← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 32

Sashe 23

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da damuwa ya ce "Wai Rabi ya ki ke so na yi, ki na gani domin neme wa Nana magani, a can gurin mai magani na baro ta, kuma na ce a tafi da Suwaiban ki ka ƙi yarda"

"Ni wallahi ka san yadda za ka yi, dan ba zan yarda a kashe mini 'ya ba"

Imaran ne yayi sallama, yana watso takalmansa da suka tsinke ya ce "Yauwwa Baba na je gidan Yaya Atine, ta ce Nana ba ta gurinta wai a gidan mai magani aka baro ta. Baba ko fa asibiti ana bar wa mutum É—an jinya, ya za ayi a kaita gurin da babu idon wani nata da sunan neman magani? Ina ne gurin da aka kaita gaskiya zuwa zan yi na É—aukkota"

Baba bai yi magana ba, Suwaiba ta ci gaba da kakari "Baba ku taimake ni, Nana za ta kashe ni, jinina take lasa tana sha, dan zatin Allah ku hanata jikina zafi yake yi mini"

Imran ya ce "Wace Nanan? Nanan da bata gidan nan?"

Mama ta ce "Amma dai a yanayin da take ba za ta yi wa Nana ƙarya ba"

Imran ya ce "To Nana dai ba mayya ba ce, abin da ku ke zunÉ—enta ne Allah ya jarrabe ku. Ni dai dan Allah Baba ka gaya mini in da ku ka kai Nana, ni fa hankalina ba zai kwanta ba ina nan tana wata uwa duniya da ban sani ba"

A fusace Baba ya ce "Ban sani ba, ba zaka iya rayuwa tana wani guri ba, da ka tafi gantalinka shekara nawa tana nan ka na can gantalinka?"

Cike da ƙwarin gwiwa Imran ya ce "Amma ai na san tana gida a gabanka, ni gaskiya ban ji na gamsu da wannan tsarin ba"

Ga dai Nana ba ta gida, amma yadda suka ga rana haka suka ga dare, Suwaiba na ihun Nana na sha mata jini.

****

A hankali Nana ta ja jikinta ta zauna, duhu kawai take gani ba ta iya gane komai, ko tafin hannunta ba ta gani. Ta shafa bayanta ta ji alamun bango, ta ja jikinta ta jingina da bangon tana sauke ajiyar zuciya.
Cikin damuwa ta haÉ—a kanta da gwiwa, zuciyarta sam babu daÉ—i yau kuma nan Allah ya kawo ta.

Jin ƙarar buɗe ƙofa, ya sanyata ɗago kanta. Wasu mata ne biyu sanye da uniform su ka shigo ɗakin. Suka bubbuɗe tagogi sai ga haske ya ratso ɗakin. Duk da yanayin hasken ya nuna rana na daf da faɗuwa.

ÆŠaya daga cikin matan ta ce "Ta ce taso" babu musu Nana ta tashi, ta bi su suka fita, sai ta ga kamar ba gidan da aka kawota ba.

"Za ki yi salla ne?" ÆŠaya daga cikin matan ta tambayeta.

Da sauri ta jinjina kai alamar eh.

Aka janyo mata ruwa a rijiya, aka nuna mata banÉ—aki. Ta yi alwala ta fito aka mayar da ita É—akin nan ta yi salla. Su na tsaye su na jiranta kamar wata fursina, wata matar ce daban, ta shigo ta kawo wa Nana abinci da ruwa pure water.

Nana ta kalli Abincin gasashsen nama ne, amma ta kawar da kai.

"Ki ci abinci mana" matar ta yi magana cikin kulawa.

"Na ƙoshi" ta faɗa a taƙaice. Babu yadda ba su yi da ita ba, amma ta ƙi ci.

Har sai da ran ɗaya ya ɓaci, ta fice ta tafi gurin mai maganin.

"Sarkin baka, yarinyar nan fa taƙi cik abinci"

"Ahh haba dai? Ta tashi kenan?"

"Eh tun É—azu har ta yi salla ma"

"Na fa gaya muku yarinyar nan ku lallaɓa mini ita, ba na buƙatar a takura mata, ko ɓata mata rai. A nemo Salamatu ta tura 'yar aike cikin gari, a samo mata wani abincin" rai a ɓace matar ta amsa da to ta fita.

Nana tana zaune tana tunani, sai ga wata matar daban ta shigo da kayan saƙi shuɗaye a jikinta.

Sallamar da ta yi Nana ta amsa tana bin ta da kallo.

Cikin sakin fuska matar ta ce "Barka da yammaci baƙuwar sarki" Nana ta bi ta da kallo ba ta amsa ba.

Ta ajiye wa Nana kwanuka, ta ce "Ga abinci an saka a canza miki"

"Ina su Baba?"

Salamatu ta ce "Sun tafi, sai nan da makonni biyu za su dawo"

"Me yasa za su tafi su bar ni a nan? Ni gaskiya gida zan tafi"

"To shikkenan, amma fara cin abincin tukuna" Da ƙyar Salamatu ta lallaɓa Nana ta ci abinci, shi ma don tana jin yunwa ne sosai shi ya sa ta ci."

Nana ta riƙe alwalarta, a nan ɗakin ta gabatar da sallar magariba, sai dai tsoro ya fara kama ta, ganin ɗakin ya yi duhu babu haske kuma ita kaɗai a ciki.
Ba a jin amon kiran salla, sai dai ta kintaci lokaci kawai.

Ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, ta rintse idanunta tana ta adduo'in da suka zo bakinta.

