Sashe 13
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Babu ƙiftawa take kallon Sa'adatu da mugun mamaki, ta sa hannu ta share hawayen ta, tace "Sa'adatu ba gaskiya kikaji ba wallahi Abbana bai rasu ba, Sa'adatu ta saka hannu ta kama Ayrah cikin kuka tace "Ayrah kiyi hakuri amma ko da zasu shigo jirgin sai da ya sanar min, wallahi Ayrah jirgin su abbane ne ya ƙone kuma babu wanda yayi rai acikin jirgin, da sauri Ayrah ta janye jikin ta, daga na Sa'adatu ta kama hanyar fita, da sauri Sa'adatu tabi bayan ta, tana tsaida napep Sa'adatu tai sauri ta shige, a asibiti aka ajjiye su, Sa'adatu ce tabiya me napep ɗin, sannan ta shige ciki ta shige, a reception ta tsaya tana kallon nurse ɗin da taga sunfi kusa da DR Kamal tace "dan Allah sis ki faɗa min gaskiya da gaske, Abbana da Dr kamal sun rasu, nurse Zainab ta ɗago idanuwan ta da duk sun kumbura saboda kuka, tace "kiyi hakuri Ayrah addu'a suke buƙata ba komai ba". Ayrah ji tayi jin ta ya ɗauke ganin ta ma ya fara ɗauke wa, su Sa'adatu basu ankara ba, suka ga ta faɗi a gurin.........
Idan kun gama karantawa ku kasance BAYAN DUHU DISCUSSION FORUM 📚, domin comments,
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 12......
***** A hankali ta buɗe idonta ta sauƙe shi akan Sa'adatu sai kuma ta mai da kallon ta kan drip ɗin da aka saka mata, ta maida kallon ta kan Sa'adatu dake zaune a bakin gadon tace "dan Allah Sa'adatu kice min Abbana bai rasu ba kinji, kice min Abbana yana da ransa kinji". Sa'adatu bata ce mata komai ba ta, tashi ta fice daga ɗakin, saboda bata so Ayrah ta kalli hawayen da take ɓoyewa, tana fita mama tana shigowa, mama ta zauna a agefen gadon tana kallon Ayrah, tace"sannu Ayrah Ya jikin naki". Tace "mama kema kin yadda Abbana ya rasu kenan?". Mama tace "kiyi hakuri Ayrah yanzu Abban ki babu abinda yake buƙata sama da addu'ar ki". Kallon mama take babu ko ƙiftawa tana jin zuciyar ta, tana ta wani irin nauyi, she wish zata iya kuka ko zataji sauƙin abinda take ji aranta, mama tace "kiyi hakuri, ke musulmace ya kamata ki yadda da ƙaddara kyakkyawa ko mummuna, wannan ba komai bane sai jarrabawa kuma muna Miki fatan ki cinye ta ɗari nisa ɗari". Ayrah ta rufe idon ta kawai ta juya,
tanajin maganga nun mama yana mata yawo a kanta, ganin ta rufe idonta mama bata ƙara ce mata komai ba tayi shiru, a rufe idon da tayi har bacci ya ɗauke ta,.....
*MAYA*
Tana zaune a falo, kana ganin ta zaka gane baƙara min kuka tayi ba, fadilah na zaune a gefen ta itama ta zuba uban ta gumi, Dr. Ahmad ne ya shigo ya kallesu, yace "Ni kam ban san sau nawa zan muku magana ba a gidan nan, kullum cikin kuka da tagumi kuke, kuma ana muku magana sai kuce kaunar Kamal kuke, wannan ba ƙauna bace, babu ƙaunar da zaku nunawa Kamal da ya wuce ku masa addu'a, anjima zamu wuce inda jirgin ya kone ni da su daddy". Maya ta ɗaga kai ta kalleshi tace " kayi hakuri yah Ahmad Insha Allahu, bazamu ƙara kuka ba,". Yace "Yawwa Allah ya Muku albarka". Fadilah dai ta kasa cewa komai, dan maganar da suke yi ma yanzu Allah ka ɗai yasan koƙarin da take gurin hana hawayen ta zubowa, A ɓangaren mommy kuwa, ammie da Mami ba ƙaramin ƙoƙari sosai suke yi ba,wajen ganin sun rarrashe ta, duka a hali biyun baƙara min tashin hankali suka shiga ba, wato alhalin QURAISH da ahalin SARAKI,.........
*AYRAH*......
Kwanan ta biyu a asibiti aka sallame ta, har yanzu Allah bai bata ikon yin kuka ba, Yau ma tana zaune a tsakar gida ita da mama da Sa'adatu Mama Abu kuma suna ɗaki ita da Ma'u, Sa'adatu ta kalle ta tace" ƙawata Insha Allahu gobe zamu koma". Ayrah ta ɗago kanta tana kallon Sa'adatu sai a lokacin ta samu damar yin kuka, tace "wai yanzu shikkenan Abbana ya rasu ya barni kamar yadda ummi ta tafi ta barni?". Mama ta janyo ta jikin ta, tace"kiyi hakuri Ayrah Insha Allahu ummin ki tana raye kuma Insha Allahu wataran Allah zai haɗa fuskokin ku". Sosai Ayrah ta fashe da kuka, tace "rayuwa ta bata da amfani idan babu Ummi kuma babu Abba, ina ma Allah ya ɗauki raina na huta da wannan mummunar ƙaddarar". Tana kaiwa nan ta fashe da kuka sosai, mama ta rungume ta amma ita ma ta kasa ce mata komai Saboda bata son hawayen da take ɓoyewa ya zubo, Sa'adatu ce tai ƙarfin halin cewa Ayrah ki daina faɗan haka dan Allah, bai dace dan Allah ya jarabce ki, ki dinga faɗan haka ba". Bata cewa Sa'adatu komai ba haka taci gaba da kukan ta, suma basu hanata ba, domin idan tayi zata rage jin wani abun da takeji......
