Sashe 11
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani mummunan faɗuwa gaban Sa'adatu yayi amma ta danne tai wucewar ta, sai da ta fita hawaye suka fara bin idonta, a ranta tana cewa shikkenan za'a ƙarisa rusa rayuwar ƙawarta , Yanzu arasa wanda za'a aura mata Sai Tanko ɗan iska ɓarawo kuma ɗan shaye-shaye, sosai hankalin ta ya tashi, ta shiga gida tana bawa mama labarin abinda ya faru, mama ta kalle ta with shock tace "Innalillahi wa inna alaihi raji'un Allah sarki Ayrah ita kuma ta, ta irin ƙaddarar kenan". Sa'adatu tace " Ya Allah ka dubi rayuwar ƙawata Ya Allah ka cire ta a cikin duhun da take ciki, Ya Allah ka kawo mata haske BAYAN DUHU, hasken da zai canza rayuwar ta daga mummuna izuwa kyakkyawa daga baƙin ciki zuwa farinciki ". Mama tace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum, kin ɗakko mata wayar ta, ta ne?". Sa'adatu tace "wallahi mama banga wayar ba, kawai zan je na bata kuɗin napep ta zo ta duba da kanta, mama tace "to shikkenan". Sa'adatu ta miƙe tare da yiwa mama sallama ta fita,....
Zaune yake a ƙasan lallausan carpet ɗin dake falon, ya tattara duk nu nutsuwar sa , Yana yiwa Daddyn nasa bayani tare da fatan Daddyn zai gamsu, sanda ya kai aya, Alhaji Abdullahi saraki, ya kalle shi, yace "Karka damu Kamal insha Allahu zan taimaka musu, amma sai dai daga kai sai shine zaku tafi kaci gaba da kula da rayuwar shi, tunda kace daga shi sai 'yar sa ne, amma bazan bari ka tafi da kai da ita jinyar sa ba, duk da na yadda da kai Kamal amma zuciya bata da ƙashi, kuma shaiɗan yana ko ina". Kamal yace "Nagode sosai daddy Allah ya ƙara arziki da nisan kwana kuma insha Allahu zan musu bayani idan na koma asibitin". Alhaji Abdullahi yace "Ameen Ya Allah, amma wace ƙasa zaku je". Kamal yace "Egypt saboda suna da kwararrun likitoci". Alhaji Abdullahi saraki yace "babu damuwa ka fara shirya muku tafiyar , Allah ya bashi lafiya". Kamal yace "Ameen". Tare da ƙarayiwa Alhaji Abdullahi saraki godiya sannan ya masa sallama ya fito daga ɓangaren nasa saboda komawa asibitin,
Tunda ta fito take tafiya tana tunane-tunane zuciyar ta, ta kasa nutsuwa da bada auren Ayrah da za'a bada a wannan ɗan iskan, gashi ta kasa samun abun hawa, wata baƙar mota ce tayi parking dai-dai inda take tsaye, ya sauƙe glass ɗin motar yana kallon ta, yace " mallama ina zuwa haka?". Tayi murmishi tace "zan koma hosital ne". Yace "bissimillah ki shigo mutafi nima can na nufa amma zaki biyani". Tace "badamuwa ". Tare da zagaya wa ta buɗe front seat ta zauna, Ya tada motar, ya juya ya kalleta yace "I'm sorry na manta ban tambayi sunan mallamar ba". Tace "sunana Sa'adatu". Yace "Masha Allah, Ni kuma sunana .......,". Tace "Dr kamal ". Murmishi ya sakar mata ya na maida hankalinsa kan driving ɗin da yake yi, yace "how do you know?". Tace "a office ɗin ka mana nagani". Yace "ohhh haka fa, Mahaifin kune ba lafiya". Tace "Erh kusan mahaifi yake a gareni". Yace "ok ". Daga nan babu wanda ya ƙara yiwa ɗan uwansa magana har suka isa hospital ɗin, ta fita tare da masa godiya ta wuce, bayan ya sanar da ita yana buƙatar kallon mama, ........
