← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 32

Sashe 3

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nana kuwa tun da ta fita daga islamiyyar, babu wanda ya ganta, dan haka ta ci gaba da tafiya ba tare da ta san in da take sanya ƙafafuwanta ba, ba ta iya tantance rana ce ko dare ma, sai dai tana jin yadda zafin rana yake ratsa ƙafafuwanta da kuma tafin ƙafarta, da take takawa babu ko takalmi. Ita dai burinta ta yi nesa da in da take, ko ta fita daga halin da take  ciki, ko kuma tserewa abin da take jin tamkar ajalinta ne yake tunkarota.

Wani matsakaicin gida ta tunkara, babu sallama babu neman izinin masu gidan, kawai ta afka ciki. ÆŠaya daga cikin jerin É—akunan ta shiga, ta cire hijjabin jikinta na islamiyya, ta cukuikuye shi, ta yi fulo da shi, ta kwanta.

Kusan mintuna goma sha biyar, da shigarta babu motsin kowa a gidan. Wani matashi ne yayi sallama, ya ji shiru, ya sake sallama ya ji shiru.

Saka kai yayi ya shiga ciki yayi tozali da Nana a kwance tana bacci. Turus yayi yana kallonta, yana tunanin ita kuma wannan daga ina.

Shaiɗan ne ya shiga ƙawata masa kyakkyawar baƙar fatarta mai sheƙi, da kuma ilahirin jikinta.

A hankali cikin sanɗa ya shiga ɗakin, yana cigaba da ƙare wa ƙirjinta kallo.

ÆŠan dukan gefen carfet yayi, dan ya tabattar da idonta biyu ko bacci take yi.

A hankali yake ƙoƙarin kai hannu jikinta, kwatsam! Ya jiyo muryar matar gidan a ƙofar gida tana gaisawa da maƙwabta.

Cikin hanzari yayi baya ya dawo tsakar gida ya tsaya.

Sallama tayi tare da yara ƙanana, ya amsa yana mazewa.

"Saleh, zuwa babu sanarwa haka?"

Ya É—an sosa kansa ya ce "Wallahi kuwa, ina ta sallama amma gidan shiru babu kowa"

Ta kalli gidan ta ce "Ikon Allah, kuma yarinyar maƙwabta na bari a gidan, ta jire mini na je ɗaukko su hafsa daga makaranta shi ne ta bar mini gidan a buɗe haka?"

Saleh ya ce "Aikuwa ta yi ganganci da ta bar miki gidan babu kowa haka"

"Aikam yaushe ka shigo garin ne?"

"Shekaranjiya da daddare na ce yau bari na ɓullo mu gaisa"

"Aikuwa ka kyauta" ta yi maganar tana É—aga labulen É—akin.

Turus tayi, tana maimaita"Innalillahi wa innalillahi raji'un" ganin mutum a kwance.

Ya kalleta ya ce "Lafiya kuwa?"

Ba ta amsa masa ba, ta ƙarasa tana ƙare mata kallo, ta kai hannu ta taɓa ta ta ce "Nana" sai dai shiru ba ta amsa ba.

Ta kalli ƙafafuwan Nanan, futu-futu, har da jini alamar ta taka abubuwa a hanya.

"Subhnallah, kar dai da ƙafa ta taho Nana, Nana tashi mana" sai dai ba ta motsa ba.

Cikin basarwa Saleh ya ce "Anty lafiya kuwa? Wace wannan ɗin dama da mutum a gidan nake ta sallama ba a amsa ba?" Yayi maganar yana ƙare mata kallo, dan shi gaba ɗaya ma bai lura da raunin da yake ƙafarta ba.

Anty ta ce "Ƙanwata ce wallahi, ba ta da cikakkiyar lafiya ne, ga wayata ta lalace balle in kira gida in ce tana nan, kuma ni Wallahi ban haddace lambar kowa ba, balle na kira na gaya musu"

Suka ci gaba da jimantawa, Nana kuwa ta ci gaba da baccinta, mai kama da suma.

