← Book details Buzu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 32

Sashe 19

Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wallahi ko ki rufe mana baki, ko na yi miki mugun duka, dan abin naki zunzurutun iskanci ne na za ki hana mutane bacci ba". Amma a banza dan ba ta san ma yana yi ba, sai wani irin gurnani da take yi kamar an yanka sa.

Ya nufi wurin da aka sayo ice aka ajiye, ya samo wata sanda dai-dai lokacin ta fito daga É—akin za ta fita waje.
Babu tausayi babu imani, ya fara shirga mata icen nan a jikinta.

Nasiru tun da Nana ta fara wannan gurnanin, ya fita majalissar da ya ga Imarana, ya ce masa ya zo ya ga abin da Nana take yi, zuwansu yayi daidai da dukan da Gaddafi yake yi wa Nana.

Imran ya hankaɗe shi ya ce "Kar ka sake dukanta, wani irin azzalumi ne kai, da wanne za ta ji? Dama abin da ku ke yi mata kenan" hankaɗe shi Gaddafi ya yi yana ƙoƙarin sake dukan Nana, Imran ya ɗaukko ƙaton itace a murhu yana wuta yayi kan Gaddafi zai jirga masa gadan-gadan.
Da ƙyar Baba ya raba faɗan ya ce "Gaddafi na ce ka daina dukan yarinyar nan, tun da ka ga nima na saduda ba ciwon ƙarya take yi ba, ba ta da lafiya da gaske. Kuɗin auren da na ce yaron nan Saleh ya kawo, su nake jira mu kaita can in da ka ke ba ni labarin nan, amma tun da abin ya kai haka ma dole ko rance ayo a kaita wannan jaraba ta ishe ni.
Kai kuma jarababbe ɗan nema, kai ba aljan ba amma ka fi sheɗan shaiɗanci,  wallahi aljanun Nana sun fiye mini hatsabibancin ka nesa ba kusa ba Imrana."

Imran bai kula Baba ba, ya durƙusa ya ɗago Nana, matsanancin tausayinta ya mamaye zuciyarsa.
Suka ci gaba da hayaniyarsu, shi kuma ya mayar da hankali kan tofa wa Nana ayatul kursiyyu, a fuskarta.

Miƙa ta yi a hankali, sai kuma ta riƙe hannunsa tana ajiyar zuciya.

"Nana"

"Na'am Imran, ka tsaya a kusa da ni, tsoro nake ji"

"Na sha gaya miki, ki daina jin tsoro, kar wani abu ya din ga ba ki tsoro. Babu wani abu da ya isa ya cutar da ke sai abin da Allah ya ƙaddara zai same ki" Ta jinjina masa kai, tare da ƙara jin ƙwarin gwiwa.
Ya ɗaukko ruwa pure water ya bata ya ce "Yi bismillah ki sha ruwa" ta karɓa ta yi bismillah ta fara sha.

Ta kammala sha, ta ce "Alhamdilillah"

"Amma Nana ki na addu'a kuwa?"

Ta jinjina masa kai ta ce "Eh"

"Lamarin nan yana damuna Nana, da kafin na tafi kamar abin ya lafa miki"

"Eh, tun da aka saka mini rana ta farko abin ya dawo, har zuwa yanzu"

Imran ya ce "Ba komai akwai Allah"

"Imran" ta kira sunansa a hankali.

Ya amsa da "Na'am"

"Tun da ka tafi, ka je wurin babarmu ne?"

