Sashe 16
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta share hawayenta ta ce "Eh, da fari tausayina, daga baya ka koma so na, dama na san zaka rabu da ni, dama na fi so na ji daga bakin ka ne, tun lokacin da aka ce ba zaka iya riƙe aure ba, na ga komai a bacci, har rabuwar nan tamu na yi mafarki na gani, ba zaka aure ni ba. Hakan ba ya nufin zan manta tarin alkhairin ka a gare ni, Ubangiji Allah ya baka mace ta gari lafiyayyiya"
Zai yi magana ta girgiza kai, ta fice daga ofishin, zuciyarta na zafi hawayen da take ƙoƙarin dannewa, su ka ƙi dannuwa.
Auwal bai taɓa tunanin yana son Nana har haka ba, sai da Umma ta hana shi aurenta, kuma abin bai tsaya a nan ba, sai da Umma suka tura shi Qatar.
Nana ta tafi rijiya, ta É—ebi ruwa ta wanke fuskarta, sannan ta koma ajinsu aka ci gaba da tilawa da ita.
Sosai rabuwa da Auwal ya shigi Nana, duk da ta yi mafarkin hakan, amma ba ta bari ta gasgata hakan ba.
Har aka tashi daga makaranta, hankalinta ba ya kan abin da aka ƙara musu sam.
Da daddare, bacci ya gagari idanun Nana, sai tunani da zancen zuci, ya din ga ziyartar zuciyarta, har ta rasa wane tunani ya kamata ta yi.
Jamila ce ta zo da abinci daga gidan maman khairat, ta cewa Nana ta tashi ta ci, amma ta ƙi.
Sai da ta takura mata, sannan ta ci kaɗan, ta sha lemon ta kwanta, sai dai abincin ya tsaya mata yaƙi wucewa.
Tana daga kwance, tiryan-tiryan, yadda aka fasa aurenta na farko ya dawo mata, yadda take samari, su na tafiya, duk da galibi mutanen banza ne suke bibiyarta. Amma Suleiman ya zo da gaske zai aure ta.
Sai dai Baba ya din ga zubar mata da mutunci a idonsa, ta hanyar roƙe-roƙen kuɗi, kuma wani abin mama ce take ziga shi yake yi, har ita ma wasu lokutan sai ta tura ta ce ya bata kuɗi, sun wuni ba su ci abinci ba. Tun yana bayarwa da marmari, har ya gaji ya fara mita. Ya san da Nana ba ta da cikakkiyar lafiya, duk da a lokacin abin ya lafa, amma mama ta zaunar da shi, ta din ga karanta masa Nana aljanu har sun fara haukata ta. Matarsa ta zo har gida ta ci mutuncin Nana, har da an gaya musu babarta ce take biye-biyen bokaye, abin ya koma kanta take fama da aljanu.
Duk da dama Mama ta saba faÉ—ar wannan maganar, idan ta so cin mutuncinta, amma abin yayi mata zafi ya mata ciwo.
Wuni ta yi tana kuka, Suleiman da kansa ya je gida ya ba wa Nana haƙuri, bayan ya samu labarin abin da matarsa ta zo ta yi mata, sai dai tun da matar ta koma gida, ya aka rasa gane kanta, ta kwanta rashin lafiya.
Ta din ga fama da matsanancin ciwon kai, idan ta fara sai ta fita hayyacinta ko gani ba ta iya yi, suka je asibiti ba a ga komai ba.
Ya koma gidansu Nana, ya ce idan ta san wani abu ta yi wa matarsa, ta bari uwar 'ya'yansa ce, ba zai so lafiyarta ta taɓu ba, tun da ai ya zo ya bata haƙuri.
Nana ta din ga rantse-rantsen ita babu abin da ta yi mata, ƙarshe dai matar kamar za ta haukace, ya zo ya ce a dawo masa da kayan aurensa, tun a waje Nana ta cutar da iyalinsa, ina ga idan ya aureta, dama kuma an ce masa mahaifiyarta na biye-biye.
