← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 32

Sashe 2

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata mata da tun da su ka fara maganar ba ta yi magana ba, sai yanzu, ta kada baki ta ce "Ai kuwa sai ka san yadda za ka yi, haka zamu dauwwama mu na gantalin yawon kashi a maƙwabta kai ko kunya ma ba ka ji, Nana ka tsare ka na ta baka kuɗin da zaka ɗaga katangar gidanka, kai fa take miƙawa albashin nata, dubu bakwan nawa take, ka bi ka kashe zuciyarka, wallahi dole ka nemi yadda za ka yi"

Nana dai ba ta sake cewa komai ba, ta nufi hanyar wurin kwananta, ta na jiyo ɗaya daga cikin yaran gidan ya na cewa "Abu mai sauƙi, a samu ƙaton bokiti kawai, kowa ya din ga juyewa a ciki, a tara a sayar zazzafan taki ne fa, tsaf za a samu kuɗin ɗaga katangar gidan nan, gwargwadon ƙwazonmu wurin tarawa da yawa gwargwadon.....

"Za ka rufe mini baki, ko sai na daka ka a wurin nan, shashasha mara tunani kawai"

Baba kuwa waje ya yi, saboda tijarar da mama ta fara yi masa, maƙwabta duk sun fito waje, ana jajanta ɓarnar da ruwan yayi a layin, tare da jajantawa su Baba abin da ya faru da su.

Jiki a sanyaye ta shiga wani É—an madaidaicin É—aki, bakinta É—auke da sallama.

'yan mata biyu ne a kwance su na danna waya, da ƙyar ɗaya ta amsa, ɗayar kuwa ko ɗagowa ba ta yi ba.

Nana ta ajiye jakar hannunta tare da faÉ—in "Jamila, ashe ruwa ne yayi mana gyara haka?"

Jamila ta ce "Aikam, ɓarna ma ba ƙarama ba, kin ganni nan lissafi nake yi yadda zan tsallake na bar gidan nan, wannan abin kunya da mai yayi kama, ace in da zaka tsuguna ka juye najasarka babu, sai dai ka bi maƙwabta, wannan gidan Allah kaɗai ya san lokacin da za a gyara shi".

Nana ta nemi wuri ta zauna ta ce "Idan kin bar gidan nan, ina za ki je?"

Cike da takaici Jamila ta ce "Ko ma ina ne, tun kan jarabar talauci ta kashe mutum, kullum gida babu cigaba ba a É—auki É—awainiyarka ba, amma ana nema a wurinka"

Nana ta girgiza kai ta ce "To, Allah ya sa mu dace, ya bamu mafita".

"Amin, kalli wurin kwanciyar ki ma duk ya jiƙe, nan wurin ma zuba yake yi".

Nana ta kalli wurin tare da yin ajiyar zuciya, ba tare da ta ce komai ba.

Haka gidan su Nana suka kwana, rabin katanga a zube, kowa ya zo wucewa ya na kallon cikin gidan.

Washegari da asuba da 'yan kame-kame su ka kama ruwa, wasu su ka zagaya maƙwabta wasu kuma suka yi a wani wurin, su ka yi alwala su ka gabatar da sallar asuba.

Tun daren da abin ya faru maƙwabta suke shigowa yi musu jajen abin da ya faru.

Jamila sai masifa take yi tana mita, "Wallahi na san ikon Allah ne kawai zai sanya a gyara katangar nan, haka zamu ci gaba da zama da zubabbiyar katanga, ni matsalar banÉ—akin nan ba ta dame ni ba sama da katangar nan, duk asirinmu a tone, kodayake wane asiri ne ma da mu, banda damin talauci da tsiya"

Nana ta na jin ta ba ta ce uffan ba, ta É—aukki Alqur'aninta tana dubawa.

*****

Tsura masa ido yayi, yana nazarinsa, sannu a hankali yake cin abincin gabansa, ya gama ya wanke hannunsa, ya gyara zaman rawaninsa ya rufe fuskarsa.