Baba yayi sintiri zuwa islamiyyar su Nana babu adadi, tun yana yawon neman ta har ya gaji.

Suwaiba ta ce "Wataƙila mutanenta ne su ka yi wani wurin da ita"

"Ba wasu mutanenta, ayi ta fakewa da sheɗanu tana rashin mutunci, ta taɓa yin irin haka ne? Allah ne kaɗai ya san gidan uban wanda ta tafi"

Baba ya ce "A'a ba na tunanin za ta je wani wurin ba mu sani ba, tun da ba ta taɓa yin hakan ba, amma ina Jamila ma?"

"Ta na gidan uwa É—akkinta É—in nan, maman khairat, tun azahar tana can"

Baba ya ce "Kuma haryanzu goma saura na dare, ba ta gida uban me take yi a gidan mutane?"

Mama ta ce "A'a yau na ga abin tsiya, to malam ba abincin safe babu na rana, ba dole yarinya ta tafi in da za ta samu ta ci ba? Ai gara ita an san in da take, 'yar ka fa? Shi ya yi nasa wuri, ita ma gashi ta kama gabanta" Baba yayi shiru bai sake cewa komai ba.

Shirun sa ke da wuya, Jamila ta yi sallama, suka amsa baki É—aya, Baba ya É—aga kai zai yi magana, sai yayi shiru ganinta da babbar leda.

"Mama na dawo"

"Sannu jamila, ya ki ka barota?"

"Lafiya kalau Alhamdilillah, baba sannu da gida"

Baba ya ce 'Yauwwa Jamila, amma ina ki ka tafi haka ba kya gida?"

Jamila ta taɓe baki ta ce "Baba Allah ya gani na gaji da raragefen shiga banɗaki ne, ga yunwa ina ji shi yasa na tafi gidan maman khairat na wuni a can"

Baba ya ce "Ku yi ta haƙuri ku na addu'a, in sha Allah za a gyara katangar nan, kuma a gyara masan, mutanen unguwar nan ne ma, babu haɗin kai da zuciyar taimako, amma yadda iftila'in nan ya afko mini, ai kamata yayi ayi gidauniyar da za a tallafa mini"

Mama ta ce "Kai wa ka ke tallafawa idan matsalarsa ta tashi?"

"Rabi wai babu damar na yi magana, sai ki nemi tozarta ni a gaban yara"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani tozarci gaskiya ce"

Bai bi ta kanta ba, ya kalli Jamila ya ce "Jamila, Nana fa ba ta dawo gidan nan ba, tun É—azu ake neman ta ba a ganta ba" Jamila ta tsaya da juye abincin da take yi ta ce "To ina ta tafi?"

"Wallahi ban sani ba, an rasa in da ta shiga "

Jamila ta ce "Kuma ita ba waya ba, balle a kira ta kuma dai na ga ba ta taɓa yin irin haka ba"

"Wallahi kuwa. Kai Sani É—aukko kwano a zuba mini abincin nan nima na saka a cikina, dan rabona da abinci tun safe, ashe akwai sauran masu zuciyar taimako a unguwar nan, irin wannan abinci haka Jamila"

Haka Baba ya karkace aka lamushe abinci da shi, har ya nemi ya manta batun ɓatan 'yar sa Nana.

*****
Misalin ƙarfe tara na safe, Nana ce a zaune, tana kurɓar kunun tsamiya, duk da babu sukari a cikinsa, amma ba ƙaramin daɗi yake yi mata ba, ga dankali da aka take mata kwano da shi, wanda rabonta da ta ci ta ƙoshi haka har ta manta.

