Sashe 28
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
Misalin ƙarfe 9 na dare dukkanin mutane gidan sun hallaru a falon Abie
Abie ya buɗe taron da sallama kafin ya fara magana Yace "da farko dai zamu fara da nuna farinciki da gidiyar mu ga Allah da ya bayyana mana jinin mu kuma 'yar uwar mu Fatima tare da 'yar ta A'isha, sai kuma magana ta biyu akan auren Aliyu da mubeenah da kuma auren Muhammad da Maryam, sai kuma batu akan Auren Ammar". Dammm zuciyar Ammar, Ayrah, Amjad , da kuma Maya a tare zuciyoyin su suka buga da mugun ƙarfi, Abie Ya kalli Muhammad Yace" fatan dai ka gama aikin da kakeyi a Madina domin bazaka koma ba sai da matar ka". Amjad mai makon ya bada amsa sai ya juya ya kalli Maya ya Kalli Ayrah sai kuma ya kalli Jaddah ya sunkuyar da kansa, jaddah tace "Ahmad Yanzu a saka ranar auren Mubeenah da Aliyun amma ina so amin alfarma abamu lokaci ni da Muhammad akwai abin da muke shirya tukunna". Abie yace Tom shikkenan Jaddah mun baki lokaci, Amma bazamu fasa saka ranar auren ba, mun saka nan da 2 months za'ayi auren Maryam da Muhammad, Aliyu da mubeenah, kafin 2 months ɗin sai ku gama shirin na ku, idan kuma lokacin bai muku ba sai ki faɗi lokacin da kike so Jaddah ". Jaddah tace "babu komai lokacin yayi min, Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya". Abbie Yace "sai kuma kai Ammar kaima na gaji da kallon ka haka, na baka 2 months ɗin ka fito da mata, idan ba haka ba, na haɗaka aure da koma wacece ". Shi dai Yah Ammar ya sunkuyar da kansa baice komai ba, Abie Yace" sai kuma Nailah tunda kin kammala karatun ki, bazaki ƙara bin Jaddah ku koma Madina ba, a nan zaki zauna kuma kema ki fito da mijin aure". Tace "insha Allahu Abie". Yace "akwai me ƙorafi ko kuma ƙarin bayani ". Jaddah tace "babu Ahmad hukuncin da yanke yayi Allah ya maka albarka". Yace "Ameen Jaddah". Daga haka dukkanin su, suka watse a gurin, babu wanda yake cikin farinciki, Nailah da Ayrah suka nufi ɗakin su, dukkanin su jiki babu ƙwari duk zuciyoyin su babu daɗi musamman Ayrah ji take zuciyar ta kamar zata fasa ƙirjin ta, ta fito............
GODIYA
Da sunan Allah Mai Rahama, Mai Jinƙai.
Alhamdulillaah, godiya ta tabbata ga Allah (SWT), wanda Ya bani ikon farawa, Ya bani ƙarfin ci gaba, kuma Ya bani damar kammala wannan littafi book 1. Ba dan ikonsa ba, da wannan rubutu bai zama komai ba.
Ina mika godiya ta musamman ga duk wanda ya karanta BAYAN DUHU, ya bi labarin tun daga farko, ya fahimci saÆ™onninsa, ya yi dariya, ya yi mamaki, ko ma ya yi tambayar, “Me zai faru a gaba?â€
Ga masu karantawa shafi bayan shafi, ga waɗanda suka yi min magana a lokacin posting, da waɗanda suka ƙarfafa ni da kalamansu—na gode sosai. Ƙaunar da kuke nuna wa rubutuna ita ce ɗaya daga cikin abubuwan da suke ƙara min ƙwarin gwiwa.
Allah Ya saka muku da alheri, Ya kuma sanya wannan littafi ya zama abin tunani da darasi ga duk wanda ya karanta shi.
RUFEWA
A nan ne muka kawo ƙarshen Book 1 na BAYAN DUHU.
Amma ƙarshen wannan littafin ba yana nufin ƙarshen komai ba ne.
Abubuwan da suka faru sun bar tambayoyi da dama, wasu abubuwa kuma har yanzu suna ɓoye a bayan labarin. Wasu amsoshi ba su zo ba tukuna, domin akwai abubuwan da sai lokaci ya bayyana su.
Ku huta da wannan labarin na ɗan lokaci… domin idan lokaci ya yi, za mu sake komawa inda muka tsaya.
Book 1 ya ƙare… amma labarin BAYAN DUHU bai ƙare ba, Yanzu ma labarin ya fara
— MA’EESHER âœï¸