Habu ya dube shi ya ce "Ka ƙoshi?" Ya jinjina masa kai alamar eh.

"Yanzu za ka iya tuna sunanka?" Ya girgiza kai alamar a'a.

Habu yayi ajiyar zuciya yana sake jinjina lamarin, ya sake kallonsa ya ce "Babu abin da yake iya zuwa kanka ka tuna?"

"Eh" ya faɗa a taƙaice.

"Shikenan, kar ka matsawa kanka sai ka tuna wani abu, amma a duk lokacin da ka tuna wani abu ka sanar mini, dole in fara tunanin nema maka magani kafin yin komai, amma sai mun samu wurin masu amana" shi dai yayi shiru bai ce masa komai ba.

Ya saka hannu a aljihun babbar rigarsa, ya É—aukko waya, ya duba wata lamba, ya kara wayar a kunnensa.

Mintuna kaɗan ya amsa sallamar sannan ya ɗora da cewa "Mun iso Nigeria tun jiya, yanzu mene ne abu na gaba?" Ya ɗan yi shiru tsawon wasu mintuna sannan ya ce  "Ka tabbatar babu matsala? Ba na son azo a samu matsala, dole ayi taka tsantsan da lamarin nan, kafin mu san ma in da za mu nufa neman maganin" ya sake yin shiru sannan ya ce "Shikenan, ina sauraronka" har ya kammala wayar bin sa yake yi da ido, kamar zai yi magana amma bai ce komai ba.

*****
Kwanaki uku suka shuɗe ana tsilla-tsillar makewayi a gidan Malam Isa, wato gidansu Nana, ƙarshe katanga sai buhu aka saka aka rufe ta.

Cikin ikon Allah, maƙwabta su ka yi ta kawo masa gudunmuwa, sai dai idan kuɗi ne sai ya karɓa ya saye abin sa, tun da matarsa rabi ta fuskanci haka, ta sanya shi a gaba da tijara, da masifar ya fito da kuɗi a san abin yi.

Nana ta na É—aki tana shafa mai, amma hankalinta yana kan su Baba sa suke ta faÉ—a.

"Amma rabi da kuÉ—aÉ—en gudunmuwar nan, nake ta baku kuÉ—in cefane, kuÉ—in nan fa ba isa za su yi ba ayi aikin katangar nan"

Ta hayyaƙo masa cikin ɗaga murya ta ce "Wane cefanen, ba wata tsiyar ka bamu ba, makewayi ya gagari mutum, kamar mun fi kowa talauci a tsukin nan"

Nannauyar ajiyar zuciya Nana ta yi, ta tashi ta ƙarasa shirinta, ko sallama ba ta yi wa su Baba ba ta fice, dan wannan rashin girmamawar da suke yi wa juna ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba.

Kamar yadda ta saba, tana ƙule a gefe guda, tana dudduba cikin Alqur'ani, yayin sa sauran 'yan ajin suke ta tilawarsu daban.

A hankali ta fara jin jikinta yana wani irin sanyi, ta fara jin tamkar daga wata duniyar take jiyo karatun 'yan ajin nasu.

"Nana" ta ji muryar Amira ƙawarta.

Tayi jarumta ta É—aga kai ta kalleta, Amira ta zauna a kusa da ita ta ce "Na biya miki makaranta, ashe abin da ya faru kenan, Allah ya mayar da alkhairi ya tsare gaba, na tarar da baba yana ta faÉ—a, wai kowa ya nemi in da zai tafi kafin Allah ya hore masa abin da zai gyara gidan"

Sai Nana tayi da gaske take fahimtar me Amira take faɗa, ganin yadda Nana ta ƙura mata idanu ko ƙiftawa ba ta yi, ya sanya ta ɗan matsa baya kaɗan ta ce "Nana lafiya kuwa? Ko baki da lafiya ne?"

