← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 28

Sashe 15

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta fiya kawai takeyi ba tare da tasan ina zataje ba, tayi tafiya mai nisa kafin ta zauna abakin wani titi, Kasan cewar tarasa gurin zuwa , ta daɗe tana yawo for almost 2hours tun 9 gashi yanzu har 11, tana zaune tana ta kallon motoci suna wucewa, wata farar mota ce tazo har ta wuce ta, tayi reverse ta dawo dai-dai inda Ayrah ke zaune, ta buɗe motar ta fito, ta ƙarisa har inda Ayrah take, ta kalle ta, sai kuma ta maida kallon ta kan jakar kayan Ayrah, tace "ƙanwata lafiya kike zaune a bakin titi da daren nan bakya tsoron 'yan isakan unguwa su zo, su sameki a nan?". Ayrah ta ɗaga kai ta kalle ta sai kawai ta fashe da kuka, matar ta kalle ta tace "ba kuka zakiyi ba ƙanwata kiyi magana kinji". Ayrah ta kai hannu ta share hawayen idonta tace "bansan ina zanje ba". Matar tace "subhnallahi kinga ki tashi muje gidana kiyi wanka kici abinci zuwa gobe da safe sai na maida ke gidan ku". Ayrah dai tai shiru bata ce mata komai ba, matar ta tsugunna ta dafa Ayrah tace "ki yadda da ni sunana Jiddah zaki iya kirana da aunty Jiddah wallahi ban tsaya a nan gurin ba sai da niyyar na taimake ki, saboda duk mai hankali bai kamata ya ga mace budurwa a bakin titi acikin halin damuwa kuma ya tafi ya barta ba". Ayrah ta daga ido ta lalle ta, Jiddah tace "Please tashi muje kinji". Ayrah ta miƙe Jiddah ta ɗauki kayan ta, ta saka mata a back seat, ta buɗe mata front seat ta shiga, ita ma ta zagaya ta shiga tare da yiwa motar key, tunda suka shiga motar babu wanda ya ƙara cewa ɗan uwansa wani abu, sunyi tafiya mai nisa kafin suka isa wani makeken gida, hon ɗaya tayi gate man ya buɗe mata suka shiga, bayan tayi parking ta kalli Ayrah tace " fita muje kinji ƙanwata". Ayrah ta fita jiki a sanyaye, Jiddah ta zagayo ta buɗe Black seat ta ciro kayan Ayrah, ta kama hannun ta suka shiga ciki, Masha Allah Ayrah ta furta a zuciyar ta lokacin da suka shiga falon saboda kyau da tsarin da falon yake da shi, yara guda uku ne biyu mata da na miji ɗaya kwance a falon suna bacci, Jiddah ta ajjiye jakar ayrah ta ɗauki na mijin ta shiga da shi ciki, Ayrah dai tana tsaye a inda ta barta har ta dawo ta ɗauki ɗaya macen, Ayrah ta ƙarisa itama ta ɗauki ɗayar ta bi bayanta, sai da suka kwantar da yaran kafin ta kalli Ayrah tace "muje na nuna Miki inda zaki kwana". Ta fita Ayrah ta bi bayan ta, sai da ta ɗauki kayan Ayrah a falo kafin suka wuce, wani ɗaki ta kai Ayrah wanda yake kusa da na yaran nata, ta kalle ta, tace kishiga kiyi wanka kafin nan barin je, na da fa Miki ko indomie ne dan babu da faffen abinci a gidan". Ayrah dai tana tsaye bata ce komai ba, Jiddah tace "muje na nuna miki yadda zakiyi using da bathroom ɗin, Ayrah tabi bayan ta, sai da ta gwada mata komai kafin ta fita, tana fita Ayrah ta buɗe jakar kayan ta, wani photo ta ciro na maza yara guda uku sai da mace ɗaya babban cikin su yana ɗauke da macen, kallon ƙaramin ciki tayi kafin tace "Abba na, nayi kewarka, Abbana duk inda kake Allah yasa kana cikin ƙoshin lafiya, Abba sunce ka rasu, amma ni ban yadda ba, Abba na dan Allah ka dawo gareni". Ta ƙarisa maganar hawaye na bin ƙuncinta, sai da tayi kuka sosai ganin kukan ba zai kai ta ba, ya saka ta, ta shi , ta shiga bathroom ɗin, wanka tayi tare da ɗauro alwala, ta fito, ta ɗauki doguwar rigar material acikin kayan ta, ta saka, ta saka half Sunnah black, tana zaune sai ga, Jiddah ta dawo hannun ta ɗauke da babban plate, tace "ƙanwata har kin fito?". Ayrah tace "Erh aunty" . Jiddah ta ajjiye mata babban plate ɗin wanda yake ɗauke da, da plate ɗin da ta juye mata indomien ta rufe sa da wani plate sai kuma, ruwa gora 1 da cup, bayan ta ajjiye ta kalli Ayrah tace " ki sake jikinki kamar kina gidan ku, kinji?". Ayrah ta gyaɗa mata kai tana wasa da yatsun ta, tace "Yawwa na manta ban tambaye ki sunanki ba". Ayrah tace "sunana Ayrah ". Jiddah tace"Masha Allah, to kici abinci Ayrah barinje nayi wanka nima ". Ayrah tace "Nagode ". Jiddah ta sakar mata murmushi ta juya ta fice daga ɗakin, Ayrah ta jima a zaune tana tunani kafin daga baya ta buɗe plate ɗin abincin ta fara ci, ka ɗan taci, ta rufe sauran ta buɗe goran ruwan ta raga a cup ɗin ta sha, ta tashi ta ɗauki plate ɗin ta fice, tunda ta fara tafiya takejin kaman ido na yawo akan ta, ita dai bata ɗaga kai ba har ta ƙarisa falon, kafin ta ɗaga kanta, da wani irin mugun kallo Yake binta, haka kawai taji ta tsargu a ranta tace "subhnallahi wannan wane irin kallo ne". Tana ɗaga kai taga yana kallon ta har wani lashe lips yake, cikin sanyin murya tace " ina wuni". Yace "lafiya 'yan mata". Tace "dan Allah ina ne kitchen?". Hanayar kitchen ɗin ya nuna mata, yana bin ƙirjin ta da kallo, ita dai kan ta a ƙasa ta wuce kitchen ɗin, bata fito ba sai da ta wanke, duk abubuwan da taga anyi amfani da su ba a wanke ba, ta wanke ta tsaftace gurin ka fin ta fito, lokacin da ta fito, bata kalle shi ba, a ranta tana hamdala ga Ubangiji ta wuce ɗakin da aka ajjiye ta, tana shiga tai kwanciyar ta akan bed in tana kartanto addu'oi, bata daɗe ba bacci ya ɗauke ta, Jiddah ce ta shigo ta bakin ta ɗauke da sallama amma da taga tayi bacci kawai ta ja mata duvet, ta mayar mata da wutan ɗakin, dim light sannan ta fice, tare da rufo mata ƙofar, ..........

