Sashe 13
Buzu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ka kwantar da hankalinka, kamar ka aureta ka gama ne, har wani zaɓi take da shi, kai da zaka taimaka mata. Ka manta da ita kawai ka turo a kawo kuɗi"
Saleh ya washe baki ya ce "Allah mutumina"
"To me za a jira, kawai ayi abin da ya dace" Nan ya tsaya suka ci gaba da hira, saboda Gaddafi ma a Lagos yake neman kuÉ—i, kuma su na haÉ—uwa da Saleh sosai.
Sai da suka gama hirar, sannan suka yi sallama, Gaddafi ya shiga cikin gidan, ya dira wa Nana bala'i da cin mutunci a tsakar gida. " 'yar gidan uban waye ke, da za ki hurawa mutane hanci, ke da da za a taimakawa, mahaukaciyar banza da ta wofi. Ki na yawo a kwararo ki na wannan tamɓelen ki hana jama'a bacci, kowa ya san mahaukaciya ce ke a unguwar nan, kin samu ana sonki, amma ki bujire. To wallahi ba ki isa ba dole ki auri Saleh, ki fita ki bar gidan nan ƙila ma rashin aure ne ya sanya ki ke wannan haukan "
Nana ta toshe kunnneta, saboda zafi da tururin da zuciyarta take yi, ji take tamkar ta É—ura masa ashariya, ta rama cin mutuncin da yake yi mata, amma ta din ga maimaita Innalillahi wa innalillahi raji'un.
Baba ne yayi sallama, ya tarar da Gaddafi yana bala'i, da ya tambaye shi ba'asi, ya ji da Nana yake, sai ya karɓa ya ɗora shi ma.
Nana ta rasa wannan jaraba, babu wanda aka tsangwama yayi aure a gidan sai ita, saboda su ga babarsu a gidan, ita kuma ga rashin uwa, ga larura ga shi duk wata hanya da za ta samu mahaifiyarta ko a waya, Baba ya datseta, har yana nema ya yi mat baki.
'meye na damuwa ma, matar da ko in da ku ke ba ta zuwa, ta ga halin da ku ke ciki, balle ki gaya mata halin da ki ke ciki, ta saka ki a addu'a, ko kuma t nema miki magani' wata zuciyar tayi mata tunin, abin da ba ta so, domin in dai tana ire-iren waÉ—annan tunanin, ta na jin zafin mahaifiyarta a ranta.
"Ke Nana, zo ga waya Atine za ta yi magana dake" maganar Baba ta dawo da ita daga duniyar tunani da ta lula.
Gabanta ne ya faɗi, wata sabuwa in ji 'yan caca, ba ta ƙaunar duk abin da zai haɗata da matar nan a rayuwarta.
Ba tare da ta amsa ba, ta tashi ta fita.
Baba ya miƙa mata waya, ta karɓa hannunta na rawa ta saka a kunneta, ta yi shiru.
"Ke ma'u ki na ji na?"
"Eh" ta amsa a cunkushe.
"Dan ubanki sai ki yi mini shiru, ko gaishe ni ba za ki yi ba, har kya yi wa mutane ƙaryar iskancin aljanu, mu da a ka yi gadon bori a gidanmu.
Nana ta yi shiru, tana mamkin yadda jahilci, ya sanya yaya Atine alfahari da harkar shirka, da shi ne musababbin gadar mata da bala'i, kamar yadda mutumin da take mafarki da shi, yake iƙrari.
