← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 28

Sashe 12

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kwana biyu da tafiyar su, Sa'adatu ta, Ayrah ta rame, saboda ayyukan gidan nan da tunanin halin da Abban ta yake ciki, kullum cikin addu'a take da fatan Allah ya bashi lafiya, kullum cikin kewar Sa'adatu da mama take sometimes takan sha kuka idan ta tuna su, gashi yanzu bata da waya ballantana taji daga garesu,......

MAYA....

Tunda yah Ammar ya kira yace" su je Madina su sameshi ita da mubeenah, jikin ta yayi sanyi, babu abinda bata kawo a ranta ba, mubeenah kam babu abinda ta kawo a ranta sai murna take ji, tana fatan Allah yasa a Dubai zasu yi taron kasuwancin nasu, haka suka fito suna jan akwati nan su, a falo suka ajjiye akwati nan suka wuce ɓangaren Mami suna shiga, suka sameta a falo tana kallo, ƙarisa wa sukayi suka gaisheta, ta amsa da fara'a tace "har kun shirya kenan". Mubeenah tace "erh Mami". Mami tace "Masha Allah, Allah ya kaiku lafiya ya dawo da ku lafiya". Dukkan su, suka amsa da "Ameen". Mami tace "ai munyi waya da Amjad ɗin ma Yace taron na ku, sai after 5 days, amma dai ku tafi yanzu saboda wasu dalilai,". Sosai Maya taji hankalin ta ya kwanta, jin anyi waya da Amjad, bata san sau nawa ta kira shi ba, amma baya picking, mubeenah tace"Mami Allah yasa a Dubai za'ayi taron". Mami tayi dariya tace "Ni kam mubeenah wani yaji kina maganar nan ai sai yayi tunanin baki taɓa zuwa, Dubai ɗin ba".
Tace " Mami Allah ina son ƙasar ne sosai". Mami tace "to Allah ya baki mijin da zaku zauna da shi a Dubai ɗin". Tace "Ameen Mami nah". Maya tayi sauri tace "Mami ai ɗan kine ma, mijin baki sani ba". Da sauri mubeenah ta juyo tana kallon ta, Mami tace "to ɗana kuma ko dai Aliyu?". Mubeenah ta tashi ta fice daga falon tana hararan Maya, Mami tayi farinciki sosai da jin wannan labarin 'yar mijin nata, da ɗan yayan ta take soyayya,

Mubeenah na fitowa taga Aliyu zaune a falo yana danna wayarsa, da sauri ta ƙarisa ta zauna tana kallon sa tace " Meyasa baka faɗa min zaka zo ba, bayan ɗazu ma sai da mukayi waya?". Ya ɗaga kai ya kalle ta sai kuma ya maida wayar aljihun sa, yace "The happiness I saw on your face is exactly why I decided to surprise you." Har zata yi magana sai ga Ahmad da fadila sun shigo falon sai baza ƙamshi suke yi, Aliyu yace "good morning bro". Ahmad yace "morning Aliyu yanzu nake tunanin kiranka ashe ma ka ƙariso". Mami ce ta fito tare da Maya, da sauri mubeenah ta, tashi daga gefen Aliyu da take zaune tana sunne kai, Mami tayi murmishi tace "Aliyu ashe ka ƙariso?". Yace "Erh Mami ". Tace "ya ka baro su ammien da farhan?". Yace " suna lafiya". Ahmad yace "Mami zamu tafi saboda saura 30 minutes flights ɗin su ya tashi, Mami ta kalle su tace "to Allah ya tsare a gaishe min da Jiddah da Ammar da sauran mutanen gidan". Aliyu Yace" insha Allahu zan suji". Mami taita musu addu'a tare da musu sallama suka wuce, Ahmad ne ke driving sai Aliyu a front seat, su kuma matan suna baya, suka nufi airport,.....

AYRAH.....

Yauma kamar kullum tana wanki tsakar gida, Tanko ya shigo ko sallama babu kallon ta yayi yana wani irin murmishi É—ago kanta, tayi ta kalle shi, sai kuma ta sunkuya taci gaba da wankin ta, Yace "ke dan ubanki baki iya gaisuwa bane?".
Tace "ina wuni". A taƙaice, Yace" lafiya an faɗa maki, an bani auren ki?". Dammm zuciyar ta, tai mugun bugawa da sauri ta ɗago ta kalle shi, idon ta na tara ƙwallah, tace "wa ya baka aure na?". Yace "kaji 'yar rainin hankali ni kike tambaya?". Sosai taji hankalin ta ya tashi, ta kasa magana, tasa hannu ta share hawayen da yake zubo mata, ta ci gaba da wankin ta, Tanko ya kalle ta ya kwashe da dariyar mugun ta, yace "au kuka ma kike?, ai baki ma yi kuka ba yarinya sai an daura mana aure nan da wata ɗaya". Wai nan da wata ɗaya, Mafi ce ta fito daga ɗaki, ta kalle su tace "kaga angon wata ɗaya da amaryar wata ɗaya ". Tanko yace "sa'adai ƙanwata". Ma'u tace " Ni dai idan ka amince da abubuwan da na faɗa maka, komai kake so zan maka a auren nan". Yace "darrr ƙanwata ai ko mutum kika saka na kashe Miki sai na miƙa miki shi lahira indai bukata ta zata biya akan wannan yarinyar". Ma'u ta kalle shi tace" sai da kai ɗan uwana". Daga haka ta koma ɗakin su". "Aure nan da wata ɗaya kuma da Tanko, kuma menene Ma'u ta shirya masa danna san abin dole yana da nasaba da ni". Da Ayrah tayiwa kanta tambayar da bata da also shinsu, a ranta tana fatan Allah ya kar ya bawa su mama Abu iko akan ta, domin wallahi bazata iya zama da Tanko ba, .........

