← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 32

Sashe 21

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya saka dogwayen yatsunsa yana ci gaba da shafa kumatunta ya ce "Alamu na nuna, sarƙar ƙaddara ta mayen ƙarfe na ƙoƙarin janmu wani  wuri, ta yi wani ɗauri mai wahalar kwancewa. Ko na ce sarƙar na ƙoƙarin sarƙe ki. Gobe za a wuce da ke gurin mai magani, 'yar uwakki ta shafa miki mugun tabo, tun da ta ce kina sha mata jini, babarta ba za ta yi shiru ba, za ta yi ta gaya wa mutane ne. Ga yayanki can ya sha ƙwayoyi yana ta bacci, gobe har ku tafi ba zai farka ba, domin na ƙarawa abin da ya sha ƙarfi. A duniya zan ga wanda ya isa ya raba ni da ke. Zan ga mai karambanin mai maganin da zai jarraba hakan".

"Allah ne zai raba ni da kai" ta yi maganar a hasale.

"Da zai rabani da ke, da bamu haÉ—u ba" ya bata amsa.

Nana ta waro ido ta ce "Kaii zaka yi saɓo, ki ba musulmi ba ne? Ko da yake musulmi ba zai yi abin da ka ke yi ba"

Ƙaisar ya yi dariya ya ce "Kamar ba musulmin ne ke neman jininki su yi tsafi da shi ba"

Ya koma ta bayanta, ya zuro kansa gefen fuskarta, hakan ya ƙara adadin bugun zuciyarta, jikinta yayi sanyi ƙalau kamar wadda aka saka a cikin firinji.

Ya ce "Bari na sake nuna miki wani abu, amma akwai buƙatar na tsaya kusa da ke, idan ba haka ba, wannan 'yar ƙaramar ƙwaƙwalwar ta ki bugawa za ta yi. Kalli can" ya nuna mata wani mudubi. Ta ɗaga kai ta kalla.

Kawai ta ga Auwwal a kwance ana yi masa wankan gawa, gefen cikinsa na ta zubar da jini.

Razana tayi za ta miƙe, amma ya riƙe ta ya ce "Kar ki zarge ni, babu sanya hannuna a cikin wannan abin, ya gama shirinsa gobe zai tafi Abuja, ɗazun nan masu ƙwacen waya suka tare shi, suka karɓi wayar suka caka masa ɗan buda.
Yaran kuma da suka yi, abokan yayanki ne, nan da 'yan kwanaki idan bincike yayi nisa shi ma za a kamo shi".

Wani irin yinƙuri Nana ta yi, domin ta ƙwace daga jikinsa amma ta ji an riƙeta. Ta ɗaga kanta kawai ta ganta a ana kiciniyar shiga taxi da ita, ta waiwaya ta ganta a tare da Yaya Atine da Baba.

Ta ja ta tsaya ta ce "Wai ya na ga haka?"

Baba ya ce "Ba ki da lafiya, gidan mai magani za mu je"

"To Baba ai ban yi sallar asuba ba"

Yaya Atine ta ce "Mu je, idan an je gidan mai magani sai ki yi sallar"

Nana ta kalli sama yadda gari ya fara haske, ta ce "A'a ni a bari na yi salla"

Baba ya ce "Ta dawo hayyacinta, a ƙyale ta tayi sallar"

Nana ta shiga gida Yaya Atine ta bita, ta yi alwala.

Yaya Atine ta ce "Rabi ki bari a tafi da Suwaiba gidan mai maganin nan a duba ta ita ma"

Mam ta ce "Eh ko ba gidan mai magani ba, ta je ta ƙarasa lasheta a hanya ta kashe ta, babu in da za ta je, kuma wallahi kurwar Suwaiba ta fi ƙarfinki" ta yi maganar tana hararar Nana.

Nana dai ta yi alwala, ta gabatar da sallar asuba, aka saka ta a cikin taxi, aka ja aka tafi, ba tare da ta san ina suka dosa ba.

Suwaiba kuwa ba ta tashi daga bacci ba, sai bayan ƙarfe tara na safiya, kuma babu wanda ya tashe ta, domin ta yi salla. Sai a lokacin ta yi salla, ta nemi abin karyawa.

Jin Mama na ta jera mata sannu ya sanya ta ce "Wai mama sannun me ki ke yi mini ne?"

Mama ta ce "A'a abin da ya faru da ke jiya mana, wannan azzalumar tana neman kar ki"

Cikin rashin fahimta Suwaiba ta ce "Wace ce? Ni fa ban gane ba"

"Jiya kururwar da ki ka din ga yi ki na Nana za ta kashe ki, tana miki jini, ba mu yi bacci ba fa" Suwaiba ta zaro ido ta ce "Ni É—in?"

Jamila ta ce "Eh mana, kasa numfashi ki ka yi fa, kina ta kuka wai Nana tana sha miki jini"

Jikin Suwaiba ya yi sanyi, ta ce "To ai ni tun da na kwanta, ko juyi ba na tunanin na yi, sai yanzu na tashi daga bacci"

Jamila ta ce "Ikon Allah, kin ga kururwar da ki ka din ga yi kuwa, wai Nana na sha miki jini?"

"Ni dan Allah ku daina wannan zancen tsoro ku ke bani wallahi kar na je, aljanun nata ne nima su ka shafe ni"

Muryar Imran ce ya dawo da su kan tsakar gidan, yana ta kwaÉ—a wa Nana kira.

Nasiru ya ce "Nana fa sun tafi gurin mai magani, bayan sallar asuba"

"Kamar yaya ita da wa?"