Tsuke fuska ya yi ya ce "Ai ni da sake zuwa in da take har abada"

Cike da damuwa Nana ta ce "Saboda me? Mahaifiyarmu ce fa, ni ko a waya ba na samunta, ga Baba ya hana duk wata hanya da za ta sada ni da ita"

"Nana, ki yi focusing a kan rayuwarki. Duk duniya babu wanda dan ya cire hannunsa daga rayuwarki za ki kasa rayuwa. Uwa na haifar jariri ma, ta mutu a take ya girma ya rayu, balle ke da wayon ki da girman ki, ki ci gaba rayuwarki kawai. Ta fi son mijinta da yaran da ta haifa yanzu a kanmu, ban da haka ai ya kamata ta waiwayo mu, ta ji halin da muke ciki, amma tana can tana rayuwarta cikin kwanciyar hankali"

Hawaye na bin idon Nana ta ce "Ba haka ba ne Imran, babarmu tana sonmu, Mijin da take aure ne ba ya son mu je in da take, nan ma idan ta zo ka san Baba wulaƙanci zai yi mata".

"Kin ga mu bar wannan maganar, ki je ki yi alwala ki nemi wuri ki kwanta kawai" fafur Imran ya ƙi yarda su ci gaba da maganar.

*****

Buzaye ne su uku, zaune a cikin jeji, mai É—auke da manyan bishiyu, iska sai kaÉ—awa take yi. Dukkaninsu sanye da rawani. ShikaÉ—ai ne a gefe, ya zuba shayi a kofi , yana sha yana lumshe idanunsa, alamar yanayin yana yi masa daÉ—i.

Cikin damuwa Habu ya ce "Souley, na rasa abin yi, kaina ya kulle fa"

Souley ya ce "Nima hakan take Habou, anya ba za ka mayar da shi Nijar ba, tun da an kasa samun magani?"

Da sauri Habu ya girgiza kai ya ce "A'a, ba zan mayar da shi Nijar ba yanzu, akwai wani mai magani da na ji labari, har kwantar da mutane yake yi, ina jiran cikakken adireshin gurin ne, shi ma za mu jarraba"

"To ai ni tsoro nake ji ne Habou, kar a garin yawon neman maganin nan a samu mushikila, ka na kallo kullum abin nasa babu wani ci gaba, duk in da aka je sai dai ace mana babu mafita. Kawai ka tsinci mutum ka yi ta wahala da shi, ka je in da ka tsinto shi ka mayar da shi kawai mu huta"

Habu ya kalli Sule cike da takaici, kawai ya tashi, ba tare da ya sake tanka masa ba ya nufi in da É—ayan yake.

"Taso mu tafi" yayi maganar yana kallonsa.
Sai dai bai motsa ba, ya ci gaba da tsiyayo shayin da yake cikin buta yana sha.

Habu ya miƙa masa hannu, ya sake cewa "Taso mu tafi" sai a lokacin ya ɗaga kai ya kalli Habu, ya ƙarasa shanye shayin, ya tashi tsaye.

Sule ya ce "Habou kalli fa ko magana a 'yan kwanakin nan ba ya yi, sai a shafe kwana da kwanaki bai ce komai ba, haka zamu ci gaba da wannan aiki haka?" Habu bai tanka masa ba, ya riƙe hannunsa suka yi gaba.

*****
Dawowar Imran gidan malam Isa, ya sanya kullum cikin rigima ake da shi, kullum sai sun yi faÉ—a da Baba ko Gaddafi.
Ba ya kwana a gidan, amma garin Allah na wayewa zai zo. Nana ta samu afuwa sosai da dawowar Imran. Saboda ba ta taɓa zama da yunwa, sau ukun nan sai ta ci abinci a rana.
Sai dai ta kasa tunanin Auwwal, tun ranar da suka rabu, ba ta sake ganinsa ba.
Ga Baba ya fara addaba mata da maganar Saleh, wanda ko sunansa ba ta ƙaunar ji.
A can makaranta da take koyarwa, mahaifin ɗalibinta Muhsin, ya fara damunta, kullum ya zo ɗaukar Muhsin, sai ya ce zai rage mata hanya. Ga shi ba ta da damar tafiya, sai an gama zuwa ɗaukar yaran gaba ɗaya, kuma kullum Muhsin ne ƙarshen zuwa ɗauka.