MAYA.......

Bayan sun sauƙa a garin Madina Ammar da kansa ya zo ya ɗauke su, a airport, zuwa gidan jaddah, da sallamar su suka shiga, wata kyakkyawar budurwa tana zaune a falon ta ɗaura ƙafar ta ɗaya akan ɗaya sai faman jijjiga ƙafar take, hannun ta ɗaya ɗauke da remote tana kallo, sosai Maya taji jikin ta yayi sanyin saka makon kallon budurwar da tayi, har suka ƙarisa falon budurwar ko ɗagowa kanta batayi ba, ballan tana tasan da mutane a falon, Mubeenah tace "ikon Allah Nailah wai bakiji sallamar mu bane?". Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalli Mubeenah, tace "wa alaikissalam". Daga nan ta maida kallon ta kan TV, su kam wucewa sukayi ɗakin da suke sauƙa idan sun zo Madina wanda itama Nailah a nan ta sauƙa, bayan sunyi wanka sun gabatar da sallolin su, suka fito suka nufi ɓangaren Jaddah, a falo suka samu nailah tana kwance akan cinyar Jaddah, tana kallon su ta haɗe rai, Jaddah tace"Masha Allah Maya har kun ƙariso kenan?". Maya tana murmushi tace "erh Jaddah tun ɗazu ma". Jaddah tace "to sannu ku da zuwa". Mubeenah tace"sannu Jaddah". yayinda take zama agefen Jaddah, Maya ta kalli Jaddah tace "yanzu ke baiwar Allah haka ake tarban baƙi?". Mubeenah tace "ƙyaleta dai tabarmu ko ruwa bata bamu ba". Jaddah tace"lallai yaran nan, yaushe dama kuka zama baƙi a gidan nan ban sani ba?". Maya tace "to ni dai yunwa nake ji". Jaddah tace "kuje ku kira Ammar da Amjad su fito muyi dinner". Maya tace "to". Ta miƙe ta fita, Mubeenah tabi bayan ta, suna fita, ta kalli Mubeenah tace "dan Allah kije ki kira yah Ammar kinga ni ba shiri nake da shi ba". Mubeenah tace "Madam faɗi gaskiya dai, ke dai kawai kina so ki kira masoyin ki". Maya tace "idan nayi hakan ma ai banyi laifi ba". Mubeenah taje ɗakin Ammar ta kai 3 minutes tana knocking kafin ya buɗe, yana kallon ta yace "what's up?". Tace "dinner is ready". Bai ce mata komai ba ya rufe ƙofar, ta juya tana tafiya, tana dana sanin biyewa Maya da tayi tazo kiran wannan bawan Allahn, a haka suka ƙarisa dining bayan sun, gama dinner, kowa ya tashi ya rage daga Maya sai Mubeenah, Mubeenah ta kalli Maya tace "wallahi yah Ammar ɗin nan haushi yake bani sai shegen miskilan ci da iyayi". Maya tace"meya faru?". Mubeenah tace "wai fah da naje sai da nayi jiran 3 minutes kafin ya buɗe, yana buɗewa wai what's up". Maya bata san lokacin da ta fara dariya ba tace " ikon Allah". Mubeenah tace "wannan cankalkalar Kuma a hakan wai Yah Amjad take so, shiyasa take mana wannan iyayin". Maya dai bata ƙara ce mata komai ba, haka har suka gama suka wuce bedroom ɗin su, haka a kai su kai zaman 5 days ɗin su, suka wuce Dubai ɗin su, one week sukayi a Dubai daga nan suka wuce Nigeria, amma banda Amjad shi kam, Madina ya koma,

Su Maya a Abuja suka sauƙa gidan ammie, zo kaga farinciki agun farhan kamar ta mai da su ciki, Maya tana zaune a falo tana kallo ita da farhan, Mubeenah da ammie kuma suna kitchen suna girki, Maya ta kalli farhan tace "kunyi waya da yah Amjad ɗin ne?". Farhan tace "erh munyi waya yace next week insha Allahu zai dawo ko upper week ". Maya tace "Allah ya dawo da shi lafiya". Dai-dai lokacin Ammar ya shigo falon hannun sa riƙe da laptop ya zauna with out looking at them, Maya tace "good evening bro". "Evening". Yace a ta ƙaice, still bai ɗago kansa ba yana danna system ɗin sa, yace " farhan make coffee for me". Farhan ta miƙe ta nufi kitchen, aka bar shi daga shi sai Maya hankalin ta yana kan TV, hannu ya saka ya ɗauki remote tare da canza channel ɗin ya mai dashi zuwa channel ɗin kwallo, ta daga kai ta kalle shi kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta miƙe ta nufi kitchen itama,

Tana shiga farhan ta kalle ta, tace " ya canza channel ko?". Maya tace "how do you know?". Farhan tace "to ai kullum haka yake, idan yana gidan nan kwata-kwata bana da sukuni har gara yah Amjad sau dubu É—ari, shifa ko magana ba yayi sai dai make coffee for me,". Ammie tace "nifa ku daina gulmar É—ana". Maya dai bata ce komai ba ta fice ta koma É—akin farhan, .......

AYRAH.......
Chapter 12 · 0% Book details