← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 32

Sashe 8

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali ya saka hannunsa ya É—ago layar da take wuyansa, wadda ta sauka a cikinsa. Ya zuba mata ido yana jujjuyata. Cikin hanzari Habu ya matsa kusa da shi, ya ce "Ka gane mene ne wannan É—in?" Ya É—aga manyan idanunsa ya kalli Habu, amma bai yi magana ba.

"To ka tuna wani abu ne? Waye ya baka ita?" Bai yi magana ba, ya tattare ta, ya zura ta a cikin rigarsa, ya kawar da kansa gefe daga kallon in da Habu yake.

Habu yayi ajiyar zuciya, ƙasan zuciyar sa, yana fatan Allah ya taƙaita wannan al'amari, kamar kullum ƙara rikicewa yake yi, yanzu ba ya magana sai dole, kuma maganar ma galibi shirme ce kawai.

*****

Abin da Baba yayi, tamkar ya share wa Auwal hanya wurin bayyana wa Nana abin da yake zuciyarsa game da ita, sai dai jikinta yayi matuƙar sanyi, da ya ce mata ya daɗe yana tausayinta, hakan ya sanya take tambayar kanta anya so ne? Ko dai tausayin ne kawai, duk da ya daɗe yana nuna mata alamun so. Gefe ga tsoro da fargabar abin da zai biyo baya yana damunta, dan kullum ta kwanta sai ta yi mummunan mafarki a kan malam Auwal, abubuwa na tashin hankali sun faru da shi.

Ajiyar zuciya tayi, bayan kwashe dogon lokaci malam Auwal, na ta yi mata bayani, ba tare da ta ce "Uffan ba"

"Nana" ya kira sunanta a hankali.

"Na'am" ta amsa tana sake sunkuyar da kanta ƙasa.

Ya É—an marairaice ya ce "Ina ta zuba nikaÉ—ai, ki ce wani abu mana"

Har yanzun dai ba ta yi magana ba, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji, banbarakwai take jin abin, wai yau malaminta ne kuma yake sonta, yake ta tsarata da kalamai na soyayya.
Jin taƙi magana, ya sanya ya canza akalar hirar, zuwa ta karatu sai a lokacin ta saki jiki, tana amsa masa.

Bai wani daÉ—e ba, ya ce "Bari na tafi, tun da dai ba za a kula ni ba, amma ki sani duk lokacin da na zo wurinki, a matsayin Muhammad Auwal na zo, ba ya sayyadinki ba" murmushi ta yi, ta cigaba da sunkuyar da kai.

"Ungo saka mini lambar wayarki"

Ta girgiza kai ta ce "Ai ba ni da waya"

"Haba dai? Ke haryanzu baki girma ba kenan, to shikkenan za'a nemo waya in sha Allah, ki gaida Baba, ki sanar masa ina nan tafe, za a zo ayi magana in sha Allah" shiru Nana tayi, ba ta yi murna ba, ba ta ji haushi ba, dan ita ba ma ta tantance tana son sa ko a a ba, ita dai ta san ba dan tana jin tsoron abin da ka iya faruwa ba, da ta so ya aureta, tana matuƙar ƙaunar muryar malam Auwal mussaman idan yana karatun Alqur'ani.

"Sai da safe, ki shiga gida, ki yi ta addu'a, idan kin yi azkar É—in kwanciya bacci, ki yi ta nanata *Wa hifzan min kulli shaÉ—anin marid*"

A hankali ta ce "In sha Allah, na gode sosai"

Ya ce "Yauwwa ungo wann, kya sai farar ƙasa, dan naga yadda ki ke shanta a makaranta"  yayi maganar yana miƙa mata kuɗi.

Ta É—an kalle shi ta ce "Ya sayyadi ni É—in?"

"Au ƙarya na yi? Ba kya sha ne?"

"Ina sha amma kaɗan" ta faɗa tana mamakin yadda saka mata idon da yake yi, har ya gane tana shan farar ƙasa.