Da sallamar ta, ta shiga ɗakin da Ayrah suke, ta samu Ayrah zaune a inda take, kallon ta, tayi tace "kaddai tunda na tafi baki tashi ba, Ayrah tace "na tashi nayi sallah, ina wayar tawa?". Nan da Sa'adatu take sanar mata wallahi bata ga wayar ta, ta ba, tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un ". Sa'adatu tace "amma ga kuɗin mashin kije ki duba, daga nan sai ku tafo da mama likita yana buƙatar ganin ta". Ayrah tace "to" tare da miƙewa ta amshi kuɗin ta fita,
*MADINA*
Wata datijuwar mata ce, ta shigo falon bakin ta ɗauke da sallama, ya ɗaga kai ya kalle ta, tare da amsa mata sallamar, sai kuma Yace " Jaddah ya jikin Amjad ɗin, tace "alhamdulillah da sauƙi, inajin anjima ma za'a sallamo shi". Yace "Allah ya ƙara lafiya". Tace "Ameen " Yace "Jaddah baki ga yadda hankalina ya tashi ba lokacin da kika kirani, irin wannan jinya lokaci daya haka kamar mutum zai mutu". Jaddah tace "wallahi Nima na tsoruta shiyasa na kiraka ban kira 'yan Nigeria ba, saboda kar hankalin su, ya tashi gara kai tunda soja ne, kana da taurin zuciya". Dariya maganar ta , ta bashi ya tsaya yana kallon ta yana dariya sai kuma Yace " Lallai Jaddah wato ance Miki mu sojoji bama da imani da tausayi ko?". Tace "ban sani ba". Yayinda take wucewa ɗakin ta, Yace "haba Masoyiyar Yanzu fushi kikayi da ni?". Tace "Masoyiyar ka tana can Nigeria wato hajjah". Daga nan bai ƙara ce mata komai ba ya maida hankalin sa kan kallon da yake yi, bai fi minti biyu ba, agurin ya miƙe, ya ɗau wayar sa, ya fice, ya ɗauki mota,
A hankali yake driving ɗin sa cikin nutsuwa, har ya isa wani makeken hospital dake garin Madina, fita yayi ya shiga asibitin, direct ɗakin da Amjad yake ya shiga, ya sameshi a zaune a bakin gado, sai faman dailing number yake amma baya shiga, bayan yayi sallama ya amsa,kallon sa yayi Yace "good morning bro". Yace "morning ya jikin naka". Yace "alhamdulillah". Yace "to Allah ya baka lafiya". Yace "Ameen". Shiru ya biyo baya, can Amjad Yace "yaushe zaka koma Nigeria?". Yace "may be next week". Amjad yace "amma zaka je gida ko?". Yace "dama a jeji nake?". No ba Abuja ba, i mean Kano, kasan fa Hajjah bata da lafiya ". Yace "ok zanje insha allahu, daga nan shiru ya biyo baya, babu wanda ya ƙarayiwa ɗan uwansa magana kowa hankalin sa nakan wayar sa, har likita ya zo ya salllamesu suka kama hanyar gida,.......
*AYRAH*.....
Ko da taje gida ta gama duba, duben ta amma bata ga wayar ba, haka ta hakura ta fito ta sanar wa da Mama Abu likita yana buƙatar ganin su ita da mama, mama Abu tace suyi gaba tana zuwa, bayan ta fita, Mama Abu ta kalli Ma'u tace " nifa bazan jeba dan wallahi bazan iya jinyar kashi da fitsarin ƙato ba". Ma'u tace "ki daure kije mama may be zai ce muku ya kusa mutuwa ne". Mama Abu tace"ai kuwa da na huta wallahi ". Daga haka ta shige ɗaki ta ɗakko gyalen ta, ta nufi, ƙofar fita,......