*BAYAN WANI LOKACI*......
**** Ayrah duk da ta ɗan warware amma har yanzu kana kallon ta zaka san tana cikin damuwa, mutanen sabuwar unguwar da suka dawo kowa ya shigo gidan mama kawai, ma'u da Tanko take cewa 'ya'yan ta, ita kuma Ayrah tace mai aikin ta ne, Yauma kamar kullum tana zaune a tsakar gida tayi nisa cikin tunanin da take ciki, Tanko ya banko ƙofa ya shigo ko sallama babu yana kallon ta, sau ɗaya ta kalle shi ta ɗage kai, tace "ina wuni". Yace "lafiya amarya". Sai kuma ya maida kallon sa kan mama da Ma'u da suke zaune a gefe suna hirar su, Yace "mama wai ya labarin aurena da yarinyar nan ne, Erh naji batu yayi shiru, wallahi Allah". Mama tace "Karka damu Tanko yaushe kake so a Daura muku auren?". Yace " ko gobe ma ni banƙi a ɗaura ba mama ". Mama tace "zan samu kawun ku da dangin baban ka, na musu magana tunda wanda ya mutu ba dawowa zai yi ba, gara kawai ranar juma'a a ɗaura muku aure". Hawaye ne ya zubo a idon ayrah ta saka hannu ta share a ranta tana fatan Allah kar ya tabbatar mata da auren nan, Ma'u tace "ga munafuka kuka take". Mama tace "to ai ko zata haɗiyi rai ta mutu babu abinda zai hana auren nan". Ma'u tace "Yanzu sai tace ita bata son ɗan uwana ko ? Bayan rufa mata asiri zai yi ya aure ta, tunda ta gama wayon karuwancin ta ba mashinshi ni ". Ayrah dai batace musu komai ba ta, tashi ta shige ɗaki, tana ta tunani ta ina zata fara dan wallahi ko zata mutu bazata auri Tanko ba, .......
*MAYA*.......
Suma izuwa yanzu sun hakura sun barwa Allah komai sai dai ba dare ba rana suna addu'a a Kamal da marar lafiyar da ya tafi da shi, kamar yadda Ayrah itama take yi,
Tana tsaye a jikin wardrobe tana jera kayan ta, Mubeenah ta shigo da saurin ta, tana kallon Maya tace "sis can you guess what?". Maya ta juyo tana kallon ta, tace "i can't". Sai kuma ta juya taci gaba da abinda take, Mubeenah tace "Yah Amjad ya dawo". Da sauri Maya ta juyo tana kallon Mubeenah tace "are you serious?". Mubeenah tace" You can go and see for yourself ". da sauri Maya ta fice daga ɗakin tana fatan Allah yasa ba tsokanar ta Mubeenah takeyi ba, tana fita ta sameshi a zaune a falo yana kallon ball duk da hankalin shi, baya kan TVn kawai idanuwansa ne suke kai shi bai ma san abinda suke cewa ba, ta daɗe tana kallon sa kafin ta ƙarisa tace "ina wuni yah Amjad". Yace "lafiya". A taƙaice, kitchen ta wuce ta fara haɗa masa kunun madara saboda tasan ya naso, kafin ta fito har ya tashi ya tafi ɓangaren sa,.....
Suna zaune a farlo shi da Dr. Ahmad, Dr. Ahmad ya kalle shi, Yace" wai dama da gaske kake kana son yarinyar nan wallahi i thought wasa kake yi". Amjad dai ya kalle shi, baice masa komai ba, yaci gaba da danna system ɗin da yake yi, Dr Ahmad yace "dan Allah ka cirewa kanka damuwa, dan mun rasa inda yarinyar nan take ba yana nufin mun rasa ta har abada bane". Amjad ya ɗago kai ya kalle shi, yace "amma ai ban san halin da take ciki ba". Dr. Ahmad yace " nifa ina mamaki yadda ka damu da rashin samun yarinyar nan". Amjad bai ce masa komai ba, Dr. Ahmad yace " mubarshi a kasamu yarinyar nan ta ina zaka fara gabatar da ita a matsayin kana so ka aure ta bayan kasan Maya tana sonka, kuma da baikonka a kanta". Amjad Yace " I don't know". ......... Bayan ta haɗa kunun madaran ta, ta saka a jug mai kyau ta ɗaura akan plate mai ɗan girma ta haɗa da cups guda biyu, ta ɗauka ta nufi hanyar ɓangaren sa, tana tafiya zuciyar ta, cike da tunane-tunane sai tayi karo da mutum, kunun duka ya zube a jikin sa da mugun mamaki da haushi lokaci guda ya ɗago yana kallon ta, zuciyar ta tayi mugun bugawa bayan ta ɗaga kai ta kalle shi, a zuciyar tace "na shiga uku, Yah Ammar".
*AYRAH*