"Karɓi mana" yayi maganar yana sake miƙa mata.

Ta girgiza kai ta ce "A'a ka bar shi, na gode"

Haɗe rai yayi ya ce "Bana son jayayya, karɓi" jikinta na ɗan rawa ta haɗa hannayenta biyu, ta risuna ta karɓa ta ce "Na gode sosai, Allah ya ƙara buɗi"

"Amin, shiga gida ina kallon ki" ta juya ta shiga gida, sannan ya juya ya tafi.

ta juya a hankali ta shiga cikin gida tana murmushi.
Abin har mamaki yake bata, wai ya sayyadi Auwal ne yake sonta, ganin abin take kamar almara.
Duk da damuwar, abin da take fargabar faruwarsa, na ci gaba da addabar zuciyarta, amma wani sashin na zuciyarta, na kwantar mata da hankali, saboda a ganinta malam Auwal masanin addini ne, mai riƙo da addini dan haka babu abin da zai faru da shi.

Tana sallama Baba ya tsare ta, ya ce "Yauwwa dama ke nake jira, tuntuni"

Ta tsaya, tana sauraron abun da Baba zai ce.

"Yaya maganar turowar? Ni fa ba na son a tsaya a ɓata lokaci a waje ana shashancin nan, ya kawo abin da Allah ya sa yake da shi, a ɗaura auren nan ki tafi, ko a rage mini wata wahalar" A yanzu dai Nana ba zata iya tuna, rabon da Baba ya mora mata wani abu ba, amma da an motsa sai ya yi ta mitar wahala ta yi masa yawa.

Ta numfasa ta ce "Ya ce na ce maka, ka yi haƙuri, yana kan tattaunawa da magabatansa ne, in sha Allah za su zo"

"Yauwwa ya dai fi. Na ce babu abin da ya baki ne? ƙanen ki sai kuka suke yi, sun ci abinci amma ba su ƙoshi ba, dama wanda Jamila ta zo da shi ne, suka karɓa suka cinye"

Nana ta ce "Gashi ya bani" ta miƙa wa Baba kuɗin da ba ta san ma nawa ne ba.

Ya saka hannu ya karɓa, ya duba naira dubu biyu ce. "To shi wannan saurayin naki kuma da haka ya zo, ka zo wurin budurwa ka ɓuge da bata dubu biyu kamar abin tsiya. Wancan saurayin naki Sule ya fi abin arziki. Ungo ga wata naira ɗari nan a aljihuna kya sai awara, wannan kuma ayi 'yan dabaru a ci abincin dare"

Nana ta karɓi naira ɗarin ta ce "To Baba na gode sosai"

Shigarta ɗaki ke da wuya, Suwaiba ta ja uban tsaki ta ce "Wallahi Nana ba zaki taɓa kan gado a rayuwar ki ba, yanzu kuɗin duk ki ka ɗauka ki ka ba wa Baba, alhalin kin wuni daga ke sai ruwan koko a cikinki, kuma dai duk wannan abin da ki ke yi, dan ya ce kin fimu ƙaunarsa, amma ba tausayinki yake yi ba, haryanzu kallon ki yake yi da laifin babar ku"

Tabbas maganganun Suwaiba haka ne, amma har ga Allah tana tausayin mahaifin nasu da gaske, ba ta ƙaunar gori da wulaƙancin da mama take yi masa a kan riƙe gida, amma ita ta lura ko a jikin sa, hakan baya wani damun sa.

"Nana, wai da gaske Auwwalun gidan mai koko ne yake zuwa wurinki? Wannan na ajin saukar, lokacin mu na zuwa islamiyya?"

Cike da ƙwarin gwiwa Nana ta ce "Eh shi ne, meyafaru?"

"Lallai Nana, me na sama ya ci balle ya jefowa na ƙasa? Ban da koyarwar nan fa, ban ce yana da wata sana'ar ba"

"Suby arziki ai na Allah ne, kuma ni 'yar waye da zan É—aga kai na ce sai wani?"

