← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai jira abinda Aliyu zai faÉ—a ba ya kashe wayar ya ajjiye, ya tashi ya fara haÉ—a kayan sa, infew minutes ya gama ya shiryawa, Aliyu ya kirasa ya sanar da shi an samu flight É—in 5:30 ok yace tare da kashe wayar,

Fitowa yayi ya wuce ɓangaren Ammi bakin sa ɗauke da sallama ya tura ƙofar ɗakin ta ya shiga, tana zaune abakin gado tana waya, kallon sa ya saka ta kashe wayar tare da amsa masa sallamar sa cikin fara'a.......

________ 🥀 BAYAN DUHU 🥀 _______

*AISHA MUHAMMAD KABIR*

*Ma'eesher*✍️

FEATURE WRITERS ASSOCIATION.

F.U.W.A

8. .....

Ƙarisa wa yayi, ya zauna a ƙasan carpet tare da gaishe ta, ta amsa, yace "Ammi ni kam zan wuce Kano yanzu inshaa Allah". Tace " ikon Allah bazaka jira Abbie ya dawo ba, ko kuma zaka dawo".
Yace "Erh ammie ba daga can zan wuce ba, inshaa Allah gobe zan dawo". Tace" Thom shikkenan Allah ya tsare". Yace "Ameen ya hayyu ya qayyum ammie na" . Ya faÉ—a yayinda yake fita,

Yana fitowa falo ya tadda Aliyu daga alamu shi yake jira, "ka ɗakko min akwatina mu wuce". Ya faɗa yayinda yake ƙarisowa cikin falon, Aliyu baice komai ba ya wuce ya nufi ɓangaren Amjad ,

Yana tsaye yaji an turo ƙofar falon an shigo bakin ta ɗauke da sallama, zuciyar ta tayi mugun bugawa tana kallon shi, sai kuma ta sunne kai tace" good evening yaaya". Maimakon ya amsa sai kawai yace " from where are you?". Ta sunne kai ƙasa tace"from school". Bai ƙara ce mata komai ba, dan haka ta fara shigowa falon, ɗaga kanta tayi tana kallon Aliyu dake shigowa yana jan akwatin hello king a hannun sa,

Murmishi ta sakar masa tace" favorite ina zakaje naganka da akwati?". Yace "banawa bane na yah Amjad ne zai tafi Kano". Tace "favorite dan Allah nima zan raka ku airport ɗin". Yace "ok ki same mu a mota". Shi kam Amjad tuni ya fice ya nufi parking space, ita kuwa farhan autar ammie, school bag ɗin ta kawai ta ajjiye ta ƙara feso turare, ta ɗakko hand bag ɗin ta tana sauri, ta fito ta samesu a parking space tana shiga suka wuce airport........

P.O.V .... AYRAH..