*WASHE GARI*

****** Ma'u tana zaune a bakin ƙofa tana kallon uban tilin wanke-wanken da mama tace tayi, a ranta tace "Ni zanyi wanke-wanken nan to ashe ma ni jaka ce". Da mugun ƙarfi aka banko ƙofar aka shigo, ta tsaya tana kallon sa tace "ɗan uwa lafiya ?". Tanko yace "ban sani ba dan ubanki". Har Ma'u zatai magana Mama Abu ta fito daga ɗaki, tace "lafiya kake buga min ƙofa kamar zaka karya min ƙofar gida".Ma'u tace "tambaye shi dai Mama".'

Tanko yayo kan Ma'u yace "zanci ubanki na ƙarajin maganar ki a gurin nan". Ma'u ta juyar da kanta, tana murguɗa masa baki, Yace " tukunna ma wai ina Ayrah?". Mama tace "ba ta nan ta, tattara kayan ta, tabar gidan nan saboda bata so ta aure ka". Yace " wallahi ƙarya ne, sai dai kun haɗa baki da 'yar ki kun koreta". Ma'u tace "to idan an koretan sai me?, gidan ubanta ne da......". Ai bata ƙarisa maganar ba taji sauƙar mari a fuskar ta, ta dafe ƙuncinta tace " kutumar uba ni ka mara?, lallai yau zaka gane baka da hankali". Tana rufe baƙin ta, ta ƙara jin sauƙar wani zazzafan marin, da sai da yasa ta bugu da bango, da sauri ta, tashi ta nufi gurin wanke-wanken da aka tara, ta ɗakko murfin tukunya Tanko bai ankara ba, sai ji yayi ta buga masa da iya ƙarfin ta, sai da yaje ƙasa, tace "na fika iskanci da tashanci wallahi". Hankalin mama yayi mugun tashi, ganin jinin da yake zuba daga goshin Tanko, hankali tashe ta kama hannun sa tace "tashi muje chemist". Gyalen ta, taja akan igiya suka fice, Ma'u tabi bayan su da kallo, tace "ka ɗan ma ka gani ƙaramin ɗan iska". Tana faɗan haka , ta juya ta ɗauki bocket ta ɗibi ruwa ta shiga, wanka bayan ta fito ta shirya, abinta taci kwalliya ta fice tabar gidan babu kowa, ......

*AYRAH*
Chapter 15 · 0% Book details