Sashe 19
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ayrah kasancewar yau ta rufe ɗakin ta da key kafin ta kwanta, tanaji yana knocking tayi shiru, kamar tana bacci, Yace "Ayrah kizo ki buɗe ƙofar nan ko na ɗakko nawa key ɗin na buɗe, babu ɗakin da bani da key ɗin sa a gidan nan, duk da tasan hakan zata iya yiwuwa amma bata ɗauki maganar serious ba, jin ya daina knocking na wani lokaci ya sakata, ta saƙƙowa daga kan gadon, sanye take da riga da wandon bacci masu taushi da laushi sai kuma hula a kanta, tana tsaye a gurin, yazo ya buɗe ƙofar tafara ja da baya tana girgiza masa kai, ta nufi ƙofa zata fita, ya riƙo hannun ta, Yace"dan Allah Ayrah ki taimaka min, na Miki alƙawarin idan kika taimaka min yanzu bazan ƙara zuwa ɗakin ki ba". Ta daga kai ta kalle shi, hawaye na zirya a idanuwan ta, tace " kasake ni wallahi ko na maka ihu". Yace "Please Ayrah ". A tunanin sa bazata iya ihun ba, ai kuwa bai rufe baki ba, ta ƙawala ihun da ko ina a gidan sai da ya amsa, ta ƙara saka wani ihun, kowa a gidan ya fifto daga ɗakin sa, hadda su Liyana Khalil ne kawai bai tashi ba, Jabeer ma ya fito haka Jiddah, dukkan su suka nufi dakin Ayrah cikin tashin hankali........
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 17.......
Kallon Ayrah yayi Yace "Yanzu da abinda zaki sakawa Jiddah kenan?". Ta ɗaga kai ta kalle shi tace "ban fahimta ba". Yace "bakya tunanin halin da zata shiga idan ta gano mijin ta ne, yazo ɗakin ki yana neman ki". Tace "kai bakayi tunanin halin da zata shiga ba, idan tai find out kake ne mana". Yace "nasan idan Jiddah tasan gaskiya bazata taɓa cigaba da zama da ni ba, kina so kizama sanadiyyar raba uwa da yaran ta kenan?". Zatai magana ta ji ƙarar tafiyar su, da sauri ta fice daga ɗakin, tana kallon Jiddah ta tafi da gudu ta rungume ta, tana kuka". Dukkan su, suka tsaya suna kallon ta, Jiddah tace "Ayrah lafiya?". Tace "Aunty kyankyaso ne ya hau ƙafata". Dariya sosai leenah tayi tace "aunty wallahi nayi tunanin aljani kika gani". Ta ɗago kanta tana kallon leenah tace "to kinga wahalar da na sha ne, kafin na kashe shi?". Jabeer yaja tsaki , Yace "baki san yadda ake addu'a ba sai ihu ko?, duk lokacin da na ƙara jin ihunki da dare a gidan nan akan kyankyaso sai na ɓata miki rai". Yana faɗan haka ya wuce ya barsu a gurin, ta kalli Jiddah tace "aunty dan Allah nikam zan tafi ɗakin su leenah na kwana". Liyana tace "akan kyankyaso?". Jiddah tace "a'a ina kin kashe kyankyason muje na cire miki shi, sai ki kwana a ɗakin ki, kinga ɗakin su leenah babu guri". Tace "Tom shikkenan aunty kawai ku tafi ku kwanta zan koma ɗakin nawa". Jiddah tace "no muje na cire miki kyankyason ". Ayrah tace "Allah aunty kije ki kwanta kawai ". Jiddah tace "to shikkenan". Ta kalli su, leenah tace " ku wuce kuje ku kwanta". Basu ce komai ba suka juya suka nufi ɗakin su, itama ta nufi ɗakin ta, Ayrah ta koma ɗakin ta jikin ta a sanyaye ta kalle shi, tace " uncle dan Allah ka fice daga ɗakin nan". Ya kalle ta baice mata komai ba, ya fice, yana fita ta zube a inda take ta fara kuka, sosai tayi kuka har bacci ya ɗauke ta a gurin, .........