Duk yadda Nana take son ta yi aure, ko dan saboda tarin ƙalubalen da take fuskanta, amma fasa aurenta da Suleiman bai wani dame ta ba, domin tana fargaba mussaman yadda aka gama zubar mata da mutunci a wurinsa.
Ajiyar zuciya ta sauke da ta zo nan a tunaninta, sai da kanta ya sara, ta sauke ajiyar zuciya. Ga abubuwa da dama su na cin zuciyarta, tana buƙatar abokin shawara da tattaunawa, amma rashin yardarta bai sanya ta bawa wani damar, hakan a rayuwarta ba. Mutanen da suka cancanci hakan a rayuwarta duk ba ta ita suke yi ba. Babbar damuwarta a yanzu, bai wuce yadda ta san ko ba ta so, Baba sai ya ƙaƙaba mata Saleh ba, dan ta fuskanci zamanta ne kawai ba a so cikin gidan, duk ga su Suwaiba da Jamila, su babu wanda yake takura musu a kan aure sai ita.
Sosai take jin zafin rashin Auwal, ko ba komai mutum ne ma'abocin Alqur'ani da kuma riƙo da addini, ta san abu ne mawuyaci a iya cutar da shi, ta sanya ran idan tana tare da shi, za ta samu sauƙin wasu abubuwan.
"Ke baiwar Allah" ta ji an kirata. Ta ɗaga kai, ta hangi wata mata bararoji a tsaye, ta yi kwalliya da tarin tsummokara, da wasu irin tarin sarƙoƙi na zare a wuyanta, da ƙullin kaya a hannunta, ta burtso da gashin ta gaban goshin ta.
Nana ta É—aga kai ta ganta a wani wuri, da ba ta san ina ne ba.
Matar ta ce "Zo na baki magani"
Nana ta ce "magani kuma, na me?"
Matar ta sauke mayafin da ta rufe fuskarta, ko ina tsagu ne a fuskarta, har baka iya tantance kamaninta, saboda azabar billayen da ke fuskarta.
Matar ta ciro wani magani a cikin, ƙullin kayanta ta ce "Ki zuba a tafin hannunki, ki lashe"
Nana ta ce "To ai ba ki gaya mini na mene ne ba?"
"Idan ka sha, ba zaki ganin Ƙaisar ba, zai daina bibiyar ki yana takura wa rayuwarki, zai rabu da ke har gaban abada. Dukkanin damuwar ki za ta kau, babu wanda zai sake zuwa auren ki, yayi nasarar korarsa ko ya saka miki wani ciwo. Dan yan daf da fara kashe mutane, domin wata ƙungiyar asiri ce suke nemansa ido rufe yayi musu aiki. Idan suka sadaukar masa da jini, zai fara kisan mutane ne, kuma zai fara da mutane mafi soyuwa a gare ki"
Jiki na rawa Nana ta miƙa mata hannu, domin karɓar maganin.
Matar ta yi murmushi, haƙoranta suka bayyana baƙaƙe ƙirin da su, ta kama tafin hannun Nana, ta zuba mata maganin, da yawa.
Tana kama hannunta, Nana, ta ji tamkar an zare mata lakar jikinta, jikinta yayi wani irin sanyi, da ta kasa ko ƙwaƙwƙwaran motsi. Ta kai garin maganin bakinta ta fara sha...
Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807
BUZU
AISHA ADAM AYSHERCOOL
YOTA/002
P9
Ko da Nana ta sake lasar maganin, sai ta ga fuskar matar tana komawa baƙa ƙirin, tana ta fito da dogon harshe, tamkar na macijiya, wani abu mara kyan gani na futa daga bakin nata.
Iya ƙarfinta Nana take son ta yi addu'a, idan mafarki take ta farka, amma ta ji tamkar an saka dutse an tokare maƙogwaronta zuwa huhunta.
