← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 32

Sashe 32

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

"To shikkenan, tashi ki je, Sa'a na tare da ke Hajiya Sa'a tun da ki na bibiya ga duk abin da aka saka ki. Ki je za a sanar da ke lokacin da ake buƙata" tashi ta yi tana jin daɗin yabon da ya yi mata.

*****
Nana da ta koma gida, ta tarar an kai Suwaiba asibiti, daga gurin masu magani, wai jikinta babu jini an riƙe ta a asibiti.
Sam Nana ba ta yi gigin bin su ba, ta dai yi wa Suwaiba Addu'a. Ta duba kuÉ—in da baban Muhsin ya bata dubu goma cif. Addu'a ta din ga kwarara masa da shi da zuriyarsa, saboda ta ji daÉ—in kuÉ—in nesa ba kusa ba.

Da yamma Ummi ta zo gidan, ta tarar da Nana a gida.

"Nana ke ba ki je asibiti duba Suwaiba ba?"

"Hmm kin san da yadda ta yarda nake zaune a gidan nan ne ma? Su na cewa ina ƙoƙarin kashe Suwaiba, wai ina sha mata jini.. sauran maganar ya kakare mata saboda kukan da ya kufce mata mai taɓa zuciya.

Jiki a sanyaye Ummi ta ce "Yanzun ma da na je, su na ta maganganu amma dan Allah ki manta da su. Ke dai Allah ya baki lafiya. Na zo ne a kan batun shirin bikinki, Baba ya ce ba za ayi taro ba. Amma ko ba za ayi taro ba ai kya fara gyaran jiki dai ko?"

"Me zan gyara? Ni dan Allah ki rabu da ni"

Ummi ta ce "Kamar yaya na rabu da ke? Aure fa za ki yi."

"Auren jeka na yi ka ba? Ai kun san ba so nake yi ba, amma babu yadda na iya ne, shi ne sauran mafitar da ya rage mini"

"Au Nana ba za ki daina maganar ba kya so É—in nan ba ko? Ke ba kya tausayin kanki da wannan wahalar da ki ke ciki ko? Ki je ki ki yi ta yi, sai mutum ya tausaya miki, idan ki ka tafka wani rashin mutuncin zai gane ke ba abar tausayi ba ce. Ki je ki yi abin da ki ka ga dama, ni na cire hannuna a kan ki"

"Allah yana tare da ni, na san shi ba zai cire hannu daga kaina ba" Nana ta yi maganar hawaye na gangarowa daga idanunta.

Ayshercool
08081012143

Alhamdilillah free pages sun kammala, masu buƙatar ci gaba su na iya tuntuɓata a kan lambar wayata.
1k ne a telegram
Via 0069685771
Aisha Adam stanbic ibtc sai shaidar biya ta 08081012143
Chapter 32 · 0% Book details