*AMJAD*
Kwana biyu duk yabi ya rame saboda tunanin da ya saka a ransa, Yana kwance a falo akan 3 seater, Nailah ta shigo hannun ta ɗauke da cup ta ajjiye masa tace "Yaya ga coffee". Yace" thanks batare da ya ɗago ya kalle ta ba, Jaddah ce ta shigo, ta zauna akan kujera tana kallon sa, tace "Muhammad ". Amjad ya tashi ya zauna ya jinginu da kujerar Yace" na'am Jaddah". Tace "Muhammad na gaji da ɓoyeyen da kake min, ka duba kaga yadda ka dawo, kabi ka rame yau lafiya gobe jinya, ka faɗa min gaskiyar abinda yake damunka ". Nailah tana jin anfaɗi haka tasamu guri ta zauna domin itama tana sonjin ai nihin abinda yake damun sa, Amjad ya rufe idonsa ya buɗe, ya kalli Jaddah yace" zan faɗa miki gaskiya amma kimin alƙawarin babu wanda zaki faɗawa a gidan mu, it should be secret between us". Dammm zuciyar Nailah ta buga a ranta tana addu'ar Allah yasa kar Jaddah ta Kore ta, Jaddah tace" ina jinka". Yace " na haɗu da wata yarinya ne, kuma mun fara soyayya, and kuma ina sonta sosai, daga baya kuma naje gidan su, sun tashi kuma a unguwar babu wanda yasan inda suka koma shine hankali na ya tashi sosai". Jaddah tace "innalillahi wa inna alaihi raji'un, yanzu yaron nan dama akan mace ne, kake neman kashe kanka". Ya ɗage idon sa daga kanta ya lumshe idonsa, sosai Nailah taji gaban ta ya faɗi, a ranta tana jin babu daɗi sosai, Jaddah tace " maimakon ka miƙawa ubangiji komai ka dage da addu'a, sai Allah ya dubi lamarin ka". Ba tare da ya buɗe idanun sa ba, Yace " wallahi Jaddah ina addu'a ba dare ba rana". Tace "to Allah ya maka mafita, amma ita Maryam ɗin ya za kayi da ita?". Yace "zan aure ta Jaddah". Jaddah tace "to Allah ya zaɓa maka abinda yafi zama alkhairi". Yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum Nagode sosai Jaddah". Jaddah tace "Allah ya maka albarka". Jiki babu ƙawari Nailah tace "Ameen". Sai kuma ta miƙe ta shige ciki, itama Jaddah tashi tayi, ta shige ciki,......
*MAYA*
Suna isowa gida bayan yayi parking ta juya, ta kalle shi, tace "thank you". Baice mata komai ba ya buɗe motar ya fice, itama ta buɗe ta fita ta shige ciki, tana shiga ta wuce ɓangaren su, tayi wanka bayan ta fito ta shirya cikin riga da wando na bacci masu taushi da tsada, sallar la'asar ta gabatar tare da kwanciya akan bed, bata jima ba, bacci ya ɗauke ta, bata farka ba sai wuraren, 7 tana tashi, ta janyo wayar ta, taga missed calls in fadilah har 8 missed calls sai na Mubeenah 5, sai a lokacin ta tuna ma da ta baro su, a can, tana shirin dailing numbern Mubeenah sai ga ta, ta shigo, tana kallon Maya, kamar za tai magana sai kuma ta fasa ta fara rage kayan jikin ta, ta shige bathroom tana fitowa Maya ta kalle ta, tace "kun dawo ashe?". Mubeenah tace "Erh". A taƙaice, Maya tace "gobe su Abie zasu zo neman auren ki". Mubeenah bata san lokacin da ta fara dariya ba, ta faɗa jikin Maya tana tambayar ta "dan Allah da gaske?". Maya tace "wallahi I'm serious na manta tun jiya Abie ya Kirani ya ke faɗa min, and ɗazu ya saka min kuɗi a account ɗina". Mubeenah tace "Masha Allah kinga gobe sai ki ɗauke mu, muje musha ice cream". Maya tace "insha Allahu". Mubeenah ta, tashi ta buɗe wardrobe tana duba kayan da zata saka, tace" Ya akayi kika dawo gida ke ka ɗai?". Ta mata tambayar dan ita har ga Allah har ta manta ma fushi takeyi da Mayan, Maya ta bata labarin yadda akayi ta dawo, Mubeenah bayan ta gama saka doguwar rigar ta, ta juyi ta kalli Maya tace "to amma ya akayi suka san sunan ki?". Maya tace "Nima wallahi ban sani ba". Mubeenah tace "amma abin ya bani mamaki ". Maya tace"Nima haka". Mubeenah tace "ikon Allah ". Daga nan babu wanda ya ƙara cewa ɗan uwansa komai Mubeenah ta fice daga ɗakin,.......
*MAMA ABU*
Tana kitchen tana girki, ta leƙo taga uban tarin wanke-wanken da suka tara, ta juya ta kalli Ma'u da take danne-danne a waya tace "Ma'u yanzu bazaki tashi kiyi wanke-wanken nan ba?". Ma'u hankalin ta akan waya batare da ta ɗago ba, tace "kiyi hakuri kiyi na yau kawai mama dan gaskiya bazan iya ba, gobe zan ne momiki me aiki kafin na tafi". Mama tace "shikkenan amma ina zakije Ma'u?". Ma'u tace "Abuja mana ai dama na faɗa miki". Mama tace "to Allah ya kaimu". Tana faɗan haka ta fito ta ɗebo ruwa ta fara wanke-wanken, Ma'u kuwa tana zaune tana danne-danne a waya, idan taga abin dariya takwashe da dariya, ita kuwa mama tana rana tana wanke-wanken ta, shi kuwa Tanko tunda aka fasa auren sa da Ayrah da suka samu matsala da Ma'u har yau bai ƙara dawowa gidan ba,......