← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 28

Sashe 26

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Misalin ƙarfe 4 na yamma motar su Hajjah ta shigo cikin gidan Aliyu ne, ya ɗakko su daga airport, ko da suka iso ɓangaren Jaddah suka nufa, ta kalli ɗayar ta ta, tace "ki taho mana ". Matar tana kallon Hajjah tace "wallahi Hajjah ji nake gabana yana faɗuwa". Tace "to kiyi addu'a mana, idan ma tunanin gidan ki, kike 2 days kawai zamuyi a nan gidan na maida ke gidan ki". Ita dai bata ƙara cewa komai ba, ta bi bayan Hajjah suka shiga ɓangaren Jaddah bakin su ɗauke da sallama, Nailah da yanzu fitowar ta daga kitchen, ta ƙariso ta rungume Hajjah tana tace “ƙawata". Hannun Hajjah riƙe da na Nailah suka ƙariso falon suka zauna, Aliyu ya shigo busu da akwatunan su, Nailah ta kalli matar da tunda suka shigo ta ke kallon ta, tace "ina yini ". Matar tace "lafiya". Dai-dai nan aka tura ƙofar aka fito Ammie ne da Maya da Farhan da kuma Jaddah tun ɗazu su Ammie suke ɓangaren Jaddah suna jiran ƙarisowar Hajjah ko fitowar su tayi dai-dai da ɗagowar kan matar nan, a mugun zabure matar ta, tashi tana kallon su, Jaddah tace "Fatima". Matar hawaye na bin ƙuncinta ta tafi da sauri ta rungume Jaddah tace "Ammie!". Jaddah ma hawaye take sosai, itama Ammie hawaye take, tace "Fatima ashe kece wacce Hajjah suka jinya?". Matar ta sake Jaddah ta rungume Ammie tana kuka sosai tace "Aunty". Suma kuka suke sosai , Ayrah tayi sallama ta shigo hannun ta riƙe da plate da jug da cups, ƙarar faduwar plate ɗin yasa dukkan su, juyowa suna kallon ta, da ko kula da plate ɗin da ta fasa batayi ba, ta wuce har tana taka wani, ta tafi da gudu ta rungume matar tana cewa"ummie". Itama sosai take kuka, Jaddah tace "Allah sarki ashe jikata muke riƙewa agidan nan batare da mun sani ba". Sosai Fatima take kuka tana rungume da Ayrah itama ayrahn haka,take Ayrah taji wasu abubuwa suna mata yawo a ƙwaƙwalwar ta, memoring ta ya dawo ta tuna komai, sosai take kuka, sai a lokacin Maya ta ƙarisa ta kama hannun tace " sisy na kinfa taka glass ɗin da kika fasa gashi ƙafar ki tana ta jini". Maya ta kalli Farhan da ita ma hawaye take tace "jeki kira Yah Aliyu yazo da first aid box ya bata taimakon gaggawa"......................

___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________

FEATURE WRITERS ASSOCIATION....

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*MER'EESHER ✍️*

Book 1

Page 23...........

***** Bayan an bawa Ayrah taimakon gaggawa tana kwance akan kujera tana kallon ummin ta, ummin ta kuma tana zaune akan kujera tana cin abinci, ummi ta kalli Jaddah tace "Jaddah yaushe kuka dawo Nigeria". Jaddah tace "tunda muka ga kinyi shekara muka jiki shiru, shine muka tattaro muka dawo Nigeria". Ummi tace "ayya Allah sarki a ina kuka samu Ayrah kuma?". Jaddah tace "Maya ce ta kawo ta gidan nan ta haɗu da ita tayi accident shine ta taimaka mata". Ummi ta kalli Maya tace "ayya Allah sarki amfanin taimako kenan ga shi kin taimake ta, batare da sanin ita 'yar uwarki bace". Maya tace"wallahi fah ummi". Ummi tace "ayya Allah ya muku albarka". Dukkanin su, suka amsa da "Ameen ". Ummi ta kalli Nailah tace "jaddah kaddai wannan itace Nailah?". Jaddah tace "itace Nailah ". Ummi ta rufe plate ɗin abincin gabanta tace "alhamdulillah I'm okay". Maya ta tashi ta zuba mata lemon kwakwar da ta haɗa mata, a cup, ta miƙa mata ummi ta karɓa tace "thank you". Sai kuma tace "Maya kira min Mamin na ku mana". Maya tace "ok". Tare da dailing numbern Mami, Mami tayi picking tare da sallama, Maya ta miƙawa Ummi, Ummi ta karɓa, tace "wa alaikissalam". Daga ɗaya ɓangaren Mami ta miƙe daga zaunen da take hawaye yana bin ƙuncinta cikin muryar kuka tace "ukty". Ummi ta goge hawayen idonta, tace "ashe zaki gane muryata". Mami tace "to jini wasa ne?". Ummi tace "a'a ba wasa bane". Daga haka suka canza wata hirar, bayan wani lokaci sukayi sallama tare da kashe wayar, ta miƙawa Maya wayar ta, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo , dukkanin su, suka amsa masa, Maya ta tsaya tana kallon sa tana jin wani sanyi mai daɗi yana ratsa zuciyar ta, idonsa ya sauƙa akan ummi yana kallon ta, cikin rawar murya tare da shock lokaci guda, Yace "Ummi". Ummi ta miƙe tana kallon sa tace "Muhammad". Ya ƙarisa da sauri ya rungume ta, Yace "Ummi ina kika tafi kika barmu kiki barmu da kewar ki?". Tace "Nima nayi kewarku Muhammad". Kukan da Ayrah take riƙe wa ne ya fito fili, kuka take sosai abun ta bata damu da mutanen da suke falon ba , tasan baza su fahimci akan me take kukan ba, ta kalli Amjad sai kuma ta kalli Maya da take zaune a gefen ummin ta shima Amjad ɗin ya zauna a gefen ummin na ta, Ayrah ta ƙara fashewa da kuka tanajin zuciyar ta, tana mata wani irin ciyo, kamar zata fasa ƙirjin ta, ta fito, tashi tayi tana taka ƙafar a hankali, ta nufi ɗakin jaddah, tana zuwa ta faɗa kan gadon Jaddah tana kuka mai tsuma zuciya, Allah ya gani tana son Amjad sosai fiye da yadda zata iya misaltawa, amma Amjad ya cuceta meyasa bai taɓa faɗa mata yana da Engagement ɗin wata akansa ba, sai da ya bari zuciyar ta ta saba da sonsa sosai tanajin bazata iya rayuwa ba tare da shi ba,......... A ranar Mami tazo Abuja ita da ummi kamar zasu cinye junan su, kwanan ta biyu ta koma Kano, ita kuwa Ayrah a duk kwana biyun nan ta zama kamar marar lafiya duk abinda zai haɗa ta da Amjad bata son shi, bata son haɗuwa da shi, ko ɓangaren ammie ma sau biyu take zuwa a rana, taje ta gaida Ammie da safe sai kuma da Yamma, lokacin da Abbie ya dawo kusan yafi kowa farincikin ganin Ummi,......
Chapter 26 · 0% Book details