Sashe 27
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mutane ne tsirara sai ɗaurin ƙyalle ja a ƙugunsu, maza da mata su na kewaye wuta kowa da ɗan ƙoƙo a hannunsa.
Wani mutum a tsakiya yana ta karanta wasu abubuwa, gefe wata mata a kwance ba ta ko motsi da tsohon ciki a jikinta. Ta ga mutumin nan ya nufi kan matar da wata wuƙa a hannunsa yana karanto wasu abubuwan.
Razana ta yi, za ta ƙwala ihu sai kuma ta daina ganinsu, ta ga sun koma dajin da sarkin baka ya yi wa kububuwa tarko.
"Idan muka tsaya, ki ka ci gaba da gani, za ki iya rasa hankalinki"
Jikin Nana na tsuma ta ce "Su suka kashe matar?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh, jaririn cikinta za su cire, jininsa za su sha, ƴan ƙungiyar asiri ne. Nan da ki ka gansu manyan mutane ne, da suka sadaukar da lahirar su domin duniya. Akwai 'yan kasuwa a cikin su, da 'yan siyasa"
Jikin Nana sai tsuma yake yi, ba ta taɓa tunanin da gaske akwai ƙungiyar asiri ba, ta zata shaci faɗi ne kawai ake faɗa.
"Bari mu koma ki kwanta, da asuba zan dawo na kama macijiyar nan, naga duk a tsorace ki ke . Sai dai ina son mu yi wata magana da ke".
Jiki a sanyaye ta ce "Wace irin magana ce?"
"Ina son ki sadaukar mini da uban duƙusa wato ƙaisar, na din ga aiki da shi!"
Littafin nan 1k ne a telegram ta wannan account É—in
0069685771
Aisha Adam
Stanbic ibtc
Sai shaidar biya ta
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA/002
P14
Cikin hanzari Nana ta ce "Na yarda na amince, na bar maka shi"
"Ai ba da baki kawai za ki faɗa ba, akwai buƙatar yin wani aiki, idan kin amince za ki sadaukar mini da shi, za ku rabu har abada"
"Eh na amince"
Sarkin baka ya ce "Za mu ƙarasa maganar da safe"
Kawai ta gansu a ƙofar ɗakinta, suka yi sallama ta shiga ta kwanta. Sai dai jikinta na ta tsuma da tunanin wace matar aka kashe, kuma ake ƙoƙarin cin zarafin gawarta haka.
"Hmmm za ki sadaukar wa wani ni ko? Har kin yi sabo da shi haka kin yarda shi?" Ta ji maganar ƙaisar a tsakanin zuciyarta da ƙwaƙwalwarta.
"Eh zan sadaukar da kai, muddin hakan zai sama mini lafiya da nutsuwa" ta yi maganar a fili. Dariyarsa kawai ta din ga ji, gidan baki É—aya yana amsa kuwwa.
Bayan ta yi sallar asuba, ta zauna tana azkar bayan ta idar, ta yi shiru tana tunani, addu'a ta din ga yi Allah ya rabata da ƙaisar, muddin abin da sarkin baka zai sakata bai saɓa wa Allah ba, za ta yi domin ta rabu da ƙaisar.
Da kanta take zuwa gurin Sarkin baka yanzu, duk ta san hanyoyi a gidan.
Kuma ganin ta samu sassauci daga takurar ƙaisar, da sanya mata cututtuka da sauran damuwowi ga abinci tana samu babu mai takura mata da damuwa, ga kuma sukulle da kyautatawar da sarkin baka yake yi mata, sai ta fara sakin jiki da mantawa da damuwar da take ciki.
Abin mamaki, yau da Alqur'ani ta tarar da sarkin baka, bugun warshi yana karantawa, sai da ya idar sannan suka gaisa suka fita.
Sai da suka fara zuwa gurin da ake harhaɗa masa magunguna, har da injin niƙa a gurin, shi ma ma'aikatan gurin daban, ga tarin saiwoyi da tsirrai.
Gaggaisawa ya yi da masu aikin gurin, ya ce "An kawo saiwoyin nan kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Salamatu.
Salamatu ta ce "A'a sarki, ta rafi ake jira, ba ta kawo ba"
"Aljanar nan akwai sheÉ—ainiya, idan ta bari na nemo wani ya É—ebo mini, wallahi sai ta É—anÉ—an kuÉ—arta" Nana ta kalle shi ta ce "Aljana kuma?"
"Eh, wasu saiwoyin ai sai dai aljani ya É—ebo, ba dai mutum ba. Akwai abubuwan da a cikin ruwa muke É—ebo su, kuma akwai dai-dai lokacin da muke É—ibar su, idan ba aljani ba sai dai ka nemi masunta, su kuma idan ba su ga dama ba, ba za su baka ainihin abin mai kyau ba" Yana gama yi wa Nana bayani, ya ci gaba da maganar sa.
