Sashe 30
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nana tun da ta dafe kanta, ta sunkuya ba ta ko motsa ba, sai yanzu da ta ɗago ta fara magana iya ƙarfinta "Innalillahi wa innalillahi raji'un, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan, ya za ayi malam Auwal ya mutu? Dan Allah ku tashe ni kafin ƙwaƙwalwata ta samu matsala, dan Allah ku tashe ni daga baccin nan" ta ɗago da idanunta suka yi wani irin ja kamar za su kama da wuta, hawaye ne tare da mijina suke rige-rigen zuba a fuskarta.
Baba ya ce "Nana meye haka? Zuwa islamiyyar na banza dama ki ke yi? Ko ni na mutu ai ba kya yi haka ba" jefar da jakar hannunta ta yi, tai waje.
Baba ya bita da sauri, amma tamkar walƙiya bai ga ko sahunta ba.
Kai tsaye Nana rukunin ofisoshin malamai ta nufa a islamiyyar su.
Malam Nura ta tunkara, babban abokin malam Auwal.
Cikin yanayi na ɗimuwa ta ce "Wai an kashe malam Auwal? Dan Allah kai ma ka iya ruƙiyya ai ka na yi mini, dan Allah ka karanta mini koma mene ne ko zai sake ni na tashi daga wannan baccin."
Ya ƙarewa Nana kallo, da gaske a ɗimauce take, cikin sigar rarrashi ya ce "Zauna mu yi magana"
"Ba zan zauna ba, kawai ka yi mini ruƙiyya na tashi. A nan fa na same shi a ofishin sa, muka yi magana, ya gaya mini gaskiya ba zai iya aurena ba, kuma duk na fahimce shi, ya ce mini zai tafi Qatar, to kuma daga na yi tafiya sai ace mini ya mutu?"
"Al mautu haƙƙun Nana Asma'u, mun yi rashin Auwal. Æata gari ne suka soka masa makami su ka Æ™wace masa waya kafin a kai shi Asibiti rai ya yi halinsa, ki yi masa addu'a"
Jikinta na karkarwa ta ce "Ya sayyadi Nura. Na yi rashi ba zan manta Yaya Auwal ba, yanzu waye zai din ga bani addu'oin? Waye zai yadda da abubuwan da nake ji a jikina na ciwo, ba tare da ya ƙaryata ni ba?" Tuni malamai suka cika ofishin, kowa da abin da yake faɗa, wasu na kuka domin mutuwar ta dawo musu sabuwa. Da yawa ba su san ya so ya auri Nana ba sai yanzu.
An daɗe ana rarrashin Nana, da yi mata nasiha, ba a taɓa yi wa Nana mutuwa mai shiga jiki ba sai a wannan lokaci, Alkhairinsa kawai take tunawa.
Halin da take ciki, bai hana kunnuwanta jiyo maganganun wasu malaman, su na cewa yayanta ake nema ruwa a jallo shi ya kashe Auwwal. Sauti komai ƙanƙantarsa Nana na iya jiyo shi, wasu lokutan da haka take gane ƙaisar na daf da ita.
Malam Nura ya saka ta a gaba, ya tafi raka ta gida, suna tafe yana yi mata nasiha.
A ƙofar gida malam Nura ya yi mata sallama, ta shiga cikin gida tana taku da ƙyar.
Ko sallama ba ta iya yi ba, ta nufi ƙofar ɗakinsu, ta ga an saka tsumma an ɗaure ƙofar ɗakin. Ta ɗauki jakar da ta dawo da ita daga gidan sarkin baka, duk da har a wannan lokaci ba ta san mene ne a ciki ba.
Ta fara ƙoƙarin kwance ƙofar ɗakin, jin motsi ya sanya Mama sake fitowa, tana ƙoƙarin nufo Nana tana bala'i. Nana ta ɗago a hankali ta kalli Mama, sai kuwa ta ja ta tsaya, dan ba ta taɓa ganin Nana ta yi mata irin wannan kallon ba. Gani ta yi tamkar walƙiya idanun Nana suka yi. Ta buɗe ɗakin ta shiga ta kwanta.
Aka jima Baba ya dawo, dan yawon neman in da Nana ta yi ya yi. Yana dawowa suka ci gaba da faÉ—a da Mama a kan lallai sai ya fitar da Nana daga gidan.
Nana tana ji Baba ya kira Yaya Atine yana roƙonta. Baba ba ya iya waya sai ya saka ta a hansfree, kuma sai ya ta ɗaga murya tamkar yana magana da aradu.
"Atine dan Allah idan da hali Nana ta zo gidanki, ta zauna kafin a ɗaura mata aure. Rabi taƙi yadda ta zauna da ita, kin san halin da Suwaiba take ciki"
"Wace Nana kuma? Ba tana gidan mai magani ba?"
"Ta dawo ɗazu, wai mai maganin ne ya sallamo ta, kuma ga 'yan sanda sun tafi da Gaddafi a taho da ita, shi kuma Imarana ya gudu neman sa ake yi ana zargin sun kashe wannan yaron da ake ta magana a kansa a radio, wanda ya ƙi auren Nanan"
Nana na jiyo Yaya Atine, kasancewar wayar Baba a ragargaje take kuma China ce ta na cewa "Taɓ lallai Isa Allah ya jarabce ka, wannan masifar duk a gidan ka? To mai magani ma ya kasa ya sallamo ta balle kuma ni, ya zan yi da ita ina ma na ga gurin ajiyeta? Ka yi haƙuri ta zauna a gurinka kafin lokacin bikin nata"
Ya marairaice ya ce "Me nake da shi, ba wani biki aure kawai za a É—aura su tafi, ai kin san ba shi ne da ni ba"
Yaya Atine ta ce "To ai shikenan, amma ka riƙe 'yar ka, ba zan je nima na gogi bala'i ba, dan ni na fara tsorata da al'amuranta"
"Amma yay... Ba ta bari ya gama maganar ba, ta kaste kiran.
