Sashe 16
Bayan Duhu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Misalin karfe 8:00am ta, tashi ta fito da mugun mamaki ta fito, tana bin falon da kallo yanda ya fita fes-fes ko ina sai ƙamshi ya keyi, kitchen ta nufa domin ɗaura musu ko da indomie ne, da mugun mamaki take kallon Ayrah da take tsaye tana soya Irish, Ayrah jin kamar ana kallon ta, ya saka ta saurin juyowa, murmushi ta sakarwa Jiddah tace "good morning Aunty". Jiddah tace "morning Ayrah". Still tana tsaye tana kallon Ayrah, Ayrah ta juyo bayan ta tsame Irish ɗin a kosko ta saka wani, ta kalli Jiddah tace "aunty kina buƙatar wani abu ne?". Jiddah tace "no Ayrah, thank you". Ta wuce ta juya ɓangaren ta domin ta tayi wanka ta shirya, Ayrah bayan ta gama haɗa musu break past, ta kai dining ta jere, ta koma ta gyara kitchen ɗin da duk abubuwan da ta tayi amfani da su, sannan ta fita, ta nufi ɗakin da suka kai yara jiya, bakin ta ɗauke da sallama ta buɗe ƙofar ta shiga, mace ce, wacce bazata wuce 7 years ba tana ƙoƙarin sakawa ƙanin ta kaya wanda shima bazai wuce 4 years ba, juyowa sukayi suna kallon ta, ta ƙarisa inda suke tana murmushi, macen ta kalle ta, tace"good morning". Tace" morning". Shiru ya biyo baya, Ayrah ta kalle ta, tace kawo shi , na shirya sa, ta karɓi rigar yaron ta saka masa tana, murmushi ta kalli macen tace "sunana Ayrah ke fah?". Itama murmushin tayiwa Ayrah tace "sunana liyana". Ayrah tace "nice name". Bayan ta gama sakama yaron kaya tace "what about you" yace Khalil ". Tace "Masha Allah nice to meet you ". Dai-dai nan aka murɗa handle ɗin bathroom aka fito, dukkan su juyawa sukayi suna kallon ta, Ayrah ba ƙaramin shock ta shiga ba, ta kalle ta, ta juya ta kalli liyana tace "twins?". Liyana ta gyaɗa mata kai tana murmushi, tace "sunan ta leenah ". Leenah ta ƙariso tana kallon Liyana tace " sis please help me dry my hair". Liyana tace "ba zan iya ba gaskiya". Leenah ta kalli Ayrah tace "aunty help me please ". Ayrah taje ta busar mata kanta da hand Drayer, bayan ta gama leenah ta shirya Ayrah ta kalle su tana murmushi tace "to muje kuyi break fast". Khalil da yake riƙe da hannun Ayrah yace "aunty Ni bana son taliya ko indomie kullum momy taliya take mana ko indomie". Ayrah ta daga shi sama tace "Tom yau aunty bata maka taliya ba kuma bata maka indomie ba". Yace "aunty me kika mana". Tace "abun daɗi". A haka suka ƙariso dining ɗin suna ta hira da Ayrah suna dariya, Ayrah taja kujera da zaunar da Khalil suma twins suka zauna, sai lokacin suka lura da momyn su da take zaune take break fast hankali kwance, dukkan su, suka gaishe ta, ta amsa, Abubakar shima da yanzu ƙariso warsa yaja kujera ya zauna, Jiddah tace "good morning darling". Ayrah tace ", morning". Ayrah da sauran yaran duk sukece "good morning ".Yace " morning". Yana kallon Jiddah yace "baƙuwa mukayi ne?". Jiddah tace "itace wacce jiya nace maka zamuyi magana akan ta".Yace "ok". Da ga nan shiru ya biyo baya ita dai Ayrah ta kasa sakewa saboda yanda take jin idonsa akan ta, ...........
___________ 🥀BAYAN DUHU🥀__________
FEATURE WRITERS ASSOCIATION....
*AISHA MUHAMMAD KABIR*
*MER'EESHER âœï¸*
Book 1
Page 15......
