← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu da tafiyar Amjad, ayrah ta shiga damuwa Saboda rabon ta da shi, tun lokacin da ya kira ta yace mata ya ƙariso airport basu ƙara magana ba, bayan yace mata idan ya isa zai kirata amma shiru har yanzu, yau ma kamar kullum tana cikin gida tana shara taji ana sallama daga waje, har zataje sai ga wani yaro ya shigo, haka kawai taji zuciyar ta na tsinkewa, yaron yace wai abokan me gidan ne suna so abasu izinin shigowa tare da me gidan suke, Ayrah tace" kace su shigo". Tana faɗan haka mama ta fito hannun ta da taburma tace jeki shimfiɗa musu, a ƙofar ɗakin Abban ta, ta shimfiɗa musu suka shigo da sallama tunda ta ɗago kai ta kalli Abban su, sai kuma ta tsaya kamar andasa ta agurin with shock, hawaye ne suka fara binƙuncin ta, mama tace"bissimillah ku ƙariso ". Ƙariso wa sukayi suka kwantar da Abban nata da babu abinda yake motsi a jikinsa sai ido, ita kuwa Ayrah banda hawaye ba abinda take , sai kuma ta kalle su tace "ina wunin ku". Sukace" lafiya". Bayan sun gaisa da mama suka sanar mata cewa faɗuwa yayi suna cikin aiki, su ba 'yan garin nan bane kwanan su biyu suna neman garin su kafin aka samu wanda ya sanshi, mama ta musu godiya suka masa fatan Allah ya bashi lafiya tare da ajjiye musu kuɗi dubu 20 akan taburmar suka fice, Ayrah kam ji tayi duniyar ta mata duhu yanzu Abban tane ya dawo haka "innalillahi wa inna alaihi raji'un". Ta furta a bayyane, ta kalli mama tace" mama dan Allah mu kai Abba asibiti". Mama tace "mayya wato kinga kuɗin nan ko to wallahi ko biyar daga ke har ubannaki babu wanda zaici a kuɗin nan". Ayrah ta tsaya tana kallon mama hawaye na bin ƙuncinta........

*🥀BAYAN DUHU🥀*

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*Mer'eesher*✍️

FEATURE WRITERS ASSOCIATION...

9......

Mama bayan tagama magana ta kai hannu ta kwashe kuɗin, Ayrah tana zaune a gurin can dai ta miƙe, ta ɗau hijabin ta ta fice, ta nemo maza suka zo suka saka mata Abban a ɗakin sa, ranar haka ta wuni damuwa ta mata waya duniyar gaba ɗaya ta mata zafi, da dare ta fita taje gidan su, Sa'adatu ta sanar mata halin da ake ciki tare suka dawo, tana kallon Abban nata, Sa'adatu tace "sannu Abba Allah ya baka lafiya". Basu sa ran zai basu amsa ba kuma hakan ne tafaru, Sa'adatu ta kalli Ayrah tana jin tausayin ta a zuciyar ta, saboda tasan duk wahalar da take sha yanzun mai sauƙine saboda mahaifin ta yana raye, amma ranar da akace babu ran Abba batasan yadda rayuwar Ayrah zata kasance ba, kamar bazata yi magana ba sai kuma tace "ƙawata gaskiya bai kamata abar Abba haka ba,gobe a kai shi asibiti". Ayrah tace "Nima nayi tunanin nan Sa'adatu Allah ya kaimu goben sai muje". Sa'adatu tace "Ameen Allah ya bashi lafiya". Ayrah ta amsa da "Ameen". Daga haka su ka fice daga ɗakin ta raka Sa'adatu bakin ƙofa sannan ta dawo, ranar a ɗakin Abban nata ta kwana, da asuba ya tashi ya zura mata ido yana kallon ta, tana kwance akan taburma a ƙasan yana ta kallon ta, can ta miƙe tana kallon sa, tace "Abba na maka alwala ne". Ya rufe ido ya buɗe , ta tashi ta fita bata daɗe ba sai gata da buta da baho, haka dai ta lallaɓa ta masa alwalan, sannan ta taimaka masa ta saka pillow a bayan sa ta jinginar da shi, sannan ta fita itama tayo alwala ta dawo ta tada sallah, bayan ta idar ta gyara masa kwanciyar sa , sannan itama ta kwanta, ba'a jima ba bacci ya sace ta, ƙarfe 7:30am ta tashi ta fita, ɗaura abinci bayan ta gama, tayi wanke-wanke tana cikin shara Sa'adatu ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Ayrah ta amsa mata sallamar tana kallon ta, Sa'adatu tace "sannu da aiki ya jikin Abban?". Ta faɗa yayinda take shiga ɗakin da Abban yake, Ayrah tace "da sauƙi ". Sai kuma ta ajjiye shawarar ta bi bayan Sa'adatu, Sa'adatu ta shiga bakin ta ɗauke da sallama tana ganin Abban tace "Allah ya baka lafiya Abba". Da ido kawai yake kallon ta, amma bazai iya magana ba, Sa'adatu tace" Ayrah kishirya barinje na nemo mana me napep ya kaimu asibitin, Ayrah tace"to ƙawata nagode ". Sa'adatu ta fita daga gidan, bayan wani lokaci ta dawo da me napep, Ayrah taje ƙofar ɗakin mama, tace "mama ga me napep yazo ki fito mu kai Abba asibiti". Mama daga cikin ɗakin tace "kuje kawai zan samo ku". Ayrah bata ƙara ce mata komai ba ta wuce suka tafi ita da Sa'adatu da kuma mama,

