← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 28

Sashe 2

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana matuƙar ƙaunar mami kamar itace ta haifesa ƙaunar da yake mata ne ma ya shafi 'yar ta maya, wacce tun haihuwar ta yake ƙaunar ta amma shi yana mata ƙaunar 'yan uwan taka ne, saɓanin ita da take masa ƙaunar aure,
Wanda hakan yasa family suka yanke shawarar haɗasu aure, duk da baya mata so na aure bazai iya rejecting jinin mamin sa ba ko yaƙi yin biyayya a familyn su,

Mami ce ta kalle shi tace "to yanzu kaje kayi wanka kayi sallah sai ka fito muyi dinner".

Yace "ok".
Tare da nufar ɗakin sa, Dr. Ahmad ne ya kalli maya da farincikin ta ya kasa ɓoyuwa, yace "maya ya maganar tafiyan mu Abuja goben?". Murmushi tayi tace "yah Ahmad kawai abar tafiyar nan sai upper week". Murmushi mami tayi ta juya ta nufi kitchen, shima Ahmad ɗin dariya ya fara mata ya juya ya nufi ɗakin sa saboda yasan duk saboda zuwan Amjad ne yasaka tace su bari sai upper week,

Itama bin bayan mami tayi har yanzu farincikin fuskarta ya nan, tana zuwa tai kan wata budurwa da take haÉ—a kunun madara,

Ta rungume ta, juyowa tayi tace "masha Allah maya wannan farincikin ya tabbatar min da cewa yah Amjad ya ƙariso". Sake ta tayi tace "Erh mana mubeenah bakiga yadda ya ƙara haske da kyau ba masha Allah ". Mami tace "Allah ko?". Sai a lokacin ta lura da mami dan ita wallahi tama manta mami tana gurin,

Ai bashiri ta juya da gudu ta nufi upstairs É—akinsu ta shiga ta faÉ—a kan gado tana rungume filo, bata daÉ—e da shigowa ba mubeenah ma ta shigo hannun ta É—auke da glass cup da kunun madarar ta, zama tayi a bakin gado tana sha,

Ta kalli maya tace "maya irin wannan farinciki haka sai kace wanda kika yi one year baki ganshi ba?".

Maya tace "bazaki fahimta bane, 5 months fah nayi bangan shiba to kowani month jinsa nake kamar year".

Mubeenah zatayi magana wayar ta, tafara wringing, picking tayi tare da sallama, daga ɗaya ɓangaren aka amsa mata sallamar ta,

Tace "Barka da dare". Yace " Barka dai mubeenah fatan kina lafiya". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Yace "masha Allah yasu mami?". Tace "duk suna lafiya wallahi alhamdulillah ". Yace "hope dai yah Amjad ɗin ya iso?".

Tace"Erh ya iso tun É—azu". Yace "ok ina maya?". Tace "tana nan". Yace "ok ina zuwa I will call you back".
Tace" ok" tare da kashe wayar ta ajjiye,
A saman bed side drower, maya ta kalleta tace "yah Aliyu ne ko?" Mubeenah tace "Erh shine". Maya tace "sis ko kinso ko kinƙi fa gaskiya ɗaya ce shine yah Aliyu yana sonki". Mubeenah batace da ita ƙala ba, ta shiga bathroom domin ɗauro alwala alwala tayi ta fito ta da Sallah, ..... A ɓangaren Amjad suma tare suka tafi masallaci shida Dr Ahmad sukayi sallah suna fitowa suka tsaya a dining,..

Mubeenah ma bayan ta idar da Sallah , tare suka fito da maya wacce tayi wanka ta canza kaya zuwa riga da wando masu laushi maras sa nauyi, sai ƙaramin half Sunnah black da ta saka, sai ƙamshi take,

A dining suka tadda mami da kuma su Dr Ahmad zama sukayi tare da gaida kowa, bayan sun amsa Amjad ya kalli mami yace " mami kaddai daddy baya gari?". Mami tace " Erh yana Abuja amma may be gobe zai dawo". Yace "ok".

Daga nan babu wanda ya ƙara cewa komai a ɗan uwansa mami ce da kanta tayi saving ɗin su, bayan sun gama suka dawo falo suka fara hira, maya ta kalle shi tace "yah Amjad wannan karan baka siyo mana abayas bane?". Yace " dukka suna mota". Mami tace "ohhh maya ke ko sha'awar atamfa bakyayi ne? Kullum rayuwar ki cikin abaya". Miƙewa Amjad yayi yace "mami na zanje wani guri amma ban daɗeba zan dawo". Tace "ok". Ahmad yace " bari muje tare". Tare suka fita basu tsaya a ko ina ba sai a M. SARKI hospital, ya daɗe a dakin yana kallon ta kafin daga baya ya miƙe ya jamata bedsheet ya rufe ta tare da karanto mata addu'oi sannan ya fice,...