***** Ayrah dai bata wani sake taci abincin kirki ba, kasancewar yau ranar Lahadi ce, babu aiki, bayan sun gama breakfast suka dawo falo suka zauna, Jiddah ta kalli su Liyana tace "kuje kuyi wasa amma banda faɗa kunji, zamuyi magana da aunty". Leenah ta kama hannun Khalil suka fice daga falon, Jiddah ta kalli Ayrah, tace "ai da baki wahalan tar da kanki ba, na fito ne fa zan haɗa mana break fast na ganki a kitchen ɗin". Ayrah tace "babu komai ai da yake na saba da aiki ne sosai, to idan bana aiki sai naji bana jindaɗi". Jiddah tace "ayya Nagode sosai fah". Ayrah tace "nice da godiya ai,". Sai kuma tace " lokacin da muka zo jiya ko dan dare ne, ban lura da kaman nin su Liyana ba, ashe twins ne". Jiddah tace "ayya wallahi twins ne". Sai kuma shiru ya biyo baya babu wanda ya ƙara cewa komai shidai Abubakar yana zaune,kaman yana danna waya amma hankalin sa yana kan Ayrah da take zaune a ƙasan carpet, after some minutes Jiddah tai breaking silent ɗin nasu da cewa "Ayrah". Ayrah ta ɗago kai tace "na'am". Jiddah tace "dan Allah inaso ki faɗa min tsakanin dan Allah mekike jiya cikin dare a bakin titi". Ayrah kamar baza tai magana ba, sai kuma tace "ban san inda zanje bane wallahi". Abubakar yace "to ina gidan ku yake?". Tace " sanin gidan mu bashi da amfani domin yanzu gidan yafi ƙarfina". Abubakar yace "ban fahimta ba". Ayrah ta share hawayen idonta tace " da ni da matar babana muke rayuwa kuma ta kore ni". Jiddah tace "amma Meyasa?". Ayrah tace"saboda tana so ta aura min ɗan ta, ɗan shaye-shaye kuma ɓarawo ". Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru jiya ta faɗa musu, Jiddah ta kalli mijin ta, tace "dan Allah darling idan babu damuwa ta zauna damu mana". Abubakar yace "babu damuwa Allah ya mana jagora, Allah ya shirya masu hali irin na kishiyar maman ta". Dukkan su, sukace "Ameen". Ayrah a zuciyar ta tace " dan ma ban faɗa muku abubuwan da ta min da kuma gidan mu da tasiyar ta siya wani ba". Jiddah ta kalle ta, tace "Ayrah ina zaki zauna damu". Ayrah tace "Nagode sosai Allah ya saka Miki da alkhairi aunty". Jiddah tace "Ameen ya Allah". Ayrah ta kalli Abubakar sai kuma ta sunkuyar da kanta tana wasa da yatsun hannunta tace ", Nagode uncle". Yace "karki damu Ayrah ai yiwa kaine". Daga nan ta tashi ta fita gurin su leenah ta biye musu suka fara wasa kamar wata yarinya,.....
*AMJAD*
I zuwa yanzu har ya gaji da neman da yake yiwa Ayrah ya tattara komai ya sallama wa , Ubangiji addu'a yake babu dare babu rana, akan Allah ya haÉ—a fuskokin su, a lokacin da baiyi tsammani ba, tunda yaga ba samun ta zai yi ba ya tattara kayan sa ya koma Madina, saboda yana tunanin idan ya zauna ma auren sa da Maya za'ayi kwana kusa,.......
*MAYA*
Kasancewar yau Lahadi ne, babu aiki, Mubeenah ta shirya musu fita ita da fadeelah , duk dama ba'a sanar mata gurin da za suje ɗin ba,tana gaban mirror tana feshe jikin ta da turaruka masu daɗin ƙamshi, wayar ta, ta fara wringing picking tayi tare da sallama daga ɗaya ɓangaren yace "wa alaikissalam Maryam Yakike?". Tace "lafiya ƙalau alhamdulillah Abie ya su ammie?". Yace "suna lafiya ya gidan naku?". Tace "lafiya ƙalau Abie na". Yace "Maryam akwai wata matsala ne?". Tace "babu matsalar komai Abie". Yace "bakya buƙatar wani abu?". Tace "alhamdulillah bana buƙatar komai Abie". Yace "to shikkenan alhamdulillah amma duk da haka zan tura miki kuɗi kiyi wani abun da shi". Tace "Abie wanda ka turamin ma fah bai ƙare ba". Yace " badamuwa Maryam zan ƙara Miki saboda nasan koya ƙare ɗin ma ba magana zakiyi ba". Tace "Nagode sosai Abie Allah ya saka da alkhairi Allah ya ƙara arziki". Yace"Ameen Maryam Allah ya miki albarka". Tace "Ameen Abie nah". Bai ƙara cewa komai ba, ya kashe wayar, bayan ya kashe ya tura mata kuɗin, kafin ya kalli ammie da take zaune a gefen sa tun ɗazun yace "yarinyar nan akwai hankali". Ammie tace "Maryam kam babu laifi, Amjad yayi sa'ar mata, sai dai mu, musu fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, Allah ya nuna mana lokacin". Abie yace "Ameen Fatima". Sai kuma ya ɗaura da cewa "bana fatan Allah ya nuna min lokacin da yarinyar nan zata ɗanɗani ɗacin maraici, Allah kar ya nuna min lokacin da yarinyar nan zatai kewar mahaifin ta, lokacin da yarinyar nan zata ji ina ma mahaifin ta yana raye, saka makon wani baƙin ciki, Allah yasa ta tun daga tuna shi tana masa addu'a a lokacin da a take farin ciki, amma ba a lokacin da muka nuna gazawar mu akan ta ba". Ammie tace "Ameen Allah ma kar ya nuna mana lokacin da zamu nuna gazawar mu akan Maya". Yace "Ameen ya hayyu ya ƙayyum"...........