← Book details Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 28

Sashe 27

Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ayrah tana zaune a falon Jaddah tana danne-danne a wayar ta, Farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama ta zauna a gefen Ayrah tana kallon ta, tace "sis ki shirya mana anjima ki raka ni unguwa". Ayrah tace "dan Allah mu tafi yanzu ba sai anjima ba". Farhan tace "ikon Allah yanzu kuma?". Ayrah tace "Erh yanzu wallahi zaman guri ɗayan ya isheni". Farhan tace "ok barinje na shirya kema ki shirya sai mu tafi". Ayrah tace "ok". Yayinda ta tashi ta nufi ɗakin ta, dan tuni ta tattaro kayan ta ta dawo ɓangaren Jiddah , tana shiga bathroom ta wuce tayi wanka, ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar azahar, sannan ta shirya cikin doguwar rigar Atamfah mai kyau, veil, hand bag plate shoe, duka farare ta saka tayi kyau sosai, ta fito ta wuce ɗakin Jaddah, ta shiga bakin ta ɗauke da sallama, ta zauna a ƙasan carpet ta gaida Jaddah, jaddah ta amsa cikin fara'a, kafin ta maida gaisuwar tata kan Hajjah, Hajjah ta amsa mata itama da fara'a Jaddah tace "mamana ina zuwa naga kin yi kwalliya haka". Ayrah tace "unguwa zan raka Farhan". Hajjah tace "Masha Allah to Allah ya tsare". Ayrah tace "Ameen Hajjahn mu ". Ta faɗa yayinda take tashi ta fice, ta shiga ɗakin ummin ta, bakin ta ɗauke da sallama, Ummi tana zaune a bakin gado Ammar kuma yana zaune akan dressing mirrow, dukkan su suka amsa, ta ƙarisa ta zauna a gefen ummin ta, tace "Ummi ina yini?". Ummi tace "lafiya ƙalau Ayrah na". Ayrah ta ɗaga kanta ta kalli Ammar da yake kallon wani direction da ban, tace "ina yini". Yace "lafiya". Lokacin Farhan ta shigo bakin ta ɗauke da sallama itama ta shirya cikin Abaya blue tayi kyau sosai, ta gaida Ummi , Ummi ta amsa mata cikin farin ciki kafin ta gaida Yah Ammar, ya amsa kamar yadda ya amsa wa Ayrah, Ayrah tace "Farhan ta shi mutafi". Ina zakuje ya tambaya a tsare, Farhan tace "Yah Ammar zamuje shopping ne". Kamar ba zai yi magana ba sai kuma Yace "duk abinda zakuyi karku kai 2 hours a waje". Farhan tace "insha Allahu". Sai kuma ta juya ta kalli Ummi tace" Ummi mun tafi". Ummi tace "sai kun dawo Allah ya tsare". Suna fitowa suka samu Mubeenah da Nailah da kuma Maya suna zaune a falo suna Game ɗin ludo master, kamar ba Nailah ce mai gaba da su adaba, Maya ta Kalle su tace "lallai bayin Allahn nan wato fita ma zaku yi shine ko neman 'yan rakiya bakwayi?". Farhan tai sauri tace "ikon Allah wai dama Ayrah bata faɗa muku ba?". Nailah tace "karfa ki mata sharri Farhan inajin ki, lokacin ina kitchen kikace ta shirya ta rakaki wani guri". Mubeenah tayi dariya tace" Indai Farhan ce zata aikata abinda yafi haka ". Ayrah tace "aunty na an sake result fah". Maya tace "Erh zan duba miki ɗazu Yah Amjad ya tambaye ni wai wace makaranta kike son zuwa?, zai ne maki admission". Ayrah da taji wani abu ya bigi zuciyar ta, tai murmushin da iya kacinsa fuskar ta, tace "idan mun dawo za muyi shawara da sisy na". Tana faɗan haka suka nufi hanyar fita driver ne ya kai su saboda Ammie ta hana ta driving, restaurant suka fara tsayawa, suna zaune bayan an kawo musu abinci suna ci, kamar da ga sama Ayrah taji ance "Ayrah". Ta ɗaga kai zuciyar ta tayi mugun bugawa sakamakon kallon sa da tayi amma ta danne saboda kar Farhan ta fahimta, tace "uncle Bissimillah ka zauna mana". Abubakar ya zauna yana murmushi, tace "uncle ina yini, ya gida ya su aunty Jiddah?". Yace "suna nan lafiya ". Tace "Masha Allah". Yace "Ayrah yanzu a ina kike da zama?". Tace "na samu familyn Abba na da na ummie na, wannan ma cousin sister na ce". Ta ƙarisa maganar tana nuna Farhan, Farhan tace "ina yini". Yace "Lafiya fatan kuna lafiya". Tace "alhamdulillah". Sai kuma ya maida kallon sa kan Ayrah Yace " na daɗe ina neman ki Ayrah tare da addu'ar Allah ya ƙara haɗa fuskokin mu, na nemi yafiyar ki akan abinda ya faru". Tace "babu komai wallahi uncle karka ji komai ni na yafe maka, kuma tun a lokacin ni ban riƙeka a zuciya ta ba". Yace "Yawwa Nagode sosai Ayrah ". Tace"badamuwa ". Yace " sannan ina so na gode miki domin kin zama sanadiyyar dawowar