Da mama da mama Abu zaune suke akan kujera, bayan ya gama musu bayani, mama Abu tace "babu komai likita sai a fitar da shi É—in, mungode sosai Allah ya saka muku da alkhairi". Dukkan su suka amsa da "Ameen". Mama dai bata so a kai gaggawar amsa wa ba duk da hankalin ta ya kwanta da tafiyar bayan sun fito sai da ta kira É—an ta Adam take faÉ—a masa Yace "badamuwa Mama babban yayan likitan abokina ne, dama su da mahaifinsu suna haka, kawai kubar shi ya tafi da shi". Tace "to shikkenan". Taje tayiwa su Ayrah bayani duk Ayrah taji daÉ—in tafiyar but in one side tanajin zatai kewar Abban ta sosai, ....
Bayan an gama komai jirgin su Abba ya daga zuwa Egypt, mama da Sa'adatu da Ayrah suka dawo gida, sosai Ayrah take kuka suna rarrashin ta ranar a gidan su, Sa'adatu ta kwana , washe gari Yah Adam ya turo mota , bayan sun fito da kayan su, Ayrah dai tana tsaye jikin motar sai kuka takeyi, Mama ta kalle ta bayan driver ya gama saka kayan a mota, tace "kiyi hakuri Ayrah ai tafiya ba mutuwa bace insha Allahu wataran Allah zai haɗa fuskokin mu fatan mu dai Allah ya bawa Abban ki lafiya". Sa'adatu da yanzu ta fito, bayan ta , rufe gidan ta ƙariso jikin motar, itama idanuwanta sun kumbura kana kallon ta zaka san tayi kuka sosai, kallon Ayrah tayi tace "bestie wai ke Meyasa kuka baya Miki wahala ne ?". Tayi maganar tana sunkuyar da kanta, saboda hawayen da suka cika mata ido, Ayrah a hankali cikin kuka tace "bestie nagode, nagode sosai da kulawar ki agareni Nagode da duk abubuwan alkhairi ki a gareni bazan taɓa mantawa da ku ba, ke da mama a rayuwa ta, saboda kuka zamemin bangon da zan jingina , kuma inuwar da zan shiga bayan na rasa mahaifiya ta, Allah ya saka muku da alkhairi kuma ya kaiku lafiya". Sa'adatu da ta rasa abin faɗa kawai ta rungume Ayrah ta fashe da kuka, Mama ma hawayen takeyi hakan ya saka ta saurin buɗe motar ta shiga, a hankali Ayrah ta zame jikin ta daga na Sa'adatu hannun su riƙe da na, juna tace "bestie ku tafi kar na ɓata muku lokaci". Ta faɗa tana share hawayen da yake gangaro mata, ta zame hannun ta daga na Sa'adatu ta juya ta fara tafiya, da sauri Sa'adatu ta ƙarisa ta janyo ta, tare da rungume ta, tana kuka mai sauti, itama Ayrah kuka takeyi sosai, ka fin ta zame jikin ta a hankali tace "Allah ya tsare". Sai kuma ta juya, tana share hawayen idonta, ita ma sa'adatu juyawa tayi tana kuka har ta ƙarisa ta shiga cikin motar ta sauƙe glass tana kallon Ayrah, jin tashin motar ya saka Ayrah juyowa da sauri tana kallon su, Sa'adatu tana hawaye tana ɗaga mata hannu, agurin Ayrah ta zube tana kuka, har motar su, ta ɓacewa ganin ta, ta fi minti 3 agurin tana kuka kafin daga bisani ta miƙe, ta nufi gida hannun ta riƙe da jakar da mama ta bata jiya, ta shiga bakin ta ɗauke da sallama babu kowa a tsakar gidan sai uban datti gidan kamar wanda yayi shekara ba ayi shara, ta wuce tana kallon uban tarin wanke-wanke shima, tana zuwa ta zube a ɗakin tana sake sabon kuka, ta buɗe jakar da mama ta bata, taga kayan Sa'adatu ne kala 5 aciki da hijabai, sai kuma kuɗi dubu 20, da ido take kallon kayan hawaye na bin ƙuncinta, kafin daga baya tasaka jakar acikin Ghana most go ɗin ta, ta kwanta agurin tana kuka har bacci ya ɗauke ta.........
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
11........