Ummi ta dube ta ta ce "Nana, wai garin yaya aka yi ki ka taho gidan nan a ƙafa haka? Tun jiya kin ƙi magana"

Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ban san ya aka yi ba, ni dai kawai ina islamiyya na ji duniya ta yi mini zafi, kamar zan mutu shikenan ban san meyafaru ba, na dai ji ina bacci, kawai na farka na ganni a nan"

Ummi ta ce "Ohh wannan larura taki Allah ya yaye miki Nana, an gode Allah ma da ki ka yo nan ba wani wurin ki ka yi ba, in ƙara miki dankalin ne?"

Nana ta girgiza kai ta ce "A'a na ƙoshi Alhamdilillah"

"Nana ina kyautata zaton mutanen nan ne, suka hana miki samun mijin aure har yanzu, ga Habibu, rumi-rumi an fara magana aka fasa, ni a yanzu ma akwai wani a ƙasa kuwa?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.

"Wallahi Nana ina yi miki fatan ki yi aure, ki bar wannan gidan namu, da ba a iya amfana maka komai, idan ba uwarka ce ta yi maka ba, kin ganni nan duk da yau da daɗi gobe babu, yau mu ci gobe mu yi haƙuri, ga azabar dangin miji, amma ya fiye mini wannan gidan namu, da kamar a cikin sa aka yi wahayin babu, ke kanki a yunwace ki ke, ga Baba ya damu ki yi aure, dan Allah kalli wata breziya a jikinki, dan masifa duk kin ƙuƙƙuleta, wallahi da na shiga banɗaki na tarar da phant ɗinki, na za ta tsumma ne da yarwa zan yi, wannan wace irin rayuwar azaba ce?"

Nana ta sunkuyar da kai ta yi shiru, dan duk abin da ummi take faÉ—a gaskiya ne, amma waye zai aureta da wannan larurar a haka? Malam Auwal na islamiyyar su, na ta nuna mata alamar soyayya amma ta yi burus, dan ta san yau da gobe sai Allah, babban fatanta ta rabu da wannan larurar, duk da tana burin yin auren, dan ita kaÉ—ai ta san masifar da take ciki.

"Kin san wani abu Nana, akwai wani mai magani da na ji maƙwabciyata su na magana rannan, zan yi mata magana ta kwatanta mini wurin, anjima mu kama hanya mu je ko Allah ya sanya a dace, daga nan na je na duba idan an gyara mini wayata sai na raka ki gida"

To kawai Nana ta iya cewa, ta cigaba da shan kununta a hankali.

*****

"Alhajin Allah"

"Na'am malam" ya amsa yana tattara nutsuwarsa a kan mutumin da yake zaune, a kan tabarma, gefensa ga carbi mai dubu, ga wani ɗan farantin katako da ƙasa a kai. Yayi shiru ya na nazartar ƙasar da ya yi wa zane-zane a gabansa.

"Malam me ka gani ne?"

"Eh to, buƙata zata biya Alhaji Zailani, amma gaskiya za a sha gwagwarmaya, ga magauta ko ta ina a tattare da kai, arziki zai ninku fiye da yadda ka ke zato, amma gaskiya zaka sha wahala, ƙila ma ka iya rasa ranka, kuma a gidan huɗu ga wata kujerar siyasa nan ko ta mulki da zaka iya samu, sai dai gidan uku ya nuna shi ma akwai bala'i, da tarin ƙalubale"

Alhaji zailani ya yakice gumin da yake tsatsafo masa daga goshinsa ya ce "Yanzu malam menene abin yi, dan ko a yanzu kasuwancina harkokin sun fara ja da baya"

Ya sake zazzana ƙasa, ya ɗago ya ce "Eh ga wani ƙulli nan a binne a kusurwa huɗu na mararraba, a kanka, amma warware wannan ba zai yi wahala ba, yanzu mafita ɗaya ce da za a samu mai burujin aƙrabu, ko hutu ko surdanu da zai dace da burujin ka, kuma za su taimaka maka ka kai ga ci, ba tare da ka fuskanci ƙalubale ba"
Chapter 3 · 0% Book details