Basu daɗe ba aka karɓe su a asibitin aka shiga da shi, aka fara dubashi, sukawa suna tsaye suna jira, can likitan ya fito ya kalli mama, yace " ya kuke da marar lafiyan". Mama tace "ƙanwar sace ni wannan kuma 'yar sace". Yace "ku biyun ku sameni a office". Yana faɗan haka yayi wucewar sa, jiki babu ƙwari mama da ayrah suka nufi office ɗin nasa, Ayrah babu abinda da take idan ba addu'a da fatan Allah ya bawa baban ta lafiya ba,

Da sallamar su suka shiga office ɗin likita ya amsa musu yana kallon su, da ido yace "mama bissimillah ki zauna". Ya faɗa yana nuna mata kujeran gaban table ɗin, zama tayi ita kuma Ayrah ta tsaya, likita ya nuna mata ɗayar kujeran yace "bissimillah ƙanwata". Zama tayi zuciyar ta cike da fargaba, tace " likita dan Allah meyake damun Abba na?". Yace "sunana Kamal". , Ayrah dai batace komai ba ta sunkuyar da kanta, tana ƙoƙarin hana wayen da suka taru a idon ta zubowa, mama tace "Kamal meyake da munsa". Dr. Kamal yace "abinda nake so da ku, ku kwantar da hankalin ku"
Mama tace "likita Meyasa baya magana baya iya motsa jikin sa?". Kamal yace " Ya samu mummunan bugun jini da ya shafi wani muhimmin sashe na ƙwaƙwalwa da ake kira brainstem. Wannan sashen ne ke isar da saƙonni daga ƙwaƙwalwa zuwa sauran sassan jiki ".

Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ,Shin yana jin mu ne ko baya jin mu idan mukayi magana a inda yake?"
Kamal Yace "Eh. Yana jin duk abin da kuke faɗa. Yana ganin ku. Yana gane ku. Yana tunani kamar kowane mutum. Amma lalacewar da ta samu ta hana jikinsa amsa umarnin ƙwaƙwalwarsa."

Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ". Ayrah dai tayi shiru takasa magana hawayen da take riƙewa ne suka fara zubowa, ta saka hannun ta, ta share,

Mama tace " likita to menene mafita".

