaji da wannan bala'in na gidan.
Ɗan tsayawa yayi yana kallon in da Nana take, ga gefe Mama riƙe da Suwaiba tana kuka.
Ya ce "Mutuwa Nanan tayi ne na ganta a haka?"
Cikin kuka Suwaiba take miƙa wa Gaddafi hannu ta ce "Yaya ka taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take sha" tayi maganar tana kuka.
"Wane irin shan jini kuma?"
Nana kuwa tuni ta lula wata duniyar a yanayin da take ciki.
Domin kuwa Ƙaisar take gani. Ya ce "Kin ga da kin sake kin fesa turaren nan a jikinki, da jininki za a sha ba nata ba. Aike ne na musamman domin ke, da na bari kin fesa turaren nan da sai dai wata ba ke ba"
Nana ta kalle shi ta ce "To ni me za ayi da jinina? Kuma meyasa ba ka hana wannan mummunar matar shan jinin Suwaiba ba?"
Ya tanƙwashe ƙafafuwansa ya kaɗa kai ya ce "Saboda ke ce uwar gijiyata, alhakin kula da ke ne kawai a kaina. Duk da ba jininta suke buƙata ba, amma idan 'yar aiken ta ji daɗin jinin na ta, to fa ta samu wurin zama. Ko da su can jinin bai yi musu amfani ba, to ita za ta ci gaba da amfani da jininta, domin ta warke daga ciwon jikinta, idan ba ayi wasa ba hakan zai yi ajalinta."
Cikin damuwa Nana ta ce "To ka yi wani abu a kai mana"
Yayi murmushi ya ce "Zan iya wani abu a kai tabbas, amma daga lokacin da ki ka fara bani umarni hakan yana nufin kin karɓi gadon gidanku. Kuma zamu yi aiki tare"
Da hanzari ta ce "A'a ni ba zan iya shirka ba na gaya maka. Amma ba zan zuba ido komai ya tafi a haka ba. Idan haka ne anya ba wannan matar Hajiya sa'a da ta kawo turaren babu masaniyarta a kan wannan abun?"
Murmushi ya yi ya shafi gefen fuskar Nana ya ce "Ban sani ba, amma ke ma zan shafe komai daga kanki yanzu wani binciken ba shi da amfani sam. Mussaman ke da ba za ki yi abin da ya dace ba, idan ki na tsananta bincike wataran za ki shiga gurin da ba zan iya ciro ki ba.
Kalli nan ki ga, ta waiwaya domin ganin abin da yake nuna mata.
ÆŠakinsu ta gani, Suwaiba ta samu bacci, Jamila kuma ta ce Allah kar ta, ba zata kwana a É—akin nan ba tsoro take ji.
Mama ta ce su tarkata su koma É—akinta, su kwana tare da yaranta a bar Nana ta ci kanta.
Baba ya kalli Gaddafi ya ce "Gaddafi, gobe in Allah ya kaimu dole mu yi sammako, mu kai yarinyar nan gurin da ka faÉ—a É—in nan. Ni kaina na fara jin tsoron abubuwan nan".
Gaddafi ya ce "Allah ya kaimu"
Nana ta dubi Ƙaisar ta ce "Ni dama gurin mamana ka nuno mini, na ganta ko na ji daɗi"
"Idan na fara karbar umarninki, haka yana nufin kin amince da sharaÉ—ina, ni kuma zan yi miki mubaya'a na zama mai hidima a gare ki"
"A'a bari ba na so" tayi maganar tana girgiza kai.