Sashe 23
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana tsaye a gaban mirrow tana rolling gyale a kanta Farhan ta tura ƙofar ɗakin ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, Ayrah ta amsa mata sallamar, ta juya ta kalle ta, bayan gama rolling gyalen a kanta, sanye take da abaya blue tayi kyau sosai, kallo ɗaya zaka mata ka gane ta haɗa jini da larabawa, kallon Farhan tayi, tace "sis sannu da dawowa". Farhan tace "Yawwa sannu". Yayinda take ajjiye school bag ɗin ta a gefen mirrorn, bayan ta ajjiye ta kalli Ayrah tace "yana ga kina ta shiri ne, kuma sai fara'a kike tayi sosai". Ayrah ta kalli Farhan da take ƙoƙarin cire abayar jikin ta daga saman school uniform ɗin ta, tace "kin manta aunty tamin alƙawarin idan na maida hankali nayi exam ɗina, nagama lafiya zata siya min waya". Farhan tace "ban manta ba". Bayan ta cire abayar riga da wandon uniform ɗin ta, suka bayyana, wando ne ash colour sai kuma farar riga, Ayrah yayinda take fesa turare a jikin ta tace " to shine fah yanzun zamu fita a cika min alƙawarina". Farhan tace "ai kuwa Nima dani za'aje barin yi wanka na fito dan Allah ku jirani". Ayrah tace "Tom shikkenan amma dan Allah karki daɗe". Farhan tace "insha Allahu". Daga nan ta fara rage kayan jikin ta, ta shiga bathroom, ita kuma Ayrah ta fice daga ɗakin ta nufi ɓangaren ammie, bakin ta ɗauke da sallama ta shiga palon, ta samu ammie da ya Aliyu ta samu a falon, ta ƙarisa ta zauna a gefen Ammie tana kallon Yah Aliyu tace "ina yini". Yace"lafiya ƙalau Ayrah". Tunda ta shigo take ta kallon sa tace "Ammie ina wuni". Tace "lafiya ƙalau Ayrah na, har kun shirya?". Tace" Erh Ammie ". Ammie tace "ina twins sistern naki". Tace" yanzu ta dawo daga school tana wanka". Aliyu ya daga kai a karo na babu a daɗi suka haɗa ido da Ayrah, Yace "Ayrah yaya dai?". Tace "babu komai kawai dai inaji kamar na sanka ne". Yayi murmushi Yace "anya kuwa to amma a ina kika Sanni?". Tace"wallahi na kasa tunawa". Yace"ikon Allah zata iya yiwuwa amma ni dai bansan ki ba". Tace "to tayiwu wani me kama da kai ne". Yace "it will be". Ammie tace"Ayrah na ina auntyn naki?". Ko rufe bakin ta batayi ba, sai ga Maya ta shigo bakin ta ɗauke da sallama, ta zaune gefen Aliyu ta gaida Ammie, sannan ta juya ta gaida ya Aliyu, Yah Aliyu yace " wai ina zakuje ne haka?". Maya tace "sisy na tagama exam ɗinta kuma na tabbata tayi ƙoƙari sosai shiyasa tun kafin result ɗin ya fito, za muje yawo sannan muje na siya mata phone, kaima ka kawo contribution ɗinka". Yace "Masha Allah ai kuwa dole na kawo contribution ɗina". Ya juya ya kalli Ayrah sannan Yace "congratulation sister ". Tace "thank you Yah Aliyu ". Yayi murmushi Yace" ki faɗa min abinda kike so insha Allahu I will buy it for you". Tace "Nagode sosai Yah Aliyu insha Allahu zan faɗa maka amma sai nayi tunani". Yace " Tom shikkenan ina jiranki amma sai naga result ɗin ki yayi kyau sosai". Tace "Tom shikkenan Yah Aliyu thank you". Maya tace "kinga Ayrah tashi mu tafi naga maganar ki da Yah Aliyu ba ƙarewa zatayi ba". Ayrah tace "Aunty bari naje na kira farhan ". Tana faɗan haka ta miƙe, bata daɗe da fita ba sai ga ta ita da Farhan sukayi yiwa su Ammie sallama sannan suka fice, gurin sai da waya suka fara