Tana ji ana sallama, amma ta kasa ɗagowa, sai da aka taɓa ta sannan ta ɗago a razane tana sauke numfashi.

Salamatu ce ta shigo da fitila, da kuma kayan abinci.

Ta ce "Yi haƙuri, na tsorata ki ko? Ga abinci ki ci, ga kuma fitila idan ki na buƙatar mai taya ki kwana kuma sai mu kwana tare"

Cikin damuwa Nana ta ce "Ni ba na buƙatar komai, gida nake so na tafi"

"Haba Nana, ba kya so ki samu lafiya ki rabu da abin da yake damunki ne? Magani za ayi miki, babu wanda zai cutar da ke" ta daÉ—e tana rarrashin Nana, tana kwantar mata da hankali. Ta É—an ci abincin sannan ta kwanta, tana ta adduo'i.

Ji ta yi sanyi ya dame ta, ta dunƙule guri ɗaya, amma ba ta daina jin sanyin ba har cikin ƙasusuwanta, ta juya domin ta gyara kwanciyarta kawai ta ganta a cikin Sahara itakaɗai.
Ga dare, sai dai farin wata ya haske saharar, sai wani irin sauti da kunnuwanta ke ji, kamar na tasowar guguwa amma ba ta san daga ina sautin yake ba.
A tsaye ta ganshi a cikin saharar, a wannan karon ma fuskarsa a rufe a cikin rawani, sai dai a wannan karon dogo ne sosai fiye da kima. A hankali gurin ya ƙara haske duhun ya ƙara raguwa. Sai kuma ta ga tsayin yana raguwa har ya dawo na daidai mutane, ya saka hannu ya warware rawaninsa.
Ƙaisar ta gani a tsaye, duk ba ta iya ƙare masa kallo, amma yadda yake bayyanar mata a mafarki cikin suffar mutane shi ta gani.
Ta buɗe baki za ta yi magana, ya fara rikiɗewa ya zama tsoho tukuf, tun da Nana take a doron duniya ba ta taɓa ganin tufa kamar wannan ba, gashin kansa yana jan ƙasa fari ƙwal da shi, ga wasu irin kaya masu kama da yanar gizo gizo a jikinsa saboda tsabar tsufa.
Nana ta fara ja da baya a hankali, zuciyarta na hakaito mata addu'a, amma ta kasa furtawa. Ya sake girgiza ya koma wani baƙin raƙumi mai muni, ya buɗe bakinsa ya fara feso mata wuta.

Da wani irin gudu Nana ta juya, tana ihu, ma'aikatan gidan suka rirriƙeta.

"Innalillahi wa innalillahi raji'un, Baba ka yi mini addu'a, wayyo Babana, baba Imaran, Jamila dan Allah ku yi mini addu'a na kasa yi"

Cikin damuwa Salmatu da ke riƙe da Nana ta kalli mutumin da ke tsaye a kan Nana yana kallonta ta ce "Sarki ka yi wani abu a kan lamarin nan, kar fa ƙwaƙwalwarta ta taɓu"

Ya durƙuso yana haska fuskar Nana ya numfasa ya ce "Ni na san za a rina. Salamatu"

Ta amsa da "Na'am sarki"

"Idan kin ji ana zaki bari, damisa bari faɗanku na manya wa yake shiga, sai wawa sai mahaukaci, to wannan rigimar ce. Wannan yarinyar da ki ke gani ban san ta ina zan fara yi miki bayani a kanta ba. Dole jikinta ya ƙara rikicewa saboda haɗuwarta da buzayen nan. Da ba su riga sun tafi ba, da ƙarshenta a cikin su ɗaya ya samu waraka ɗaya kuma ya mutu a haka tsakanin ita da Buzun"

"Sarki ka ƙara rufe mini kai na, ban gane me ka ke nufi ba"

Ya yi murmushi ya ce "Da ina buƙatar ki gane, ai gwari gwari zan yi miki salameme. Ya saka yatsunsa biyu a goshin Nana, take ta yi shiru bacci ya kwashe ta.

****
Sosai Imran yake nema ya hana kowa zaman lafiya a gidan, saboda rashin Nana, ya kaɗa ya raya Baba ya ƙi gaya masa gurin mai maganin da aka kai Nana.
Ɓangaren Suwaiba ma abin nata gaba yake yi, sai ana zaune lafiya, sai ta yanke jiki ta faɗi tana kururwar Nana na sha mata jini.
Babu shiri Mama ta ce dole ta fita nema wa Suwaiba magani, kafin Nana ta kashe ta. Baba ya ce ta bari a kai ta gurin da aka kai Nana, amma fafur ta ƙi yarda.

Washegari, bayan Nana ta idar da sallar asuba, Salamatu ta zo.
A duk lokacin da ta zo gurin Nana, cikin sakin fuska da fara'a take yi wa Nana magana, hakan ya saka Nana ta É—an fara sakin jiki da ita kaÉ—an, duk da ba magana take yi mata ba.

"Nana taso mu je ko" babu musu ta tashi ta bi Salamatu.

Suna fita daga ɗakin, ta tuna mafarkin da ta yi, sai da ta ji gabanta ya faɗi, ta fara karanto addu'oin da Malam Auwal yake bata. A take ya faɗo mata a rai, har yanzu tana jin kewarsa sai dai a wannan karon, jikinta ne yayi matuƙar sanyi.

Salamatu na gaba tana biye da ita, sai da suka É—an yi doguwar tafiya, sannan ta fuskanci a cikin gidan da aka kawo ta neman magani suke.
Chapter 23 · 0% Book details