← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 28

Sashe 5

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da tai kukan ta mai isarta kafin a hankali ta fara magana, sunana "A'ishatul Humaira na taso ban san kowa ba a dangin ummina haka na abbana muna zaman lafiya da Abbana da ummina wani lokaci abba yace zai ƙara aure ummi bataji daɗin hakan ba amma babu yanda muka iya haka baba ya aura mama abu tazo da 'yarta ma'u wacce take Sa'a ta sai kuma ɗan ta Tanko ɗan shaye-shaye babu irin abinda mama abu bata mana ba , na wulaƙanci Abba yana goya mata baya sai da muka zama tamkar bayi a gidan nan, wata rana aka nemi umma na aka rasa lokacin muna jss3 tun daga lokacin babin wahala ta ya buɗe, Ni nake komai a gidan nan, idan nayi kuskure ka ɗan mama abu takama ni tamin duka, shi Tanko bai cika kwana a gidan ba sai yayi sati biyu ma bai shigo gidan ba, yace a mama abu yana sona, tun daga lokacin ta yanke babu wanda zan aura sai shi kuma wallahi bana son shi, bana son auran ɗan shaye-shaye, daga baya idan mama Abu tamin abu Abba na baya iya magana amma yana bani hakuri, ya kan bani kuɗi a ɓoye na siya duk abinda da nake so, amma yanzu Abba shima ya canza ta kwashe labarin duk abinda ya faru jiya da dare ta basu,........

________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*Ma'eesher*✍️

Feature writers association

F.U.W.A

5

Ba Amjad ka ɗai ba shima kansa Dr Ahmad ya tausaya mata, Amjad yace" kiyi hakuri Allah yana jarabtan bayin sa da yake ƙauna ta kowace irin hanya fatan mu dai Allah ya baki ikon cinye wannan jarrabawar insha Allahu bazan bari a aura miki wannan ɗan shaye-shayen ba, kuma insha Allahu zan inganta miki rayuwar ki, sai kin zama abin alfahari a idon duniya, kuma insha Allahu, Allah zai bayyana mana ummin ki". Tace "Allah yasa yayinda take goge hawayen idon ta". Ta ƙirkiro murmushi tace " yah Ahmad menene sunan brothern ka?". yace "gashi nan ki tambaye sa mana ". Sai ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsar ta, Amjad yace "Ahmad yaushe zaku sallame ta?". Ahmad yace"gaskiya akwai buƙatar ta kwana a nan saboda akwai sauran drip in da za'a ƙara saka mata da allurai". Yace "to shikkenan". Ya kalle ta yace "zaki iya kwana ke kaɗai ko mu samo miki me tayaki kwana?". Tace "zan iya kwana ni ka ɗai". Yace " kin tabbata?". Tace" Erh insha Allahu".

Basu bar asibitin nan ba sai da sukayi Isha, sannan yazo ya mata sallama, ta kalle shi tana da fe cikin ta dake mata ciyo sama-sama tace" sai da safe". Yace " ki yi addu'a kafin ki kwanta, masu night duty zasu na zuwa suna du baki". Tace "insha Allahu Nagode ". Bai ce mata komai ba ya fice, wayar da ya bata ta É—akko ta kunna data, tayi downloading TikTok da Whatsapp, TikTok ta sai ta tana ta kallo, abinta sai kusan 11:30 bacci sace ta,..........

Shi kuma bayan sun koma gida yayi wanka ya fito dinning lokacin da ya ƙariso kowa hallaru, yau kam hadda daddy, bayan ya zauna ya gaida daddy sannan ya gaida mami, shima su Maya suka gaishe shi, mubeenah tace "yah Amjad mun gode da shopping Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Dukkan su suka amsa da "Ameen ". Daddy ya kalle shi yace " Amjad ya maganar komawar ka Madina?". Yace daddy nan da 2 weeks insha Allahu zan koma". Mami tace" sai a musu Engagement kafin ya koma yana dawowa Sai a musu aure".
kunya ce ta kama Maya kamar ta nutse ƙasa a hankali ta tashi zata bar gurin?". Mami ta kalle ta, tace "where are you going?". Tace "I'm okay". Mami tace "to ai bakici komai ba, dawo kici abincin ki". Ba dan taso ba ta koma gurin tanajin kunya kamar ta nitse ƙasa, bayan sun gama dinner Mami ta kira ammi ta sanar da ita shawarar da suka yanke ita da daddy Ammi tayi farinciki ta sanar da ita insha Allahu suma suna hanya cikin satin nan zasu zo kawai sai a tsaida ranar Engagement in, shi kam tunda ya kwanta duk juyin sa labarin Ayrah ne yake masa yawo a kunne tunda aka yanke shawarar haɗa shi aure da Maya bai taɓaji baya son auren ba kamar yadda bai taɓaji yana son auren ba, sai da Ayrah ta shigo rayuwar sa, ya rasa gane me yake ji game da yarinyar nan,