"Asubar farko, aka je aka taho da Yaya Atine daga gidanta, a taxi É—in malam Shehu, gari yana fara haske suka tafi. Jiya ne Suwaiba ta din ga ihu cikin dare wai Nana tana sha mata jini, shi ne suka tafi da sassafe"

"Kuma shi ne ba a gaya mini ba, ina ne garin mai maganin, kar aje a kai ta gurin bokaye"

"Wallahi ban sani ba"

Imran ya ce "Ke Suwaiba, ya aka yi Nanan ta sha miki jini, ita ba mayya ba, kar ki ja a ɓata mata suna, ni ba na son ƙananan maganganu ki bar ta ta ji da halin da take ciki mana"

A fusace Mama ta ɗaga labule ta fito ta ce "Ban gane ba, za ta yi mata ƙarya ne? ko dan kai ba a gidan ka kwana ba, ba ka san a halin da ta kwana ba"

"Eh Alhamdilillah, na ji daɗin hakan ma, ai da gani ku ke yi Nana tana sane, duk abubuwan da yake faruwa da ita, tana sane ita ta yi wa kanta ƙarya take yi. Yanzu idan ma ƙarya take idan ma gaske ne, ai kwa gani, kuma wallahi na ji wata magana a unguwa ta cin zarafin Nana, ko yi mata ƙage wallahi sai na saka an ɗaure mutum igiya ta yi saura"

Jamila ta ce "Mama dan Allah rabu da shi, kar ya yi miki rashin kunya"

***
Nana kuwa rarraba ido kawai take yi a hanya, tana ta ƙoƙarin tuna wasu abubuwa a ƙwaƙwalwarta, amma abu ya gagara. Abin da take iya tunawa, kawai hango Suwaiba tana zubar da jini, amma ta kasa tuna takamaiman yadda aka yi ta ga jini a jikin Suwaiba.

Gaba ɗaya ta nemi kuzarinta ta rasa, jikinta yayi sanyi ƙalau, ko ƙwaƙwƙwaran motsi, sai ta yi da gaske take iya yin sa.

Sannu a hankali, ƙwaƙwalwarta ta fara fassara mata maganganun da ta jiyo Baba yake yi. Wai ana idar da sallar asuba, ya kira Saleh a waya ya ce masa wai idan akwai kuɗi a hannunsa, ya turo wani abu za a nema mata magani. Wani irin takaici ya kama Nana, sam Baba ba ya gudun abin kunya da duk wani abu da zai zubar musu da kima.

"Atine, ai yakamata tun yanzu yaron nan, ya fara ƙoƙartawa shi ma, tun da dai aurenta zai yi, duk wata hidima da za a yi mata, ya saka hannu a yi da shi"

Babu kunya Yaya Atine ta ce "Gaskiya ne, ai kamata yayi ace ya É—auke maka wasu nauye-nauyen".

Baba ya ce "Sosai fa, kuma kin ga  hakan zai ƙara tabattar masa da gaske zan ba shi aurenta. Ai mu na dawowa daga gurin maganin nan kawai iyayensa su zo a wuce gurin"

Nana ta rintse  idanunta, tana fatan bacci ya ɗauke ta, ba ta tunanin akwai wani wanda zai aureta ta yi mutunci a idonsa, da irin wannan halin na Baba, na son jinginawa wani ɗawainiyar da shi yakamata ace ya yi abarsa.

Sun sha doguwar tafiya sosai, kafin su isa wani surƙuƙin ƙauye, sai da suka yi nisa sosai da sosai, suka daina ganin gidaje. shige da ficen ababen hawa ne, ya sanya suka tabattar da akwai mutane a gurin, domin kuwa hatta kwalta babu a gurin, sai uwar zangarniya.

Yanayin surƙuƙin gurin, sai parking ɗin motar suka yi a bakin hanya, suka saukko domin takawa su ƙarasa, sai dai ƙafar Nana ta ƙi takuwa sai ma lanƙwashewa da ta yi, kamar mai shan inna.

Sun daɗe a gurin, Nana ta kasa taka ƙafafuwanta, sai da ƙyar ta ɗan saki, ta  takawa a hankali.

Tun da suka doshi hanyar da aka nuna musu, aka ce a nan gidan mai maganin yake, Nana take ganin garke garke na Raƙuma su na fitowa daga hanyar, jajaye da farare. Yaya Atine ce ta riƙe ta suke tafe a hankali, saboda da ƙyar take taka ƙafafuwanta.
Nana ta ce "Yaya Atine dama akwai baƙin raƙumi?"

Yaya Atine ta ce "A ina?"

"Ga su nan su na ta wucewa, ba ki gansu ba?"

Yaya Atine ta ja ta tsaya ta ce "Kai Gaddafi, ku na ganin raƙuma ko kuma nima abin nata ne zai shafe ni, nice ba na ganinsu?"

Baba ya ce "Raƙuma kuma a ina?"

"Yo ai ji na yi tana zancen baƙin raƙumi, ni kuma ko kofato ban gani ba balle raƙumi. Kai zo ka riƙe 'yar ka, kar na gano abin da ba shikenan ba"

Nana na jin haka, ta zame hannunta daga na Yaya Atine ta ci gaba da takawa a hankali.
Daga nesa suka hango gidan, mutane na ta shiga su na fita.

Ja da baya Nana tayi da sauri tana kare fuskarta.

Baba ya ce "Me kuma ya faru?"

Cikin damuwa Nana ta ce "Baba wai ba ka gani, baƙin raƙumin nan ne yake feso mini wuta fa"
Cikin takaici Gaddafi ya ce "Dan Allah Baba ku daina biyewa yarinyar nan, ku zo mu ƙarasa."
Su na tunkarar gidan, amma raƙuman na ƙara yawa, Nana ta fahimci ita kaɗai take ganinsu, su ba sa ganinsu.
Chapter 21 · 0% Book details