Sashe 25
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
_______ Jaddah dai tana ta kallon ta, can tace "ƙawata menene sunanki?". Ayrah tace "sunana A'isha amma ana cemin Ayrah ". Jaddah tace"Masha Allah suna mai daɗi". Ammie tace "ayya Allah sarki". Hajiya ce ta shigo hannun ta ɗauke da akwati, ammie tana kallon ta tace "Hajiya lafiya naganki da akwati haka?". Hajiya tace "wallahi zan tafi Kano ne amma insha Allahu kafin na wuce gidana zan dawo nan ɗin". Ammie tace "ayya Allah sarki to Allah ya tsare". Hajiya ta kalli Amjad tace "my son kazo ku ajjiye ni a airport kai da 'yar tawa". Amjad yace "to Hajiya". tare da miƙewa Har zai fita, mubeenah ta kalle shi, tace "Yawwa Yah Amjad ɗazu naji kace a sister na Fulani ita fa sunan ta Ayrah ba Fulani ba". Ya kalli mubeenah kamar ba zaice komai ba sai kuma Yace "ok". Hajiya ta kalli Ayrah tace "daughter zo ku rakani airport". Ayrah tace "to Hajiya" tare da miƙewa ta tabi bayan su, ko da suka isa har Amjad ya saka akwatin Hajiya a Boot Hajiya ta shiga back seat Ayrah Kuma ta shiga front seat, tun da suka fara tafiya ta jinginar da kanta ajikin seat ɗin ta lumshe idanun ta tana shaƙar ƙamshin turaren sa da ya haɗu da sanyin AC da yake ta shi acikin motar, tana ƙoƙwarin tuna wani abu a ranta tana ji kamar wannan ranar ta taɓa faruwa, Muryarsa taji ta dake dodon kunnen ta da wani sautin sa mai daɗin sauraro, Yace "Fulani naga kin rufe idonki ko dai bakyajin daɗi ne?". Ta buɗe ido ta kalle shi, cikin sanyin murya tace "lafiya na ƙalau". Yace "ok". Daga nan kuma bai ƙara cewa komai ba har suka isa airport ɗin, suka sauƙa hannun Hajiya riƙe da na Ayrah shi kuma ya ja mata akwatin ta, Hajiya ta tambayi Ayrah ko tana da account ne, tace"a'a ita fah bata da account ". Hajiya ta kalli Ayrah tace "amma ai kina da national ID card". Tace "erh ina da shi". Hajiya ta mai da kallon ta kan Amjad tace "my son dan Allah ko zuwa gobe ma if you have time ka ɗauke ta ka rakata ko bank ɗin Abbie ne ta buɗe account". Yace "badamuwa Hajiya insha Allahu zan kai kaita ". Hajiya tace "Yawwa Nagode". Tare da musu sallama ta wuce, su kuma suka juya, suna cikin mota suna tafiya ya kalle ta, Yace "Fulani sai kuma naji labarin ke ahalin SARAKI ce". Tace "Erh fah". Yace "Fulani nasan yanzu kinsan komai game da Engagement ɗin da yake kaina ko?". Tace "nasani mana ko ba Engagement ɗin ka da Aunty na ba?". Yace "shi". Yace "amma yanzu menene matsayina a zuciyar ki?". Tace "uncle Amjad nifa ban fahimci akan me kake magana ba". Yace "amma ya akayi kika haɗu da Maya". Tace "wallahi Nima ban sani ba, nakasa tunawa". Yace "ban fahimta ba". Tace "bakomai nake iya tunawa saka makon bugun da na samu a brain ɗin na". Da mugun sauri ya taka burki, sai da ta ɗan bugu da seat ɗin motar, ta maida kallon ta kanshi tace "lafiya". Yace "kina nufin kina fama da partial amnesia kenan?". Tace "Erh haka likita Yace ". Yace "yanzu kina nufin Nima baki tunani ba". Tace "inajin kamar nasan ka tun ba yau ba, kuma ina iya tuna wasu maganganu da suka faru tsakanin mu, amma ban yadda irin maganar da nakeji ta taɓa shiga tsakanin mu ba kawai ƙwaƙwalwata tana yaudara ta ne". Yace "ikon Allah to Allah ya baki lafiya". Tace "amma fa inajin wani abu game da kai wanda shima ban yadda da shi ba". Yace "Allah ya baki lafiya". Tace "Ameen thank you". Da ganan babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har suka isa gida, ...........