Suwaiba ta kwaɓe baki ta ce "Lallai kam"

Nana kuwa a zuciyarta, tana addu'a Allah ya tabattar mata da alkhairi, ko a daji malam Auwal yake rayuwa, muddin zai rabata da rayuwar wannan gidan na su, ta samu farin ciki haka take fata.

Ta cire hijjabin jikinta, ta saka wani ta fita tsakar gida ta tarar da mama su na ta dambarwa da Baba a kan dubu biyun da ta bayar.

Kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce "Baba dan Allah zan je bakin layi, idan maimuna tayi waina na sayo"

Baba ya ce "To hanzarta, ba na son fitar daren nan, mussaman da ba lafiya ce da ke ba, ki hanzarta" ta nufi hanyar fita cikin takunta mai kama da na ƙasaita.

Dai-dai lokacin da yayi sallama yake shigowa, ita kuma ta saka kai za ta fita, suka yi kiciɓis, gabanta ya yanke ya faɗi, ta ja da baya cikin tashin hankali da bugun zuciya mai tsanani.

Ayshercool
08081012143
What's app only please.
5
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

Daga tsakar gida Baba ya ce "Muryar wa nake ji haka, kamar Gaddafi?"

Kallon kallo Gaddafi suka yi da Nana daga bisani ya ce "Za ki matsa, ko sai na bi ta kan ki?" Jikinta na tsuma, ta ja da baya ta bashi hanya.

Sai da ya ja tsaki, sannan ya shiga cikin gidan.

"Kai kuwa Gaddafi ya da zuwan dare haka, kamar mara gaskiya?"

Ya numfasa ya ce "Na tsaya wani uzuri ne a hanya, fatan na same ku lafiya?"

Baba ya ce "Lafiya ƙalau, ya ikkon?"

"Lafiya kalau, amma ya na ga gidan duk ya canza?"

Baba ya kalli gidan ya e "Damunar nan, ruwan ƙarshe da aka yi ne, ya yi mana gyara, ya zubar mana da katanga, masai ta haɗe da rijiya... Cikin alfahari mama ta karɓe zancen, da bashi labarin cewa mijin uwar ɗakin Jamila ne, ya sanya aka gyara katangar gidan.

Ko da Nana ta dawo, duk su na tsakar gida, sun kewaye Gaddafi, ana hira ya ajiye musu ledojin da ya zo da su.

ÆŠakinsu ta shiga ta zauna, ta cinye wainar fulawan, da bai fi loma huÉ—u ta yi ba, kuma babu in da ta je mata sam.
Ƙasan zuciyarta, tana ta addu'a, Ubangiji Allah kar ya kawo abin da zai haɗata da Gaddafi, saboda karon su ba ya yi mata daɗi.

Tana zaune Nasiru ya shigo ya kawo mata abin da aka raba aka bata, ta karɓa tayi godiya, ta ajiye a gefenta ta kwanta, ba tare da ta buɗe, ta ga ko mene ne ba.

Sannu a hankali Malam Auwal yake nufo in da da take yana murmushi, ita ma murmushin take yi, tana jiran ƙarasowarsa, sai dai kafin ya ƙaraso in da take, ya bayyana cikin ainihin suffarsa mai tsayin gaske, ya shiga tsakiyarsu. A hankali ya din ga rage tsawonsa ya dawo daidai da tsawonsu.
Danƙo wuyan malam Auwal yayi, ya zura dogwayen yatsun hannunsa a cikinsa, yana zaro kayan cikinsa, yana watsarwa a ƙasa, ya ƙarasa har maƙogwaronsa, ya zura faratansa zai zaro maƙogwaronsa. Iya ƙarfinta Nana take ihu, da kururwar neman agaji, tare da magiyar ya ƙyale shi.

A fusace Gaddafi ya fito tsakar gida yana bala'i ya ce "Wai wannan 'yar abu kazan uban, ba ta daina wannan iskancin ba dama?"
Chapter 8 · 0% Book details