farincikin gidana, yanzu Jiddah ta canza ta ajjiye aiki bata da aikin da ya wuce kula da mu, ni da kuma yaran mu". Ayrah tace "alhamdulillah amma wallahi naji daɗi uncle kuma nayi farincikin jin haka". Sai da ya musu marking payment ya karɓi numbern Ayrah, kafin ya musu sallama ya wuce, suma daga nan suka shiga mota suka wuce shopping, tana cikin mota taji wayar ta, tayi ƙara alamar shigowar massage, buɗe wayar ta duba, taga credit alert na 1M da mugun mamaki, ta ke kallon sunan wanda ya tura mata, Muhammad Ahmad QURAISH, ta kalli Farhan kamar zatai magana sai kuma ta fasa, bayan sun ƙarisa sun gama shopping ɗin su, suna ƙoƙarin fitowa , Ayrah hankalin ta yana kan wayar ta, taci karo da wata, da sauri ta ɗago da niyyar bawa wacce ta bige ɗin hakuri, da mugun mamaki ta tsaya tana kallon ta, ita ɗin ma ita take kallo, sai kuma ta daka tsalle ta rungume Ayrahn tana hawayen farin ciki tace "bestie". Ayrah tace " ƙawata nayi kewarki sosai ". Itama tana hawaye, Ayrah ta sake ta tana share hawayen idon ta, da bakin veil ɗin ta, tace " ina mama?". Sa'adatu tace "mama tana gida mun ne meki sosai har mun fidda rai kullum muna Miki addu'ar Allah yasa kina hannu nagari kuma cikin farinciki". Ayrah tace "ai nasamu familyn Abba da na Ummi, yanzu haka ma muna tare da Ummi na a gidan elder brothern ta". Cikin farinciki Sa'adatu tace "Masha Allah na ma fasa shopping ɗin kawai zan biku naje naga Ummi ". Ayrah tace "a'a kije kiyi shopping ɗin ki, kawai ki bani numbern wayar ki, insha Allahu gobe zamu zo har gida ni da ummi". Sa'adatu tace "shikkenan". Ta karɓi wayar Ayrah ta saka mata numbern ta, har zata tafi sai kuma ta tsaya tana kallon Ayrah tace "bestie amma akwai abinda yake da munki". Ayrah tace "zamuyi magana zuwa goben ko anjima ". Sa'adatu tace "Tom shikkenan amma ina Yah mufaddhal yake ?". Ayrah tayi murmushin da iya kacinsa fuskar ta, ne tace "yana nan". Sa'adatu tace "to bazaki gabatar min da ƙawar taki bane?". Ayrah tace "ohhhh I'm sorry she's my cousin sister me sunan Ummi ce, amma ana ce mata Farhan ". Sa'adatu tace "Masha Allah Farhan nice to meet you ". Farhan tace "nice to meet you too". Daga haka sukayi sallama suka wuce, ko da suka dawo gida, ɗakin ta ta nufa ta ajjiye shopping ɗin nasu, tayi wanka ta ɗaura alwala bayan ta fito, ta canza kaya zuwa doguwar riga marar nauyi, ta gabatar da sallar la'asar, tana kan sallaya wayar ta, ta fara wringing, kallon screen ɗin wayar tayi taga, baƙuwar number, picking tayi tare da sallama, yaji Muryar ta, ta daki dogon kunnen sa, ya amsa mata sallamar, sai shiru ya biyo baya, Yace "Fulani". Har cikin zuciyar ta taji kiran da ya mata, maimakon ta amsa sai tace "naga alert ɗazu Nagode sosai Allah yasaka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Yace "Ameen Fulani na, Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen". Yace "kun dawo ne?". Tace "Erh mun dawo". Yace "kinyi Sallah?". Tace "Erh". Yace "Masha Allah, to abinci fah?". Tace "munci abinci dasu yanzu kuma banajin yunwa". Yace "shikkenan Fulani na Allah ya Miki albarka". Tace "Ameen". Daga haka ya kashe wayar, yana ƙara jin ƙaunar ta yana ratsa dukkan wani sassan jikinsa, ita kam yana kashewa tabi wayar da kallo kawai ta fashe da kuka tanajin wani abu mai nauyi ya tsaya mata a zuciyarta, ganin kukan bazai kaita ba, kawai ta miƙe ta nufi, bathroom ta wanke fuskar ta, ta fice ta nufi ɗakin ummin ta, bata samu Ummi a ɗakin ba, sai ta wuce ɓangaren ɓangare hajjah ta sameta a falon Hajjah tana zaune suna magana da Jaddah kallo ɗaya zaka yiwa Ummi ka gane tana cikin damuwa, sosai Ayrah tace "na ƙariso ko na koma maganar da kukeyi mai muhimmanci ce". Jaddah tace "shigo ƙawata". Ummi tana kallon Ayrah ta fashe da kuka, jaddah tace "to miye na kukan kuma, addu'a mijinki yake buƙata ba kukan ki ba". Ayrah da idon ta ya ciko da hawaye ta danne tace " haba Ummi miye amfanin kukan kuma? Kawai ki tashi ki shiga ɗakin kin Hajjah, kiyi alwala kiyi sallah ki roƙa masa gafara a gurin Ubangiji ". Ayrah tana faɗan haka ta miƙe ta nufi ƙofar fita, domin hawayen ta take ɓoyewa yana ƙoƙarin tona mata asiri...........
Chapter 27 · 0% Book details