Babu tsammani, ta ga wata irin guguwa ta haɗu, Ƙaisar ya bayyana a tsakaninsu yayi wani irin mugun cilli da matar a gefe. Yayo kan Nana, ya zubar da sauran maganin hannunta, ya shaƙe mata wuya.
Wani irin kakari ta din ga yi, ta na amai dunƙunlen jini yana fitowa ta hancinta da bakinta. Ji ta yi numfashinta na neman ɗaukewa.
Ita ma Nanan, ya yi jifa da ita gefe, ta riƙe wuyanta tana numfashi da ƙyar.
Ya kalle ta a zafafe ya ce "Idan ki ka ci gaba da irin wannan gangancin, za a kashe ki a haka, babu wani mahaluki da zai iya raba ni da ke. Guba ta baki za ta kai jininki ayi tsafi da ke saboda tasirin taurarinki. babu wanda zai iya baki wani magani ya raba ki da ni, idan ki ka ci gaba da yinƙurin rabuwa da ni, za ki kashe kan ki da kan ki" yana maganar tartsatsin wuta na fitowa daga jikinsa, yana ƙona Nana.
A hankali ta buÉ—e idonta, ta ganta a kan shimfiÉ—arta, ta takure jikinta yana ta rawa, numfashinta yana fita da kyar. Wuyanta sai raÉ—aÉ—i yake yi mata, haka ma jikinta.
Ta kai hannu ta É—auki fitilarta ta kunna, tana haska É—akin, ba kowa a É—akin sai ita kaÉ—ai. Jikinta ya ba ta wani abin tayi, su Jamila suka gudu suka bar ta a É—akin.
Ta yinƙura da azama ta tashi tsaye, amma jikinta sai raɗaɗi yake mata, kafaɗunta kamar ba a jikinta suke ba.
Ayatul kursiyyu ta din ga karantawa, ta fita ta É—auki buta, ta shiga banÉ—aki.
Tana fara fitsari ta ji ƙarnin jini, tana dubawa ta ga fitsarin jawur, jini a maimakon fitsari. Gashi ko kwana bakwai ba ta yi da gama al'ada ba. Ta wanke jikinta tayi alwala, ta koma ɗaki, gaba ɗaya ta kasa yadda har yanzu ba a cikin mafarki take ba.
Da safe ta fito ta yi aikace-aikace da za ta yi, Jamila ta ce "Nana me ya same ki haka?"
"A ina?"
"Jiya da daddare ki na ta kakarin amai, ki na kuka a bacci, yanzu kuma kalli jikinki, kamar an zane ki da bulala" Baba da ya fito daga banÉ—aki, shi ma ya kalli Nana.
Jikinta duk kwanciyar bulala, gashi ta É—ashe ta yi haske, kamar mara jini a jiki.
Nana ta kalli jikinta, ta ɗan taɓe baki ba ta ce komai ba, ta ɗebi ruwa ta shiga banɗaki domin yin wanka. Sai dai wannan karon ma, fitsarinta jini ne kawai yake zuba.
Kawai ta jingina da jikin banÉ—akin, ta fashe da kuka, sai da ta yi mai isarta sannan ta ta fara yin wankan. Sai dai tana zuba ruwan a jikinta, ta ji kamar fatarta za ta zazzago, jikinta ya hau kyarma.
Duk da a cikin banÉ—aki ta yi, haka ta furta a'uzubillah, ta cigaba da zuba ruwan a jikinta tana wanka, har ta kammala ta fito.
Ta yi alwala, ta shiga ɗaki ta shirya, tana kallon Baba yana kallonta, amma ba ta gaishe shi ba, haka kurum ta tashi da matsanancin ɓacin rai, ko ganin Baban ba ta son yi.
Ba ta kula kowa ba, ta fice ta tafi makaranta.
Gaba É—aya jikinta ciwo yake yi mata, ga jiri tana fama, dan haka a cikin aji ta yi zamanta, ta kifa kanta a kan tebur, tana ta kewar rashin Auwal.
*****
"Safiyya"
"Na'am Hajjaju"
"Yaya kin yi magana da Jamila kuwa?"