Suna tsaye suna hira ita da Sa'adatu a ƙofar gidan su, sai ga Tanko yazo wucewa ya ƙariso inda suke yace" ke uban mekikeyi a nan gurin?". Banza sukayi da shi kamar basu sanda mutum a gurin ba, ƙarisa yayi gurin cikin masifa yace "ke dan ubanki ba da ke nake magana ba". Ayrah kuwa ganin ya nufo ta yasa ta juya da gudu ta shige gidan su Sa'adatu, Sa'adatu kuwa ta juya ciki tare da rufe ƙofar gidan, Ayrah bata fito daga gidan su Sa'adatu ba sai 6:30 suka fito tare da Sa'adatu suka nufi inda yayi parking ɗin motar sa, yana tsaye jikin motar hannun sa ɗaya na cikin aljihu ɗaya kuma ya kara waya a kunnen sa daga alama waya yakeyi, yana ganin su ya kashe wayar , bakin su ɗauke da sallama suka ƙarisa, ya amsa cikin fara'a , Sa'adatu tace" ina wuni". Yace "lafiya klw alhamdulillah Sa'adatu mun samo ku lafiya". Tace"alhamdulillah" yace "masha Allah yasu mama". Tace "suna lafiya mama tama ce a gaishe ka". Yace"ina amsawa". Tace"to ni zan koma dama na fito ne kawai mu gaisa". Yace "ayya Nagode sosai Sa'adatu". Tare da ciro kuɗi a aljihun sa ya miƙa mata, amma tace" kabarshi wallahi Nagode". Tare da juyawa tabar gurin, a ranta tana ayyana irin kyawun da bawan Allahn nan yake da shi, bayan Sa'adatu ta tafi, Ayrah ta sunkuyar da kanta, tace "ina yini". Yace"ai ni bazan amsa gaisuwar ki ba". Tace"subhnallahi me nayi kuma?". Yace "ɓoyemin damuwar ki mana". Tace"nifa babu abinda yake damuna kawai abbane ya tafi garin da yake aiki kuma kwana biyu yake ya dawo amma yau kwanan sa 4 shiru". Yace" Fulani addu'a kawai zaki dinga masa tare da fatan Allah yasa yana lafiya". Tace"insha Allahu". Yace "amma kin ƙira wayar sa?". Tace"Erh kullum sai na kira amma baya tafiya". Yace" Tom shikkenan ki dage da addu'a mu jira nan da 2 days idan bai dawo ba kije garin ki ɗibo shi". Tace"Thom shikkenan yasu ammie?". Yace"ammie tana nan lafiya". Sun daɗe suna hira kafin daga bisani ya mata sallama tare da bata kuɗi yace "ta kaiwa Sa'adatu". Godiya ta masa ta juya ta tafi, sai da yaga ta shiga gida kafin shima ya juya ya wuce...

MAYA......

Tana zaune a falo tana kallo, aka murɗa handle ɗin ƙofar falon aka shigo, jin Muryar dake sallamar ya saka ta saurin ɗago kanta, tana kallon sa babu ko ƙiftawa, sai da ya ƙariso har inda take ya haɗe rai yace" ke baki iya gaisuwa bane?". Ta sunkuyar da kanta tace " ina wuni". Bai kula ta ba ya wuce part ɗin sa, ta shi tayi da sauri ta nufi part ɗin fadila, tana shiga falon taga fadila da mubeenah suna hira da sauri ta ƙarisa ta faɗa jikin mubeenah tana farinciki, kamar kuma wacce ta tuna wani abu nan farincikin ya koma baƙin ciki, fadila ta kalle ta tace"sis lafiya?". Maya kamar zatai kuka tace " lafiya fadila kawai dai yah Amjad ne ya dawo". Mubeenah tace "ai kin banza to shine na baƙinciki da farincikin?". Maya tace "u will never uderstand ". Mubeenah tace" how will I not understand?". Maya tace "jibi zai koma Madina". Fadila tace "hakuri zakiyi ki saki ranki abinda yana dawowa zaku zama husband and his bride daga nan ko ina zai tafi saiki bishi tayi murmushi sai kuma ta miƙe tace "Allah yasa dai kun rage min kunun madara?". Fadila tace "ki duba fridge". Maya bata ƙara cewa komai ba ta tashi ta nufi kitchen,.......