Washe gari misalin 7:00am duk sun hallaru a dining suna breakfast saboda duk zasu fita aiki yau, daddy yayi gyaran murya yace "Yayana ya ƙirani jiya yace sun tsaida auren Ahmad da kuma 'yar gurin sa fadila nan da zati ɗaya wato this Saturday". Wani farinciki ne ya mamaye Dukkanin su domin dama sun riga da sun shirya gidan su amaryar kawai suke jira, daddy ya ɗaura da cewa na yanke za'a haɗa auren da Engagement ɗin su Amjad kawai". Mami ce kawai tayi magana tace "ai kuwa hakan yayi Allah ya tabbatar mana da alkhairi ". Suka amsa da "Ameen ".

Bayan sun gama breakfast Amjad da Ahmad suka wuce asibiti sai da ya tsaya ya mata take away a hanya kafin ya suka wuce, baƙin su ɗauke da sallama suka shiga ɗakin ta amsa murya ƙasa-ƙasa ta gaishe su, suka amsa , Ahmad yace "ya jikin ?". Tace " da sauƙi alhamdulillah ". Yace "Allah ya sawwaƙe". Ta amsa da "Ameen ". Yace barin wuce akwai Patience da zan duba". Tace "ok sai anjima". Zama Amjad yayi a bakin gadon yana bin fuskar ta da kallo". Yace "are you okay?". Tace "I'm okay kawai cikina kemin ciyo sai kuma jikina da banajin ƙarfinsa". Yace "karki damu you will be okay soon insha Allahu ". Tace "insha allahu ". Amma dai yau za'a sallameni ko?". Yace " I don't know". Ya ajjiye mata ledan yace kici abinci anjima nurse zata zo ta miki allura ta saka miki sauran drip ɗinki". Tace "insha Allahu Nagode sosai Allah ya saka maka da alkhairi ". Yace " ni zan wuce office". Tace "to Allah ya tsare". Yace "Ameen ".... Ai kamar jira cikin ta yake ya fita ya fara mata mugun ciyo, juyi take a kan gadon tun tana daurewa har ta fara hawaye tana addu'a". Wayar da ya bata ta ɗauka da kyar numbern da ta gani tai dailing picking yayi , ko sallama batayi ba tace "yah mufaddhal cikina zan mutu". Yace "sorry barin turo nurse ta dubaki". Yana faɗan haka ya kashe wayar ya tura mata nurse,.....

MAYA......

Bayan sun gama breakfast suka shirya suka fito suka nufi Company, basu da ɗe da isa ba wata ta shiga office ɗin Maya tace "Madam C.E.O yana ƙiranki". Tace "okay". Ta ajjiye files in da take dubawa ta miƙe ta nufi ƙofa, fitowar ta tayi dai-dai da fitowar mubeenah daga nata office ɗin da yake facing na Maya, tare suka ranka ya zuwa office ɗin nasa , nocking sukayi ya ɗau kusan 5 minutes kafin ya basu izinin shiga, tare suka shiga ko waccen su ta tsaya, sukace "good morning sir". Da wani irin kallo ya bisu kafin yace " before mu ɗauke ku aiki bakuce mana sai kun ga dama zaku na zuwa Company ba". Kallon sa Maya tayi tace "yah Amjad dama". Tsawa ya daka mata yace "who is yah Amjad". Jin ƙarar tayi har cikin kanta, take ta faɗi ƙasa sumammiya..........

________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*Ma'eesher*✍️

FEATURE WRITERS ASSOCIATION.

F.U.W.A

.....6

Da sauri mubeenah tayo kanta, ta É—ebo ruwa a pridge É—in office É—in ta watsa mata, a hankali ta fara numfashi ta buÉ—e idonta, ta É—aura akan mubeenah sai ta maida shi kansa dan shima tuni ya taso yayo kan ta, yace "mubeenah tai mata ki Kaita office É—in ta". Mubeenah ta kamata suna zuwa office É—in ta, ta tun tuntsire da dariya, tai ta dariya sai da tayi mai isarta, ta kalli mubeenah tace "ya kika ga kafcen nawa?". Mubeenah ta tsaya kallon ta, tace "Allah ya kyauta amma wallahi nayi tunanin da gaske ki ke". Tace " da banyi hakan ba Allah kai É—ai yasan abinda zai mana kamar ba yayan mu ba". Mubeenah tace "hakane kam barin wuce office akwai ayyuka da yawa a kaina". Tana faÉ—an haka ta fice....
Chapter 5 · 0% Book details