"Ka gani ko? Ita ba za ta karɓi bala'i ba, ni kuma a bar ni da bala'i ya ci gaba da kashe mu ba zai yiwu ba"
Sallamar da ake kwaÉ—awa a waje, ya sanya Baba fita, ya tarar da 'yan sada tare da Gaddafi.
ÆŠaya daga 'yan sandan ya ce, "Yauwwa barka malam, zamu tafi da kai station ne"
Baba ya ce "Saboda me?"
"Mun je in da aka ce an kai yarinyar ɗanka ya yi ta raina mana hankali muna yawo, babu wani a gurin nan, kuma ga wanda ya kawo ƙarar ana nemansa ruwa a jallo"
Baba ya ce "Ai bayan tafiyar ku ta dawo"
Gaddafi ya ce "Ta dawo kuma? Ni fa har gurin da muka ajiye mota muka shiga, bamu ga gidan nan ba"
"Wallahi ta dawo, tana cikin gidan nan"
Sai da aka tafi tare da Nana har police station, aka yi rubuce-rubuce sannan aka saki Gaddafi suka taho gida. Tana jin yadda Gaddafi yake rantsuwa shi da sake shiga duk abin da ya shafe ta har gaban abada.
Kwanaki biyu suka shuÉ—e, Nana ko rintsawa ba ta iya yi, sai da ta gwammace dama a gidan sarkin baka ta yi zamanta.
Mama kuma ba su fasa faÉ—a da Baba a kan lallai ya nemi in da Nana zata zauna ba. Dama normally ma ba abinci ake ba ta ba sai an ga dama, yanzu kuwa tun da ta dawo Baba ne ma ya kan bayar a sayo mata kunu ko awarar naira É—ari, shi ma ba iya ci take yi ba, balle kuma yanzu.
Dama ba su fiye shiri da Suwaiba ba, sun fi shiri da Jamila, sai dai a wannan karon tun da ta dawo, babu wanda yake shiga sabgarta, hatta ɗakin da take ba sa shigowa. Tana jin yadda idan aka yi baƙi, ko aka zo duba Nana mama take muzanta ta, tana cewa aljanunta ne suka halaka Auwal, wanda ya fasa aurenta kuma suke ƙoƙarin kashe Suwaiba.
Nana tana ganin yadda wasu daga hudar jikin Nana suka fara warkewa, sai dai wasu ba su fasa zubar da jini ba.
Turaren da Jamila ta kawo mata ta gani a kan tagar su, an feshe fiye da rabi. Ita dai ta san turaren nata ne, amma ta kasa tuna yadda aka yi ta same shi.
Cikin dare ta kasa bacci, ta tashi zaune ta haÉ—e gwiwoyinta ta kifa kanta, har yanzu gani take kamar za ta farka daga bacci, ace mata Auwal bai mutu ba.
Kwanakin nan da aka É—auka kuma, ta gazagata da gaske malam Auwal ya rasu. Tana so ta je ta yi wa mahaifiyarsa ta'aziyya amma ba ta sani ba ko ta santa, ga kuma surutun da ake ta yi a kanta.
"Ya Allah ka yafe mini rashin tawakalli da na yi, na bari ɗimuwa ta sanya ni yin abin da bai kamata mai imani ya yi su ba. Ya Allah Auwal bawan ka ne, mai kwaɗaitar da al'umma bin ka da manzonka, mai hidima ga addini, mai ƙaunar Manzon Allah ma'abocin Alqur'ani ya Allah ka yafe masa ka yi masa rahama" ta yi maganar kuka yana ƙwace mata.
Dariyar da ta ji ne, ya sanya ta ɗaga kanta. Ta ganta a zaune jikin wata bishiyar tsamiya, ita kaɗai ƙwal a daji rana tsaka.
"Iska na wahalar da mai kayan kara, yanzu duk saboda soyayyar ki ka koma haka? Kamar gaske mutumin nan ya riga ya mutu, kuma ba fa wai son shi ki ke yi ba, shaƙuwa da tausayi ne a tsakanin ku" tashi ta yi tsaye a fusace tana waiwayen in da za ta ga ƙaisar. Domin kuwa sai a lokacin ta tuna ya nuna mata mutuwar malam Auwal, kuma ya taɓa alwashin kashe Auwal ɗin, amma da ta tashi daga baccin, a wancan lokacin sai ta manta da komai.
"Kai ne ka kashe shi ko?"
"Idan zan kashe shin ne zan soka masa wuƙa? Kwanansa ne ya ƙare ba zan iya kashe shi ba ai, ni ba na kisan kai sai an dame ni, kamar yadda Sarkin baka ya taɓo ni, nima na taɓa shi wataƙila na karya alkadsrinsa wannan maitar wataƙila ita ce ajalinsa"
Cikin matsananciyar damuwa Nana ta ce "Kenan kashe shi za ka yi? Wai kai wani irin halitta ne azzalumi mara imani? Duk wanda na mu'malanta sai ka cuce shi?"
Ƙaisar ya ce "A'a ni ba na taɓa kowa sai ya taɓa ni. Ba ya fara lallaɓa ki ki sadaukar masa da ni ba? Ba ki yi tunanin ta wace hanya zai yi amfani da ni ba, kawai saboda ki rabu da ni, ki ka amsa masa kuma ke ba ki san ya ake sadaukarwar ba, ki ka amsa. Tabbas ya shiga gona ta ni kuma na shata masa layi" yayi maganar yana bayyana a gabanta.