Likita"Hajiya, a wannan lokaci babu wata mafita guda ɗaya da zan ce idan mun yi ta komai zai daidaita. Amma akwai abin da za mu yi domin mu ba shi damar samun sauƙi.
Na farko, za mu ci gaba da ba shi duk magungunan da suka dace.
Na biyu, za mu fara masa physiotherapy tun da wuri, domin kada tsokokinsa su daskare.
Na uku, za mu tabbatar yana samun abinci mai gina jiki, kuma idan ba zai iya haɗiye ba, za mu riƙa ciyar da shi ta bututun da aka tanadar.
Na huɗu, za mu riƙa bibiyar yanayinsa kullum. Idan Allah Ya sa ya fara samun ko da ɗan motsi ko damar magana, za mu ƙara masa wasu nau'ikan jinya".

Mama tace "Likita... shin kana nufin haka zai iya kasancewa har ƙarshen rayuwarsa?".

Dr. Kamal ya sauke numfashi Yace "Hajiya, akwai yiwuwar hakan. Amma akwai kuma marasa lafiya da suka fara samun sauƙi bayan watanni ko ma shekaru. Ba za mu yanke ƙauna ba, amma ba zan yi miki alkawarin abin da ba na da tabbaci a kanshi ba."

Maman tace: "To me za mu yi yanzu?"
Dr. Kamal yace"Ku kasance tare da shi. Ku riƙa yi masa magana. Ku yi masa addu'a. Ku ƙarfafa masa gwiwa. Mu kuma a matsayinmu na likitoci za mu yi duk abin da ilimin likitanci ya ba mu damar yi. Sauran kuma muna roƙon Allah, domin Shi ne Mai ba da lafiya."

Mama tace" mun gode likita amma kana ga aikin zai ci kamar nawa?".
Kamal Yace" banace ba mama amma dai ku ta nadi kamar million 3 zuwa 5 haka".

Mama tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un likita wallahi bamu da wannan kuÉ—aÉ—en".

Likita Yace "aikuwa ya kamata Ku ƙuƙuta ku samu dan yanzu ma zaku fara biyan 100k kuɗin CT scan (computed tomography). Da muka masa sai kuma kuɗin gado 30k ".

Mama tace "shikkenan likita mun gode insha Allahu zamuje mu biya a inda ake biya".

Ayrah kam tana zaune a gurin ta kasa motsi mamace ta kama hannun ta, suka fita tana janta, hawaye kawai Ayrah takeyi tana bin duk inda mama take janta, a haka har suka ƙariso inda Sa'adatu take zaune ta tafka tagumi,

Tana kallo su, ta taso da sauri tayo kansu tana tambayar su, me likitan yace?,

Mama ce ta kalle ta, tace " ku zauna da Ayrah barin je na biya kuɗin". Tana faɗan haka ta sake hannun Ayrah, Ayrah ta zauna a gurin hawaye na bin ƙuncinta magan-ga nun likita suna dawo mata kanta,

Sa'adatu ta dafata tace "Ayrah kiyi hakuri kinji Abba addu'a yake buƙata ba kuka ba".

Ayrah ta É—ago kanta ta kalli Sa'adatu sai kuma ta maida kanta ta haÉ—a kai da gwuiwa taci gaba da kukanta,
Bayan wani wani lokaci likitan yazo ya musu rakiya zuwa É—akin da Abba yake yanzu,

Suka shiga suna kallon su, shima yana ta binsu da kallo, mama tace "sannu Mallam Allah ya baka lafiya ". Su Ayrah suka amsa da "Ameen " Ayrah dai tana zaune a bakin gadon tana ta bin Abba da kallo, shima É—in ita yake kallo,

Suna zaune a haka babu wanda yake yiwa ɗan uwansa magana, sai shiru, sukaji an murɗa handle ɗin ƙofar an shigo, mama abu ce ta shigo ita da Ma'u,
Ko kallon inda mama take mama Abu batayi ba, ta wuce ta tsaya akan Abba, saboda wani haushin mama takeji da take taimakon Ayrah,
Chapter 9 · 0% Book details