"Akwai masu shanyewar ɓarin jiki, mutum biyu Salamatu a je a duba, idan na aljanu ne, a jira ni ki ba su taimakon gaggawa. Idan kuma na larura ne maza a haɗa musu magani, a ɗauki ɓawon kwakwa, da sassaƙen zogale, da zoɓo da ɓawon abarba, a dafa su sosai, a ƙara ruwa, a din ga basu kofi ɗaya sau uku rana. Ba cin man gyaɗa, ba cin gishiri ba cin kanwa, uzairu ya yi musu ƙaho zan zo na ga jikin nasu" cikin girmamawa ta ce "To sarki"
Tun Nana tana mamakin al'amuran sarkin baka, har ta zuba wa sarautar Allah ido kawai
Amma duk da haka, Nana ta kan kasa jurewa sai ta tambayi wasu abubuwan, yanzun ma É—an gyaran murya ta yi ta ce "Sarki, su wannan magungunan da ka ke bayarwa haka da ka, ba ka tunanin ya yi wa mara lafiya illa, a asibiti akwai maganin da idan mutum yana da wani ciwon fa ba a ba shi, ku kuma nan ba tantancewa ku ke yi ba, kuma ba auna maganin ku ke yi ba"
Ya gyara zaman sanhonsa ya ce "Ban da sharri irin naki, da kuma abu irin naku na 'yan boko aƙida, da ku ke cewa maganin hausa ba shi da awo, ba yanzu a kunnen ki na faɗi gwargwadon abin da za a ba su ba? Wanda ya sani fa ya sani Asma'u, wanda bai sani ba bai sani ba, galibi gurin masu neman na Abinci kawai ake zuwa, wani koya ya yi amma ba a koya masa maganin yadda yake ba, dan ba kowa ne yake yarda ya bayar da sirrin sa ba. Ni na gada kuma na koya. Bature ya yi nasa ban raina masa ba, kuma nima na yi nawa ba wanda ya isa ya raina mini. Ke shaida ce duk abin da ba ni da maganinsa ina gaya wa mutane. Kuma ni ba dan neman kuɗi nake bayar da magani ba. Ki din ga tambayata abin da ba ki gane ba zan yi miki bayani, amma muddin na ji kushen abin da nake yi, ba zan ba ki amsa ba, kuma kin yi wa kanki, dan ba ki san a ina abubuwan da ki ka koya a gurina, za su iya amfanar ki ba, ko su amfani wani ba" jin sa kawai Nana take yi, tana ganin me za ta amfani wani da wannan abubuwan da babu scientific proof ko research a kan su.
Bayan sun gama da nan suka tafi ɓangaren da ba ta taɓa zuwa ba a gidan.
Shi kuma garke garke ne na dabbobin dawa da na gida, wani abin ma ba ta taɓa ganinsa ba.
Ya din ga nuna mata dabbobin, da magungunan da ake yi da wasu sassa na jikinsu.
Yana cikin yi mata bayani, ta ga ya yi shiru ya daina magana, ta leƙa fuskarsa za ta yi magana kawai ta ga ƙwayar idonsa ta koma baƙa gaba ɗaya, jikinsa ya hau tsuma.
Cikin sanhonsa ya zira hannu, sai ga shi ya fito da wani shirgegen zaka, ya gaji da riƙa cerarsa jawur da ita.
Jiki na tsuma Sarkin baka ya saka hannu ya raba kan zakaran da gangar jikinsa.
Ya É—aga gangar jikin, ya tsiyaye jinin a bakinsa, ya gama ya hau cin gangar jikin zakaran a É—anyensa da gashinsa da komai yana zazzaro ido.
Ihu Nana ta saka tana karkarwa, ta juya za ta kasa da gudu, kawai ta ganta a jikin Salamatu tana shafa mata wani abu.
Nana ta juya ta ga ba ta ga Sarkin baka ba, sai ita da Salamatu a É—akin.
Salamatu ta ce "Nana zamanki a gidan nan, ya ci ace kin daina tsorata a mafarki, ki koyi dakiya garin tsoron nan wataran za ki iya zaucewa fa. Shi ya sa Sarki yake nuna miki wasu abubuwan domin ki saba ki rage tsoro"
Ajiyar zuciya kawai Nana take yi, cike da tsoron abin da ta gani da ta kasa tuna mafarki ne ko kuma gaske.
***
Gaddafi na zaune a rumfar mai shayi, yana jiran a dafa masa noodles da ƙwai ya ci.
Babu tsammani sai ga jami'an tsaro sun dira a gurin, tare da Imran.
Imran ya nuna Gaddafi aka kama shi, cikin mamaki Gaddafi yake tambayar ba'asin abin da ya faru, amma ba su gaya masa ba suka tafi da shi.
Sai da su ka je charge office, sannan aka ce Imran ya faɗi abin da ya kawo ƙarar Gaddafi a kai.
Imran ya ce "Yallaɓai, ƙanwata ya ɗauka suka haɗa kai da yayar babanmu, aka kai ta wani guri wai neman magani. Kusan sati guda kenan na yi na yi, su gaya mini ina suka kai ta sun ƙi, kuma ita kaɗai aka baro a gurin babu ɗan jinya".
Cikin mamaki da takaici Gaddafi ya ce "Amma ka cika mara mutunci, me ya hana ka saka a kama da Baban, sai ni zaka saka a kama, bayan tare muka kai ta".
Imran ya ce "Eh wannan ai ubana ne, kuma Kai ka kawo shawarar a kai ta can ɗin. Ga Suwaiba nan a gidan tana aljanun ita ma, ita baku kaita ba, saboda ita ana son ta ƙanwata ce ba a so, kawai ka gaya mini ina aka kai mini ƙanwa"
D.P.O ya ce "Ya isa haka, wannan maganar ta cikin gida ce, kuma shi ma yana da gaskiya, babu yadda za ayi ace an kai mutum gurin mai magani, babu wani nasa a gurin, kuma ba asibiti ba. Ko Asibiti ne?" Ya yi maganar yana kallon Gaddafi.
Gaddafi ya girgiza kai.