Yau bayan ta dawo daga islamiyya, Yamma liƙis, Baba ya shigo fuskarsa ɗauke da fara'a ya ce "Ke Nana, ki je ga Saleh can a waje yana jiranki" gaban Nana ya faɗi.

Imran ya tashi ya nufi hanyar fita, Baba ya ce "Kai malam ba kai fa kai na ce ba"

Ya waiwayo ya kalli Baba ya ce "Ni akwai gurin da zan je" ya fice.

"Ke kuma Nana ba magana nake yi miki ba?"

Jiki a sanyaye ta ce "Ina zuwa, kaya zan canza"

Imran kuwa yana fita ya tsaya ya ƙarewa Saleh kallo, ya ce "Kai ai kamar na sanka a gidan Ummi"

Saleh yayi murmushi ya ce "Ba kama ba ce ba ni ne ai"

Imran ya ce "Bala'i ashe idan na je neman aure nima za a bani, duk da ana ganin ba ni da saiti. Kai yanzu saboda ka raina wa kanka hankali gurin ƙanwata za ka zo neman aure a haka? Kalli wani shegen wando a jikinka ba ka san saukakkiyar Alqur'ani ba ce, kuma mahaddaciya ba?"
Saleh yayi saroro yana kallon Imran.

"Eh kalle ni da kyau, wallahi sai na je har gida na kasa wa Ummi warning, mai ku ka mayar da Nanan, wallahi ta fi ƙarfinka me za ta yi da ɗan jagaliya kamar ka?"

"Saboda na zo ƙofar gidanku neman aure, ka ke gaya mini abin da ka ga dama?"

Imaran ya ce "Malam gaskiya nake gaya maka, ba ka cikin irin mutanen da Nana za ta so da aure, a tsarinta tana son mutum mai kamala da sanya manyan kaya kuma...

Shiru ya yi, ganin Nana ta fito fuskar nan babu walwala.

Maimakon ya tafi sai ya ja ya tsaya, takaici ya hana Saleh magana, a girme ya girmi Imran amma ya tsaya yana gaya masa magana dan ya zo wurin ƙanwarsa.

Ya maze ya kalli Nana ya ce "Gimbiyata barka da fitowa"

Imran ya kwaɓe baki yana jiran me Nana za ta ce. Ta ɗago suka haɗa ido.

"Amma ko za ka bamu wuri mu yi magana" Saleh yayi maganar yana kallon Imran.

"In ba ku guri na je ina? Ka zo wurin ƙanwata zance da crazy jeans, meye banbanci na da kai, da ake cewa ba ni da hankali?. Kai wallahi ba za ayi zancen nan ba, ke koma gida ranar da ya shirya neman aure, yayi shigar mutunci ya zo"

Babu musu Nana ta shige gida, dama haka take so. Baba na ganin ta dawo ya tambayi ko lafiya?.

"Imaran ne ya ce na dawo gida"

"Ki dawo ki yi masa uban me? Idan ba ki yi aure ba zai aure ki ne?"

Ya nufi waje yana faɗa, ya tarar da Imran ya tare ƙofar gida yana cewa Saleh idan gidan ubansa ne, ya ture shi ya shiga da wannan shigar tsiyar.

"Imrana wai ba ka da hankali ne? Meye haka?"

"Baba, wai ya za a É—auki aure a ba wa mutumin da zai zo neman aure, yayi ido huÉ—u da sirikinsa da yagaggen wando, da tarin suma kamar shekararren zakara. Kuma a gaya masa gaskiya Nanan nan fa ba son sa take yi ba"

Baba ya ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, Imrana yaushe ka yi hankalin da ka fi ni sanin dai-dai? Shigar mutum ake dubawa ko halin iya riƙe auren? Ita Nanan ba taimaka mata zai yi ba, tun da ba lafiya ce da ita ba"
Chapter 19 · 0% Book details