← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 32

Sashe 4

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Zailani ya tattara hankalinsa, ya gyara zamansa ya ce "Malam Gambo to tayaya zan gane su, kuma a ina za a same su, ko nawa ne zan bayar a samo"

"Ba samo su za ayi ba, ka samu mace mai ɗaya daga cikin waɗannan burujan, ka kwanta da ita, zaka samu buɗi ta in da ka zata da in da baka zata ba, taurarinta za su haskaka naka da suke ƙoƙarin disashewa, sannan za ta ɗauke wannan wahalar da zaka sha, kafin ka cimma muradinka"

Ya jinjina kai cike da gamsuwa ya ce "In dai mata ne gasu nan kamar jamfa a jos, tayaya zan gane wadda ka ke nufi?"

Malam Gambo ya numfasa ya ce  "Wadda namiji bai taɓa kusanta ba ake so, kuma idan aka samo ta sai na duba ranar sa'ar burujanku. Kuma ba a fuska za a gane mai irin tauraron da nake faɗa ba. A samo mai suna Nadiya, ko ɗausiyya, ko badariyya"

Alhaji zailani ya ce "Ni yanzu malam ina zan samo waÉ—annan sunayen?"

"Bincikawa za ka saka ayi, ko Asma'u ma zai yi, amma shi ma da sharaÉ—i, idan aka samo É—in sai na lissafa adadin sunanta da na mahaifiyarta na tabattar da haÉ—uwar aikin"

"Shikenan malam, in sha Allah zan yi iya ƙoƙarina, zan samo in sha Allah, ga wannan ba yawa" yayi maganar yana ajiye masa kuɗi a kan shimfiɗarsa.

*****

Ummi ce ta kalli Nana a ɗan fusace ta ce "Wai nuƙu-nuƙun me ki ke yi ne haka Nana?"

"Wallahi Anty ummi ba na son zuwa wurin maganin nan ne, idan ki na da niƙab ki bani na saka, kar na je wanda suka sanni su ganni"

Sheƙeƙe ummi ta kalli Nana ta ce "Au to sai me, ba neman lafiya ki ka je ba, duk wanda ya ce ya sanki shi uban me ya kai shi? Ki wuce mu tafi dan Allah"

Jiki a sanyaye Nana ta bi Ummi, sai dai gaba ɗaya ranta babu daɗi, sai dai ta wani ɓangaren tana ƙarfafar zuciyarta a kan wataƙila ta dace da maganin.

Maƙil suka je suka tarar da gidan mai maganin, tamkar ana rabon gafara, mata ne suke ta shiga suna fita.

Suka samu wuri suka zauna, wasu a shigo da su a rirriƙe, wasu kuma da ƙafafuwansu. Ga manyan mata masu shigar alfarma da kuma yaku bayi.

Wasu na ta tumamin iskokai, wasu na kwancez Nana dai ta raɓe  ta yi shiru a gefen ummi, kasancewar Ummi ba halinsu ɗaya da Nana ba, tuni ta saki jiki suna hira da matan wurin, wannan ta ce matsalar yara ce ta kawota, wannan ta ce matsalar miji, wasu kishiya wasu larura, wasu su ce mayu ne suka kama su, wasu kuma matsalar rashin mijin aure ne ya kaisu.

Nana ta din ga nazarin matsalolin daki-daki, ita a tunaninta matsalar rashin lafiya ce kawai za ta kai mutum wurin mai magani, wadda suke samun saɓani da miji maganin me za a bata, ban da ta kai wa Allah kukanta?

Ummi da wayo da dabara, da iya daÉ—in baki da hira, ta yi wa matan nan wayo, ta ce Nana zata shigar a gani ba ta da lafiya, kwananta uku ba ta magana, kasancewar tun da suka zo ba ta ce uffan ba.

A tsanake yake ƙare masa kallo, yadda ya zauna ya tanƙwashe ƙafafuwansa, yake ta wasa da yatsun hannunsa, yaƙi ɗagowa su haɗa ido.