Ta girgiza mata kai, ba tare da ta ce komai ba. Amira ta koma gefe ta É—aukko Alqur'aninta, ta koma nesa da Nana.
kamar wadda ake zarewa laka, take ji, wani irin sanyi jikinta yayi zuciyarta ta din ga bugawa cikin matsanancin tsoro da fargaba, numfashinta ya dinga sama-sama kamar zai bar gangar jikinta, ji tayi kamar ta kurma ihu, sai dai jikinta babu wannan ƙwarin, ji take kamar ajalinta ne ya risketa.
Alqur'anin gabanta take kallo, zuciyarta ta din ga raya mata, ta yi jifa da shi.
Ganin yadda yanayinta ya sauya, ya sanya 'yan ajijsu darewa suka koma gefe daga kusa da ita.

Malam Auwallu ne ya shigo, 'yan ajin duk suka yi shiru, hankalinsa ne ya sauka a kan Nana, da take ta fizgar numfashi idanunta sun yi jawur.

Girgiza kai ya yi ya ce "Nana Asma'u" kamar wadda aka jonawa shocking, haka ta ja da baya a razane, tare da sunkuyar da kanta.

Ya janyo kujerarsa zuwa gabanta, ya ce "Yau haddar ki zan fara ji, matso ki karanto mini, kin san ina son ƙira'arki" ba ta yi magana ba ta ci gaba da sunkuyar da kai tana haki.

Ya kalli ta kusa da ita ya ce "Amira dawo nan gefe ki fara ke"

Cikin damuwa Amira ta tashi, tana kallon Nana cike da tausayawa, hatta 'yan ajin kallon Nana suke yi cike da tsoro, su na jiran kyat su falla da gudu su na iface-iface.

Amira na zama a gaban malam Auwal ta fara karatu, a haka ya ci gaba da sauran karatun ɗaliban ɗaya bayan ɗaya. Nana tana gefe a zaune tana ta gursheƙen kukan da ita kanta ba ta san dalilin sa ba, adadin yadda suke karatun ya ingiza bugun zuciyarta, tare da jin jikinta na ci gaba da yin sanyi.

Malam Auwal na fita amsa waya, Nana Asma'u ta tashi ta fice ta bar ajin, ba tare da wani ya yi yinƙurin tare ta ba, har ta yi nasarar barin cikin makarantar.

Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA)

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

Arewabooks
Ayshercool7724

P2

Kiraye-kirayen sallar magariba ake yi, Baba ya shigo gida da nufin ya yi alwala ya tafi masallaci.

"Nana, Nana"

"Baba ba ta dawo ba fa" matashin yaron da bai wuce shekara goma sha biyu ba ya bashi amsa.

"Ba ta dawo daga ina ba?"

"Makarantar islamiyya"

"A yanzun da magaribar nan, ke Jamila, Sa'adatu wai kuna ina ne ina ta magana kun mayar da ni mahaukaci?"

Jamila ce ta fito tana yamutsa fuska ta ce "Baba ba ta dawo ba fa"

"To tana ina? Ina ta tafi? Ko an aiketa ne?"

Rabi ce ta fito ta ce "Wai Nanan yarinyar goye ce ne da ka ke ta wannan haƙilon saboda ita? Idan ta gama yawon nata za ta dawo ai"

Guntun tsaki ya yi ya ce "Kai sani da aka tashe ku daga islamiyyar ba ka ganta ba?"

Sani ya ce "Ban ganta ba, kuma mu ne ƙarshen tafiya, yau na makara aka sakamu kwashe butocin alwala muka gama aka kulle makarantar"

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Allah ya sa ba bankaÉ—awa ta yi, tayi wani wurin ba"

"Ko kuma yawon watsewa ta tafi ba"

"Allah ba zai nuna mini watsewa a kan 'ya'yana ba" yayi maganar yana ficewa daga gidan.
Chapter 2 · 0% Book details