"Ki buɗe kunnenki da kyau ki saurare ni, ranar asabar ki yi kuɗin mota, ki taho gidana, akwai gidan wani mai magani da zan kai ki. A baki maganin aljanu da na farin jini, aure dole ki yi shi babu fashi, ko shi wanda ba kya so ɗin ko wani daban. Ke wannan baƙin jinin kamar an jiƙa hatimin jaɓa an baki, daga nonon babarki ki ka shawo shi. Mu zuriyarmu farin jini ne da su wallahi, babu mai nauyin jini"
"Yaya atine, idan ni a nonon uwata na sha, su suwaiba a naki nonon suka sha? Tun da Uwar tawa ba ta nan, menene na sakota a zancen ki, koma wani bala'in ne ya same ni, ba duk a dalilin shirka da iyayenku suka yi ba ne, da har ki ke alfahari da ita" ita kanta Nana ba ta san yaya aka yi, suke fita daga bakinta ba, saboda yadda ranta ya ɓaci zuciyarta take tafasa fiye da kima.
"Ma'u ni ki ke gaya wa haka?"
Gaddafi ne ya yi kan Nana, amma Baba ya tare shi, ya ce "Rabu da ita, ka na taɓa ta babu lallai, mu yi bacci mai daɗi a gidan nan, wataƙila ma ba ita ba ce ba, ƙyale ta"
Ta ajiye wa Baba wayarsa, ta koma É—aki.
****
Cike da damuwa Auwwal ya koma gida, 'yar tsarabar da ya yi wa Nana, ya bawa ƙannensa, wani irin kishi ya addabi zuciyarsa, sai dai kuma yanayin kallon da ya ga tana yi wa wanda suke tsayen ne, bai gama gane kansa ba.
"Auwwalu" Umma da ta gama kasa gurasa da naman gabanta.
Ya kalleta ya amsa da "Na'am Umma"
"Magana nake son mu yi da kai ta fahimtar juna. A matsayina na mahaifiyarka".
Ya tattara mata hankalinsa baki É—aya cike da ladabi.
"Ka zo mini da maganar aure, na ce maka ka dakata, ba yanzu ba tukuna. Karo na farko abin da ba ka taɓa yi mini ba, ka kai ƙarata wurin kawunka ƙanin mahaifinku. Ya zo har gidan nan baka nan, mun yi magana ta fahimta da shi sosai na kuma fahimce shi, har ya gaya mini ka gaya masa sunan yarinyar da gidan mahaifinta. Na ce masa to ya ɗan saurare ni. Na zo da kaina na saka ayi mini bincike, shi ma kawun naka na saka yayi ta nasa ɓangaren. To magana ta domin Allah ba zan yadda ka auri wannan yarinyar ba, ashe ita ce wadda ka ke bani labari mara lafiyar nan. 'yan unguwarsu sun tabattar da ba ta da wata matsala sai wannan iskokai, kuma ana kyautata zaton kakaninta 'yan bori ne, ni kuma gaskiya ba zan yadda a ɓatawa tsatsonmu suna ba, a sa a gada wa zuriya masifa ba. Dan haka mun gama magana da shi, shi ma zai neme ka ya kuma yi maka magana. Ya ce mini ya saka wani abokinsa ya yi naka hanyar tafiya Qatar ko Allah ya sa a dace da kyakyawar sana'a. Idan Allah ya sa ka tsaya da ƙafarka ka samu wata yarinyar mai kyakyawar nasaba da lafiya ka aura. Ba cin mutunci ba amma an ce yaran gidan ma galibi su ne suke ciyar da kansu, uban ba ya sana'ar komai, yarinya budurwa kuwa duk in da aka bari ta ciyar da kanta, ai an samu matsala. Dan haka ka cire ta daga zuciyarka" da ƙyar Auwwal ya haɗiye wani abu mai zafi da ya tsaya masa. Mama tana da gaskiya amma idan aka ce waɗannan abubuwan kacokan za a duba a ɗora mata laifi shikenan ba za a aure ta ba kenan? Nan aka zo neman auren ƙamwarsa aka ce ba za a aureta ba, 'yar mace ce, aka yi ta ɗauki ba daɗi kafin auren ya yiwu, amma Umma ta manta da wannan, ita ma tana hango aibun da ba ya cikin jerin abin da zai iya hana aure a shari'a a yanzu".