*MA'U*
ta tsaya tana binsa da kallo, kamar mai son ɓoye wani abu can kuma tace"aure fah kace sagir". Yace "Erh wallahi auren ki zanyi Ma'u idan har kin amince zaki aure ni, to ni bana da wata matsala ". Tace "sagir amma kasan fa rayuwar da muka yi a baya taya zakace zaka aureni kuma na amince da kai". Yace "wallahi Ma'u ko yau kikace min kin amince insha Allahu acikin satin nan zan turo magabata na, sai ayi maganar auren mu". Tace "amma........". Yace "amma me? Ko dai bakya sona ne Ma'u?". Tace "ina sonka mana amma inajin tsoron kar 'yan uwanka su zo bincike su binciko abinda na aika ta". Yace "karki damu babu wani bincike da zasu yi insha Allahu nasan yadda zanyi da su fatana kawai dai ki amince da aurena". Tace "babu komai sagir na amince Allah ya shige mana gaba ". Yace "Ameen Nagode ". Da ga nan sukai sallama ta fita daga motar ta shige gida". Tana shiga ta samu Mama Abu a zaune lantana sabuwar mai aikin su, tana shara, tana zuwa ta shige ɗakin Mama Abu tace "ki shigo zamuyi magana". Da sauri mama Abu ta tashi ta bi bayan Ma'u, ta sameta a zaune a bakin gado, itama ta zauna tana kallon ta tace " 'yar albarka lafiya". Ma'u ta kalle ta tace "sagir ne wani tsohon saurayi na ya zo wai aurena zaiyi". Mama Abu tace "aure kuma?". Ma'u tace "Erh shifa auren ko haramunne?". Mama Abu tace "a'a ba haramun bane". Ma'u tace "to ki sanar da 'yan uwanki, acikin satin nan dangin sagir zasu zo neman aurena, ko dan ma ashe dangin babana zasu je bana ki ba". Mama Abu tace "yanzu Ma'u aure zakiyi ki barni bayan da ke na dogara". Ma'u tace" aure fa babu fashi mama gara ma kisani ". Mama Abu tace " Ni kuwa wallahi banason kiyi auren nan". Tace "mama kawai ki fito fili kice baƙin ciki kike min da hassada kuma wallahi aure babu fashi ". Tana faɗan haka ta miƙe tai ficewar ta bata ƙara bi ta kan Mama Abu ba, Mama Abu da kallon mamaki haɗi da baƙin ciki da ta kaici tabi Ma'u, sai da Ma'u ta fice daga ɗakin Mama Abu ta tafka uban tagumi maganar auren tana mata yawo a zuciyar ta, yanzu idan Ma'u tayi aure ya zatayi ga shi dai sagir ɗin nan ba wani shegen mai kuɗi bane, ballantana ta saka a ranta, zata na samun wani abu agurin Ma'un bayan tayi auren, ..............
*AYRAH*.........
Washegari ita da Amjad da Farhan suka fita aka mata bvn aka buÉ—e mata account suka dawo, basu wani jima ba kasancewar su, masu bankin,....
Tana tsaye a kitchen tana wanke-wanken Farhan ta shigo kitchen ɗin tana kallon ta, tace "sis kije Jaddah tana kiranki". Ayrah tace "tana ina?". Farhan tace "tana ɓangaren ta". Ayrah tace "ok barinje". Tana faɗan haka ta fice daga kitchen ɗin ta nufi ɓangaren Jiddah a falo ta samu, Nailah tana kwance tana ta danne-danne a wayar ta, ta kalli, Ayrah tayi sallama Nailah ta amsa mata cikin fara'a ba tare da sanin itace wacce Amjad yake so ba, Ayrah ta ƙariso ta zauna tana kallon Nailah tace "sis Jaddah fah". Nailah tace "tana ciki". Ayrah tace "ok Nagode".tare da nufar ɗakin Jaddah, knocking tayi Jaddah dake zaune a bakin gado, ta bata izinin shiga, kafin ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, tana shiga ta zauna a ƙasan carpet tana gaida Jaddah, Jaddah ta amsa cikin fara'a kafin, ta kalle ta, tace "magana nake so muyi ƙawata". Ayrah ta sunkuyar da kanta tana wasa da carpet, dai-dai nan ya turo ƙofar ya shigo bakin sa ɗauke da sallama, dukkanin su suka amsa masa, ya shigo shima ya zauna yana gaida Jaddah, ta amsa masa, itama Ayrah ta ɗago kai ta kalleshi ta gaishe shi, ya amsa mata cikin fara'a, jaddah ta kalle ta, tace "ƙawata kin san Wannan?". Tayi maganar tare da nuna Amjad, Ayrah tace "Erh nasan shi". Ba tare da ta ɗago kai ta kalle shi ba". Jaddah tace "a ina kika sanshi kafin ki ganshi a gidan nan ". Tace "bansani ba, na kasa tunawa ni dai kawai abinda nakeji na sanshi tun kafin yanzu ". Jaddah tace " ya sanar min kun nemi mahaifiyar ki kun rasa tun shekarun baya". Hawaye ya fara bin ƙuncinta ta, ta saka hannu ta share tace "tabbas hakane". Jaddah tace" so nake ki bani labarin asalin mahaifiyar ki saboda mu taimaka Miki wajen nemo ta". Tace "jaddah wallahi bansani ba, bazan iya tunawa ba". Jaddah tace "shikkenan tashi kije". Ayrah ta, tashi ta fice tana share hawayen idanun ta, Nailah har yanzu tana zaune a inda take, bayan Ayrah ta fito, ta takalle ta tace "sis har kin fito?". Ayrah tace "Erh na fito". Daga haka babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har Ayrah ta fice, yau girke-girke suke kala-kala saboda yau jirgin su Hajjah zaiyi landing a Nigeria..........