Ya mayar da idanunsa kan Habu, da yayi shiru yana jiran bayani daga bakin mutumin.

"Wannan ciwon nasa gaskiya ba zan ɓoye maka ba, idan na matsa ni zan shiga matsala, sai dai ku bincika wani wurin"

Cikin damuwa Habu ya ce "Yanzu babu yadda za ayi ace ko sunansa ya tuna? Ya san duk wani abu da ya shafi rayuwar yau da kullum, amma ya manta duk wani abu da ya shafe shi"

Mutumin da yake zaune a kan sallaya,  "Ka san wa ka kawo mini kuwa? Anya ka san waye?"

"Na sani" Habu ya amsa cike da ƙwarin gwiwa, cikin gurɓatacciyar hausar sa"

Mutumin yayi murmushi ya ce "Ka san dai abin da ka sani, ka bar shi a haka kawai kar ka matsa sanin abin da yake a ɓoye" jiki a sanyaye habu ya kalle na zaunen ya ce "Tashi mu tafi" ya yinƙura ya tashi, ya tsaya ya  kalli malamin ya saki murmushi ta cikin rawaninsa suka fice.

Babu tsammani Nana su na tsaye a ƙofar shiga wurin mai magani, wasu mutane suka fito, ƙafafuwansa kawai ta kalla ta ji jikinta ya saki, zuciyarta ta tsinke ta sulale za ta faɗi a wurin, Ummi ta riƙe ta da sauri tana salallami.
A hankali Nana ta bi bayansa da kallo kasancewar ya riga ya wuce, zuciyarta ce ta raya mata ta bishi da gudu ta ga waye, daina ganin kowa ta yi sai itakaɗai a cikin sahara, sai kuma shi wannan mutumin da ba ta ga kowaye ba, yana tafe yana jan akalar raƙumi ya yi nesa da ita, tana hango shi a can nesa sai kuma manyan sawayen raƙumin da nasa.

"Nana" ta ji muryar ummi a kunnenta, ta buÉ—e ido ta kalle ta a hankali ta kalleta.

"Sannu Nana kin tashi" ba ta amsa ba ta É—aga kai ta gansu a gidan Ummi.

"Anty yaushe muka dawo?"

Ummi ta ce "Hmm tun É—azu, ai tun kafin mu shiga wurin mai maganin, ki ka sume, ya ce manyan dakarun aljanu ne a kewaye da ke, mu na shiga ya gansu"

Cikin mamaki Nana ta ce "Ya ga su wa?"

"Aljanun mana" ta bata amsa cike da ƙwarin gwiwa.

"Dama mutum yana iya ganin aljani a suffarsa?"

"Ban sani ba, tambaya dawanau, yanzu ga magunguna nan da hayaƙi kowane zan nuna miki yadda za ki yi amfani da shi, ki ci abinci muje na raka ki gida" Nana ta jinjina mata kai kawai, amma bakinta akwai tarin tambayoyi.

Da yamma Ummi, ta taso Nana a gaba domin ta rako ta gida. Ko da suka je gidan, mamaki ne ya cika Nana, ganin an zube kayan aikin gini  a ƙofar gidansu, a iya tunaninta Baba ba shi da wata hanyar da zai samu kuɗaɗen da za ayi musu wannan gyaran.

"Nana, haka gidan ya koma? Ummi ta yi maganar cikin mamaki.

"Eh, sai ma kin shiga, rijiya ta haÉ—e da masai, amma na ga an kawo kayan aiki ban san a ina aka samo su ba"

Da haka suka shiga gidan da salallama, Suwaiba da take wanke-wanke ta ɗago ta kalle su, ta ce  "Too yau kuma Allah ya yi miki dawowa daga yawon kenan?"

Ummi ce ta ce "Wane irin yawo kuma?"