"Auwalu ka yi shiru, ko baka yarda ba zaka bujire ne?"
"A'a subhnallah, na amince Allah ya zaɓa abin da ya fi alkhairi, amma Umma, da a bar maganar Qatar ɗin nan, idan Nana ce na haƙura amma..
Ta tari numfashinsa ta ce "Ai mun gama yanke hukunci, biyayya ce kawai taka Auwal"
Ya risuna ya ce "Shikenan Allah ya wuce mana gaba" ya tashi jikinsa a sanyaye ya bar É—akin Umma, ya koma shagonsa.
Washegari da safe, ta je gaida Baba, bayan ta shirya za ta tafi wurin aiki, amma ya ƙi amsawa, ya ma tashi ya bar wurin.
Cikin damuwa ta koma ɗakinsu, ta ɗauki jakarta, ta kalli Jamila, da ke ta danna waya ta ce "Jamila, dan Allah ko kin san laifin da na yi wa Baba, ya ƙi amsa gaisuwata?"
Jamila ta ɗago ta ce "Lallai Nana, jiya da ki ka gaggaya masa magana, da shi da yaya Atine, ko har kin manta?" Shiru Nana ta yi, ta fara jin wata ƙara a cikin kanta, ta jingina da bango ta dafe kanta ta ce "Subhnallah"
Jamila ta tashi zumbur, ta ja da baya ta ce "Ya dai?"
"Wallahi Jamila, ban san ya aka yi hakan ta faru ba, da na tashi daga bacci, tunanin abin nake yi kamar mafarki ba a gaske ya faru ba, gaba É—aya na kasa gane kan rayuwata, amma shikenan" kawai ta fita daga É—akin, ta saka takalmanta ta fice.
A ƙofar makarantar, danƙareriyar motar ta yi parking, gilasanta baƙaƙe ne ƙirin, ba a ganin wanda yake cikin motar.
Yaro ne É—an shekaru uku, ya fito daga cikin motar, ya zura hannunsa ya É—aukko akwatin abincinsa, bai tsaya rufe motar ba ya nufo wurin da Nana take tsaye, yana washe baki cike da murna.
Sakin fuska ta yi, ta ƙarasa ta ɗauke shi, ta ɗaga shi tana murmushi. Sai dai yayi shiru yana kallonta, ganin alamun damuwa a fuskarta.
Ta shiga da shi cikin makarantar, ta fara tafiya da shi aji, in da take ajiyewa ɗaliban nata, kwanukan abincinsu, ta juyo za ta kama hannunsa su fita, amma ya ƙura mata ido.
Cikin harshen turanci ta ce "Muhsin let's go" (Muhsin mu tafi)
"Anty sorry" (Anty ki yi haƙuri) ya furta cikin damuwa.
Kallon sa tayi ta ce "Meyasa ka ke bani haƙuri?"
"Anty waye ya dake ki, ki ka yi kuka?" Ya faɗa cike da yarinta. Haɗiye hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata tayi, ta ce "Atishawa na yi, mu tafi assembly ground"
Ko da suka je wurin assembly, an yi tsit ana addu'a, amma É—alibanta na ganinta, suka fara tsalle, su na kiran sunanta.
"Anty, ko ki saka 'ya'yanki su yi mana shiru, ko ki ja su ku tafi" vice principal ya gargaɗeta. Cikin hikima ta sanya yaran yin shiru, yaran da take jin ƙaunarsu, har cikin zuciyarta.
Lokacin tashin yaran, duk an zo an É—auke su, saura muhsin da ta biyewa, take yi masa lilo, kafin a zo É—aukarsa.
Daga ita sai shi a harabar wurin nishaÉ—in yara, ta É—ora shi a wannan lilon ta sauke shi a wancan.
"Laa Anty kin ga Daddy" yayi maganar yana nuna bayanta.