Shi kuwa Amjad bai fito ba sai lokacin Isha, ya fito yaje ya gaida Mami daga nan ya wuce part ɗin daddy ya gaishe sa tare suka fita sallar Isha, bayan sun dawo kuwa kamar yadda suka saba suka tsaya a dining, Mami da fadila ne suke fitowa da warmers daga kitchen, bayan sun gama suka zauna can sai ga su mubeenah suka saƙƙo daga upstairs, suma ƙarisowa sukayi suka zauna, fadila ce ta fara gaida Amjad sai kuma su Maya ya amsa batare da ya ɗago ya kalle su ba, bayan sun kammala dinner su mubeenah suka wuce ɗakin su, suna shiga Maya ta ɗauki wayar ta akan bedside drower ta buɗe data,tare da kwanciya akan gadon, ta fara chatting da wata ƙawar su, status ta gani Amjad yayi updating da sauri tayi viewing sai taga addu'a ne, duk da ba chatting suke ba, amma ta masa reply da "Ameen ya hayyu ya qayyum yah Amjad". Tana turawa taga yana online, ta cigaba da chatting ɗin ta, after some mutes taga yayi viewing amma bai mata reply ba, bata ji daɗi ba haka ta, tashi ta shiga bathroom wanka ta ƙarayi tayi brush tare da ɗauro alwala, bayan ta fito ta saka kayan baccin tana ƙoƙarin saka hularta ta kalli mubeenah da take ta waya tun shigowar su, sai kuma ta saka hular ta, ta faɗa kan gado taja duvet ta rufe jikin ta tare da ɗakko wayar ta, ta buɗe data, sai ga massage ɗinsa ya shigo da sauri ta buɗe, ta karanta abinda yace mata bata sanda hawaye suka fara binƙuncin ta ba saboda farinciki, ta share hawayen ta kalli mubeenah dake ƙoƙarin shiga bathroom tace" ya Amjad yace bayan ya tafi da sati ɗaya akwai taron kasuwanci da za'a yi, zamuje Madina mu sameshi". Da sauri mubeenah ta juyo tana kallon ta, tace " Masha Allah, Allah yasa a Dubai za'ayi taron". Tana faɗan haka bata jira me Maya zatace ba ta wuce bathroom, Maya kuwa reply ta masa da Allah ya kaimu lokacin da rai da lafiya, sai kuma ta kashe da datar ta takwanta dan tasan ba lallai ya mata reply ba,.....

AYRAH......

Ayrah bayan takaiwa Sa'adatu kuɗin nan mama take sanar mata brothern Sa'adatu Allah ya azurta shi ya siya musu gida a Abuja insha Allahu acikin satin nan zasu koma sosai Ayrah taji babu daɗi sai kuma ta kalli mama tace "to mama Allah sanya alkhairi kice ƙawata za'a zama mutanen Abuja". Sa'adatu tace "wallahi da abbanki zai yadda da mun tafi da ke". Ayrah tace "kema kin san wannan ba abu ne me yiwuwa ba". Sa'adatu tace "kwata-kwata bana farincikin tafiyar nan saboda ke ƙawata". Ayrah tace "amma meyasa yah Adam ɗin bazai bari sai kin rubata Neco ba?". Mama tace "yace acan zai nema mata makaranta ta rubuta daga nan kuma sai ta shiga makarantar gaba da secondary ". Haka nan dai suka sha hira duk suna jin babu daɗi saboda har mama bason yin nisa Ayrah take ba kawai dai babu yanda ta iya ne, sai da suka yi sallar Isha sukaci abinci, sannan Ayrah ta musu sallama tare da fita, ta shigo gida jikin ta babu ƙwari, tana shiga ta samu mama abu zaune a tsakar gida ita da Ma'u suna cin balangu ga 5alive da coke a gefen su, Ma'u ta kalli mama tace" wallahi, kinfiye loma da yawa kawai raba naman nan zamu yi". Mama tace" haba 'yar albarka". Ayrah tayi sallama amma basu kulata ba hakan ya sa ta wuce cikin ɗakin su tai kwanciyar ta, ƙarfe 3 na dare ta tashi tafara gabatar da Sallah ta daɗe akan kwalin ta, tana miƙawa Allah buƙatun ta, Allah yasa duk inda umman ta, take tana cikin hali nagari, Allah yasa Abban ta ma yana cikin ƙoshin lafiya....Washe gari tun da wuri ta tashi ta fara aikin ta saboda Amjad yace mata zai zo, tagama tayi wanka ta shirya , bayan yazo lokacin da zai tafi tasha kuka sosai ya bata kuɗi dayawa sai da ya shiga ya gaida mama kafin ya mata sallama ya fita, bayan ya koma su Maya suka masa rakiya har airport itama tana ta kuka, ji take kamar ta bishi abujan wallahi, amma bazai yiwu ba saboda aikin Company, tunda baya nan tasan yanzu itace on his behalf, ........
Chapter 8 · 0% Book details