But Mama ta fito daga É—aki ta ce "To ina ta tafi idan ba yawon ba? Wa ta gaya wa za ta je wani wurin? Kwana biyu babanku ya hana mu sakat, saboda ba a ganta ba, ana ta cigiya a unguwa, dama na gaya masa wani wurin ta yi"

Har Ummi ta É—auki numfashi za ta yi magana, Baba ya yi sallama.

Suka amsa masa baki ɗaya, baki sake ya bi Nana da kallo, ya ce "Nana daga ina ki ke? Ina ki ka tafi baki gaya mini ba? Ko wurin uwartaki da ba ta san muhimmancin ki ba ki ka wanke ƙafa ki ka tafi?"

Ummi ta girgiza kai ta ce "Haba Baba, dan Allah ka tsaya ka ji mana, ka san halin da take ciki na rashin lafiya, shekaranjiya na je ɗaukko yara daga makaranta, ina komawa gida na tarar da ita, a baje a ɗaki ƙafafuwanta duk jini ko takalmi babu, ba ma ta cikin hayyacinta. Ni kuma wayata ta lalace, babansu kuma ba ya gari, shi yasa ban kira na sanar muku ba.

Mama ta yi farat ta ce "Wallahi ƙarya ne, ki na nufin tun daga nan ta tafi gidanki a ƙafa? Ƙarya ki ke yi Ummi, ki faɗi gaskiya idan ma, yawon ta zubar ta tafi ki ke kareta"

A fusace Ummi ta ce "Allah ba zai nuna mana mai yawon ta zubar a cikin zuriyarmu ba, baƙin bakinki ya faɗa miki kanki da 'ya'yanki.....

"Ke ummi rufe mini baki kafin na kwaÉ—e ki" Baba ya katse ta cikin fushi.

Ya É—ora da cewa "Mara kunya wuce ki tafi gidan ki, Allah ya ba da lada"

Nana ji ta yi tamkar ta bi bayan Ummi su koma tare, saboda karɓar da aka yi musu, ko arzikin abin zama ba su samu ba, balle a bawa ko ummin ce ruwa, haka ta kasa magana ta bi bayan ummi da kallo yadda ta fita a fusace.

Ayshercool
08081012143
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g/9223372036854675807

BUZU

Ayshercool

YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION (YOTA/002)

BRIGHT PENS 3rd BATCH.

P3

Nana ta tsaya jiran abin da Baba zai ce, bayan fitar ummi, amma ba ta ji ya ce komai ba.

"Wai haka zaka ƙyale yarinyar nan, ba zaka tuhumi ina ta je ta kwana biyu ba?" Mama ta yi maganar tana tsare Baba da ido.

"To rabi ya ki ke so na yi, kin san a cikin larura take, ni wannan larurar ta ta ta ishe ni, Allah ya kyauta kawai"

Tun da Baba ya faÉ—i haka, mama ta dasa mita da bala'in baya ganin laifin Nana.

Nana kuwa É—akinsu ta shiga, tana jin yadda maganganun mama ke ratsa zuciyarta, da sanya mata wani irin raÉ—aÉ—i da zafi a cikin zuciyarta.

Haka ta wuni sukuku, ba wanda ta kula ta ƙule a ɗaki kamar yadda ta saba.

Sai dai wunin ɗakin nan, ya ƙara sanya zuciyar Nana a cikin ƙunci, haka kurum kewa da son ganin mahaifiyarta ya bijiro mata.

Sai daf da magariba Jamila ta shigo gidan, ta ya da zango a tsakar gida, da abin da ta zo da shi daga gidan uwar É—akinta.

Ƙamshin abinci har cikin ɗaki in da Nana take, ga yunwa tana ta sakaɗar cikinta, kamar ba ta taɓa cin abinci ba, haka take jin cikinta.

A lokacin ta tsinkayi hirarsu, wai ashe mijin maman khairat, uwar É—akin Jamila, shi ne ya É—auki gabarar gyara musu gidan.

Tun tana fahimtar hirar ta su, har ta faÉ—a duniyar tunani, ba ta iya jin me suke cewa.
Chapter 4 · 0% Book details