zuwa, suka aka siya mata wayar ta iphone 15pro. tayi registern sim sannan suka wuce, Hans&René, domin shan ice cream, gurine mai kyau da tsafta, suna zuwa suka zauna, sukayi ordern ice cream da cookies, bayan an kawo musu Farhan ta kalli Maya tace "Aunty Maya ni yaushe Yah Amjad zai dawo ne?". Ayrah tace "wallahi nima na ƙosa naga farincikin rayuwar Aunty na". Farhan tace "Yawwa Ayrah ke baki da saurayi ne?". Tace "ina da shi, akwai wanda zuciya ta, take mutuwar so, kamar yadda aunty take son uncle Amjad" Farhan tace "Masha Allah to meye sunan sa?". Ayrah tace "ban sani ba wallahi, Ni dai kawai inajin zuciya ta tana ƙaunar sa ne". Farhan tace " Masha Allah, Allah ya bar ƙauna". Maya tace "Ameen". Ayrah tace "to ke fa baki taɓa bani labarin wanda zuciyar ki take so, ba Aunty na kam kullum sai ta bani labarin uncle Amjad". Farhan tace "wallahi Ayrah ni bana soyayya ban taɓa kula wani ɗa na miji da sunan soyayya ba". Ayrah tace "Ayya Allah sarki na fahimta". Haka dai suka sha hirar su, bayan sun gama suka tashi Maya tayi making payment suka fita, suna zuwa jikin mota, sukaji ance "Assalamu alaikum". Dukkanin su, suka juya suna kallon sa, Ya kalli Ayrah , Yace "kamar Ayrah". Tace "nice ina yini?". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah Ayrah ya kwana da yawa". Tace "alhamdulillah sai dai bangane ka ba". Yace" haba dai amma wasa kikeyi ko?, uncle Jabeer ne fa, na gidan aunty Jiddah". Tace "Aunty Jiddah kamar dai nasan ta, amma wallahi na kasa tunawa". Jabeer yace" ban fahimci kin manta aunty Jiddah ba". Maya tace "uncle Jabeer ina yini". Yace "lafiya ƙalau alhamdulillah". Tace "idan babu damuwa zamu iya magana". Yace " why not?". Maya taja gefe ya bita, Maya tana kallon sa tace "kasan ta ne?". Yace " Erh mun zauna da ita a gidan yayana a Kano rana ɗaya muka ne Meta muka rasa, amma meyasa kika tambaya?". Tace "she had an accidental, ta samu bugawa a brain ɗin ta, ba komai take tunawa ba, amma kai ɗan uwanta ne?". Yace "kina nufin yanzu tana fama da partial amnesia kenan?". Maya tace "Erh ". Yace "ikon Allah, sai kuma ya juya yana kallon ta, Yace "amma wannan yarinyar tana fama da jarrabawar rayuwa kala-kala, Allah Ubangiji ya kawo mata ɗauki". Maya tace "Ameen". Yace "idan babu damuwa zan isa samun nimbern ta ko na ɗaya daga cikin ku, akwai maganar da nake so muyi". Maya tace "babu damuwa barina baka numbern ta, yanzu muka yi registern sim ɗin amma anjiman insha Allahu zamu ɗaura akan waya". Yace "ok inajinki". Maya ta buɗe hand bag ɗin ta, ta ciro sim ɗin, ta faɗa masa numbern tare da mayar wa hand bag ɗin ta, ya kalle ta, Yace " Nagode". Tace "nevermind". Daga haka suka koma inda Ayrah take, tana ta kallon sa har ya ƙariso, yayi murmushi yana kallon ta, Yace "Madam marar gaisuwa kin kasa tunani ko?". Tayi murmushin ƙarfin tace"Erh". Yace "Tom shikkenan nagode ni zan wuce, insha Allahu zanzo har gida muyi magana". Tace "thank you ka gaida mutanen gidan". Yace "zasuji". Ya wuce abinsa suma suka shiga mota suka koma gida, tun da suka shiga motar Ayrah bata ce ƙala ba, ta jinginu da seat ɗin, ta lumshe idanun ta, suna ƙarisawa gida ta fita, ta wuce ɗaki ko ta kansu bata biba, tana shiga ta faɗa kan gado ta fashe da kuka..............