****Washe gari misalin 9:20am ta farfaɗo a hankali ta sauƙe idonta akan Dr Ahmad sai kuma ta maida kallon ta kansa, hawaye ne suke bin ƙuncinta, Dr Ahmad yace "mata sannu". Kai kawai ta iya ɗaga masa, yace "akwai inda yake miki ciyo?". Tace "a'a ina ne nan ina mama abu da ma'u ina kuma talle na?". Yace "ki kwantar da hankalin ki, kin samu accident ne ". Tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un". Dr Ahmad yace "kiyi hakuri insha Allahu zuwa anjima zamu sallame ki amma kafin nan ki bamu numbern wani naki sai mu kira mu sanar da shi". Tace "no kabarshi kawai". Yace"Meyasa?". Tace "ina buƙatar nayi sallah ". Toilet ya nuna mata sannan dukkan su suka fita, ita kuma ta tashi ta shiga toilet in, bayan tayo alwala ta fito ta shimfiɗa kwalin ta tana gabatar da sallolin da ake binta,

Bata daɗe da idarwa ba sai ga su sun dawo, da sallamar su ta amsa musu, sannan ta gaishe su, suka amsa, abincin da suka siyo mata ya miƙa mata, yace " ga abinci kici ". Tace " ok". Ta karɓa tare da yi masa godiya, ledar ta buɗe ta ciro abinci da ruwan sai kuma ta tsaya tana bin abincin da kallo,

Dr. Ahmad yace "ki saki jiki kici abincin ki bari muje mu dawo". Bata ce da su komai ba har suka fice, bayan 'yan mintuna suka dawo suka samu tagama cin abincin tana ta hawaye, Dr Ahmad yace "ƙanwata lafiya kike kuka?". Tace " babu komai". Yace "akwai mana karkiji komai ki faɗa min meyake da munki ki ɗauke Ni matsayin yayan ki". Tace " dama idan na koma gida babu kuɗin goron mama abu ne to zata iya kasheni da duka". Ta faɗa tana mai share hawayen idonta yace "babu komai yanzu amshi maganin nan kisha insha Allahu zan baki kuɗin goron sai muje mu bata hakuri".

Ta karɓi maganin tace" no ba sai kunje ba ai dan idan kukaje ma kuna tafiya zata dake ni". Yace "maman kice?". Tace "a'a matar mahaifina ne ni ummi na ta ɓata tun shekaru 3 baya". Amjad yace "ayya I'm sorry Allah ya bayyana ta ". Tace "Ameen ya Allah thank you ".

Misalin ƙarfe 11:00 na safe suka ajjiye ta a unguwar su , babu yanda basu yi da ita akan sukai ta gidan su ba, amma sam ta ƙi, haka suka hakura suka ajjiye ta suka bata kuɗi suka wuce, gidan su ƙawarta Sa'adatu ta tsaya, Sa'adatu na kallon ta taso da gudu ta rungume ta tana hawaye,

Tace "Ayrah lafiya ina kika shiga hankalin mu duk yabi ya tashi?". Maman Sa'adatu tace " ai saiki barta ta huta tukunna". Kama hannun ta Sa'adatu tayi suka zauna ta basu labarin duk abinda ya faru, ta ciro kuɗin da suka bata wanda ita kanta bata san adadin su ba, ta ciri dubu biyar , tabawa maman Sa'adatu sauran tace " mama ga wannan ki ajjiye agurin ki barinje gidan". Tana faɗan haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita,

Bakin ta ɗauke da sallama ta shiga gidan ma'u ce zaune a tsakar gida tana kwalliya, kallon Ayrah tayi tace "sai yanzu kika ga damar dawowa daga yawon karuwancin naki kenan?". Ayrah bata kulata ba ta ƙarisa shigowa gidan,

Ma'u ta ƙwala kiran mama jin shiru yasa ta ƙaracewa "mama ki fito ga karuwar gidan ki ta dawo".............✍️

DUHU 🥀 ________

*A'isha Muhammad Kabir*

-Ma'eesher-

Feature writers association
N

F.U.W.A

2...

***** Da sauri mama ta fito daga ɗakin tana bin Ayrah da wani mugun kallo, Ayrah tai ƙasa da murya tace "mama ina kwana". Mama tace "zo nan muna fuka". jiki babu ƙwari ta ƙarisa gun mama, mama tace "dan ubanki ina tiren tallen da kuma goron?". Take hawaye ya fara bin ƙuncinta cikin rawan murya tace "mama dan Allah kiyi hakuri wani ne ya kaɗeni a asibiti ma na kwana amma ya biyani kuɗin goron".

Mama abu da jira take kawai Ayrah ta gama maganar ta, ta ɗauketa da mari jin maganar ta na ƙarshe na kuɗin ya sakata da katawa da marin da tayi niyyar mata tace "ina kuɗin?". Hannun zaninta ta kunce ta ciro 5k wanda ta cira acikin kuɗin can ta bawa mama, mama na washe baki ta irga, tace "Allah ya taimake ki munafuka yau da kinci uban ki". Ma'u tace " mama bafa wata mota da ta kaɗeta kawai karuwanci ta fara". Mama tace " Ni kam ina ruwana indai zata na kawo min kuɗi taje tayi abinda yafi karuwancin ma".

Ma'u tace "to munafuka tunda kin dawo sai kizo ki ɗibo mana ruwa ki dafa mana abincin rana". Tace "to". Botiki ta ɗauka ta nufi famfo sai da ta cika ko ina da ruwa agidan kafin ta hura wuta ta ɗaura abinci, tana girkin tana shara bayan ta gama share gidan tas taje ta share ɗakin mama ta gyara sannan taje ta gyara nasu, lokacin ta gama dama shinkafa da wake ta girka musu, zuwa tayi ɗakin mama ta tsaya a bakin ƙofa tace " mama nagama girkin". Mama ta ɗebo mata barkono da su maggi tace taje ta daka yaji,
Chapter 2 · 0% Book details