Mubeenah tana kashe wayar ta share hawayen ta, ta tashi ta buɗe wardrobe ta ciro hijabi ta saka , ta fice ta nufi ɓangaren Daddyn su, bakin ta ɗauke da sallama, ta samu daddy yana zaune akan kujera fuskar sa ɗauke da glass ya riƙe Alqur'ani a hannun sa yana karatu, ta ƙarisa falon ta zauna a ƙasan carpet ɗin, sai da ya kai ƙarshen a yar ya ɗago yana kallon ta, yace "Wa alaikissalam mubeenah". Tace " Daddy Barka da karatu". Yace"Barka dai mamana lafiya?". Tace" Daddy dama magana nake so muyi". Yace"inajinki". Ya faɗa yayinda yake rufe Alqur'anin ya ajjiye, tace" Daddy dama akan baiwar Allahn da Maya ta tsintane, ɗazu muna vedio call nagan ta, wallahi Daddy muna kama sosai kuma a jikina naji ita ɗin jinina ce wallahi Daddy". Ta ƙarisa maganar tana hawaye, Yace " Abbie ma ya Kirani munyi magana akan yarinyar yace zai bincike ta kuma Insha Allahu duk halin da ake ciki zai sanar da ni, mubeenah tace"Tom shikkenan daddy Allah yasa muji alkhairi". Yace "Ameen ". Mubeenah tace"kuma Daddy ina zargin mahaifin ta shine wanda suka rasu tare da Yah Kamal". Daddy yace"idan ma shi ɗinne ke ya akayi kika sani". Tace"Daddy lokacin munje duba jikin hajjah muna dinner Dr kamal yake cewa yaga wata me kamata ta kawo mahaifin ta asibitin su, har yake cewa mommy kamannin da muke ya ɓaci kawai dai ta fini haske mai kyau ne". Daddy yace "ok yanzu dai mujira miji abinda Alhaji Abdullahi zaice". Mubeenah tace "Tom shikkenan ". Daga nan suka canza wata hirar.........
Kuka tayi me isarta, sai yau take jin ciyon kasa tuna wani abu a rayuwar ta, bayan ta gama kukan ta, tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito tasaka doguwar riga marar nauyi, Farhan ce ta shigo bakin ta ɗauke da sallama bata jira Ayrah ta amsa mata ba, tace "kizo Abbie na kiranki, a main falo". Ayrah taji zuciyar ta tayi wani mummunan bugu, ta buɗe wardrobe ta ɗauki hijabin ta, tasaka ta fice, a main falo ta samu, Abbie, ammie, yah Aliyu Maya da kuma Farhan, ta zauna a ƙasan carpet tana gaida Abbie ya amsa , sannan Yace "duk kan mu nan mun hallara ne dalilin ki, inaso na Miki wata tambaya kuma ina so ki faɗa min gaskiya tsakanin da Allah kinji mamana". Tace"insha Allahu Abbie zaka sameni da faɗan gaskiya". Yace"Masha Allah, kin san mahaifin ki?". Tace"Erh nasan shi, sun cemin ya ƙone a jirgi da shi da wani likita Dr kamal wanda ya taimake ni ya fitar da shi waje, domin sama masa lafiya". Dukkanin su suka ɗago kai suna kallon ta with shock kenan mahaifin ta ne ya rasu tare da Yah Kamal?, Abbie Yace "kin san 'yan uwansa tace"ban sani ba ". Yace "ko kina da photon sa ?". Tace "Erh ". Yace "jeki ɗakko min". Ta tashi ta fita bata daɗe ba sai gata da photo ta durƙusa ta miƙawa Abbie, ya karɓa yayi snapping ya turawa Daddy,........